Ismail Kartal Ya Sake Komawa aikin horar da Fenerbahçe, Fenerbahce

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Fenerbahçe ta sanar cewa tsohon kocinta mai shekara 65, Ismail Kartal, zai sake horar da ita a karo na huɗu.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta bayyana cewa Kartal ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara ɗaya.
Kartal, wanda ya shafe kusan shekara goma yana taka leda a Fenerbahçe a lokacin ƙuriciyarsa, ya taɓa horar da ƙungiyar a:
- 2014–15
- 2021–22 (a matsayin mai rikon kwarya)
- 2023–24
Haka kuma, ya taɓa zama mataimakin koci a lokutan da Fenerbahçe ta lashe gasar Turkish Super Lig.
A ƴan shekarun nan, Fenerbahçe ta sha fama da rashin nasarar lashe kofi, inda ta ƙare a matsayi na biyu sau biyar a jere a gasar lig, yayin da abokiyar hamayyarta daga Istanbul, Galatasaray ta ɗauki kofin sau huɗu a jere.
Yanzu dai dawowar Kartal na nufin Fenerbahçe na fatan kawo ƙarshen wannan dogon lokacin na rashe lashe lik a babbar gasar tamaula ta Turkiyya.




