Tsoffin Janar-Janar sun yi kira da a ingata harkar tsaro bayan rasuwar Rabe Abubakar

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Tsoffin hafsoshin sojin Najeriya kuma abokan aikin marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (rtd) sun yi kira da a yi wa tsarin tsaron Najeriya garambawul bayan rasuwar tsohon Janar ɗin a hannun wasu ƴan bindiga da suka sace shi a jihar Katsina.
Sun yi wannan kira ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata yayin wani taron manema labarai a Kaduna wanda Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi (rtd) ya yi magana a madadin abokan aiki da kuma makusantan marigayin.
Da ya ke magana yayint aron Brig.-Janar Maharazu Tsiga (rtd), tsohon darakta-Janar na hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), ya yi kira da a ɗauki ƙwararan matakai don magance matsalar rashin tsaro a ƙasar.
A cewar sa, ana buƙatar a ƙddamar da dabarun da za a bi don wargaza ayyukansu da kuma dawo da zaman lafiya.
"Waɗannan mutane ƴan adam ne kamar mu; suna tsoron mutuwa kuma suna tsoron a fuskance su gaba da gaba. Idan muka kawar da tsoro ta a zukatan mu kuma muka fuskanci su da gaske, za mu sami sakamako mai ma'ana fiye da tattaunawar da babu ranar ƙarewa," in ji shi.
Da yake bayanio kan lokacin da ya kwashe a hannun ƴan bindiga, Tsiga ya ce da wuya ƙungiyoyin ƴan ta'adda da yan bindiga su miƙa wuya bisa radin kansu ta hanyar tattaunawa.














