Nunez ya yi sanadin da Liverpool ta raba maki a Fulham a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Sabon dan kwallon da Liverpool ta dauka a bana Darwin Nunez, ya yi sanadin da Liverpool ta tashi 2-2 a gidan Fulham a gasar Premier League ranar Asabar.
Liverpool wadda ta yi ta biyu a Premier a kakar da ta wuce ta ziyarci wadda ta lashe Championship a bara, wadda ta samu gurbin babbar gasar tamaula ta Ingila.
Fulham ce ta fara cin kwallo ta hannun Aleksandar Mitrovic, na 44 da ya yi wa Fulham tun daga bara a wasa 45 kenan.
Hakan ya sa yana da tazarar kwallo 15 tsakaninsa da duk wani gwanin zura kwallo a raga tun daga bara a gasar tamaulla ta Ingila daga Premier zuwa kasa.
Liverpool ta farke ta hannun Nunez, wanda ya shiga wasan daga baya, sannan shi ne ya taba kwallon da Mohamed Salah ya farke na biyu da aka ci kungiyar Anfield.
Da wannan kwazon Nunez ya zama na uku da ya ci kwallo ya kuma bayar aka zura a raga a wasansa na farko a Premier, bayan da ya shiga daga baya.
Masu wannan bajintar sun hada da Sergio Aguero a 2011/12 da kuma Álvaro Morata a kakar 201718.
Liverpool ta raba maki da Fulham kernan, wadda ta hada maki 115 a gasar Premier League karkashin Jurgen Kloop, bayan an doke ta ta farke daga baya.
Kloop ya karbi aikin kociyan Liverpool daga Oktoban 2015.
Haka kuma Liverpool ta kawo karshen wasa 51 a Premier League ba tare da bayar da fenariti ba, kuma karon farko da Virgil van Dijk ya yi ketar fenariti tun Oktoban 2018 a fafatawa da Manchester City.
Liverpool ta fara wasan makon farko da 'yan kwallo shida da suke da shekara 30 ko fiye da haka da suka hada da Firmino da Henderson da Matip da Salah da Thiago da kuma Van Dijk.
Rabon da ta yi hakan tun a wasa da Southampton a Fabrairun 1994 da saka 'yan wasa shida masu shekara daga 30 zuwa fiye da suka hada da Barnes da Grobbelaar da Nicol da Rush da Whelan da kuma Wright.











