Anya Liverpool za ta shiga 'yan huɗun Premier a bana?

Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool ta tashi 0-0 da Chelsea a kwantan wasan mako na takwas a gasar Premier League da suka ranar Talata a Stamford Bridge.

A wasan farko ma a Janairu haka suka tashi, sau hudu a jere suna raba maki a tsakaninsu a dukkan fafatawa

Karo na uku da manyan kungiyoyin Premier na raba maki a fafatawa hudu a jere, bayan Everton da Liverpool tsakanin 1974 - 1975 da na Arsenal da QPR tsakanin 1992 - 1994.

Da wannan sakamakon Liverpool tana ta takwas a teburin Premier da maki 43, saura wasa 10 ta kammala fafatawar bana.

An fitar da Liverpool a Champions League da FA Cup a bana, Manchester United ce ta lashe Carabao Cup na kakar nan.

Kenan matakin 'yan hudun farko Liverpool ke fatan shiga, domin ta buga Champions League a badi, bayan da za ta kare kakar nan ba kofi ko daya.

A bara Liverpool wadda ta yi ta biyu a Premier League a bara da lashe FA da League Cup ta buga wasan karshe da Real Madrid a bara a Champions League.

Liverpool wadda ta yi wasa 28 kawo yanzu a Premier ta yi nasara 12 da canajaras bakwai aka doke ta sau tara, sannan ta ci kwallo 48 aka zura mata 33 a raga.

Wasanni da suka rage wa Liverpool a Premier League:

Premier League Lahadi 9 ga watan Afirilu

  • Liverpool da Arsenal

Premier League Litinin 17 ga watan Afirilu

  • Leeds da Liverpool

Premier League Asabar 22 ga watan Afirilu

  • Liverpool da Nottingham Forest

Premier League Laraba 26 ga watan Afirilu

  • West Ham da Liverpool

Premier League Lahadi 30 ga watan Afirilu

  • Liverpool da Tottenham

Premier League Laraba 3 ga watan Mayu

  • Liverpool da Fulham

Premier League Asabar 6 ga watan Mayu

  • Liverpool da Brentford

Premier League Asabar 13 ga watan Mayu

  • Leicester da Liverpool

Premier League Asabar 20 ga watan Mayu

  • Liverpool da Aston Villa

Premier League Lahadi 28 ga watan Mayu

  • Southampton da Liverpool