'Ba ciwon asma ne ya yi ajalin 'yarmu ba'

'Yansanda

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

An kaddamar da bincike akan mutuwar wata daliba a makarantar sakandire ta St. Louis bayan da iyayen suka tabbatar da cewa 'yarsu bata da ciwon da ake zargi ya yi ajalinta.

Korafin da iyalan marigayiyar suka shigar gaban 'yan sanda a jihar Kano ne yasa aka kaddamar da bincike don gano hakikanin abubuwan da suka faru game da rasuwar yariyar a makarantar sakandire ta St. Louis.

Mahafiyar yarinyar ta shaida wa BBC cewa, suna zargin hukuntata ne ta hanyar bulala da kuma tsugunnar da ita na tsawon lokaci ne ya yi sanadin rabata da duniya.

Ta ce," Koda aka zo mini da labarin mutuwarta abin da aka ce mini shi ne an sanyata (Knell down) wato tsugunno akan gwiwarta na tsawon lokaci, shi ne ta yanke jiki ta fadi ta kuma ce ga garinku nan."

"To bayan da malaman makarantar kuma suka zo mana ta'aziyya sai suka fadi bambancin abin da aka fada mana da farko inda su suka ce wai ta makara sallah ne shi ne aka hukuntata kuma wai ashe tana da asma shi ne ta yanke jiki ta fadi." In ji mahaifiyar yarinyar.

Ta ce," Da muka je asibiti bayan sanar damu cewa bata da lafiya na shaida mana cewa dama ko da aka kaita asibitin daga makarantar a mace aka kaita."

Mahaifiyar dalibar ta ce, " A gaskiya ni 'yata bata da ciwon asma hasali ma ni ban san ko da maganin ciwon guda ba, yarinya lafiyarta kalau don ko zazzabi ma zafi bata yi ballantana ciwon zuciya."

" To ace kawai don an Sanya mutum (knell down) tsugunno akan gwiwa sai ya fadi ya mutu, wannan ba abu ba ne da hankali zai yar da dashi."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta ce, " Mu fa abin da wadansu a makarantar da aka yi abin a gabansu suka shaida mana shi ne tsugunno akan gwiwarta aka sanyata a rana na tsawon lokaci, domin da farko an sanyata shara ta ce ba zata yi ba don tana da lalurar asma, to bata da wannan ciwo ba mamaki ta fadi hakan ne don ta kare kanta daga yin sharar, to shi ne aka ce ta tsugunna akan gwiwarta a rana, anan ne kuma saboda dadewar da ta yi ta yanke jiki ta fadi."

" Wadanda suka fadi wannan magana ganau ne 'yan makarantar ne, don haka yanzu mu mun kai kara wajen jami'an tsaro, kuma aka fara bincike." In ji mahaifiyar yarinyar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Kano dai, ta sanar da kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike akan musabbabin mutuwar dalibar.

Rasuwar yarinyar 'yar shekara goma sha hudu ta haifar da ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta inda ake ta yada bayanai mabanbanta game da musabbabin rasuwar.

Tuni dai kwamishinan 'yan sandan Kano CP Adamu Ibrahim Bakori, ya kaddamar da bincike ƙarƙashin jagorancin DCP Shehu Idris tare da haɗin gwiwar jami'an ma'aikatar shari'a ta jihar Kano.

Duk kokarin jin bangaren makarantar sakandire ta St. Louis da BBC ta yi ya ci tura.