Michael Flynn: Trump ya yafe wa jami'in da ya kira "tsarkakakke"

Former national security adviser Michael Flynn pictured in 2018

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Shugaban Amurka Donald Trump ya yafe wa tsohon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Michael Flynn.

Mista Flynn ne mutumin da ya amsa laifin shirgawa hukumar tsaro ta FBI karya dangane da zargin da ake yi masa na mu'amala da jami'an Rasha a kokarin yin kutse a zaɓen shugaban kasar na 2016

Shugaban ya kira matakin nasa a matsayin "abin alfahari".

Mista Flynn na cikin makusantan shugaba Trump da ma'aikatar shari'a ta Amurka ta samu da laifin taimakawa hukumomin Rasha, wajen yin kutse a zaɓen Amurka na shekarar 2016 da zummar taimaka wa Trump.

A shekarar 2017 ne ya amince cewa ya yi wa hukumar FBI ƙarya dangane da hulɗa da jakadan Rasha a kan wannan manufa.

Fadar White House ta ce yafiyar za ta kawo ƙarshen tsangwamar mutumin da ta kira a matsayin "Tsarkakakke."

Cikin wata sanarwa, fadar ta ambaci Flynn a matsayin wanda tuggun ƴan siyasa ya rutsa da shi.

Mista Flynn ya mayar da martani ta hanyar wallafa wani saƙo da ke ɗauke da tutar Amurka da wata aya ta Baibul.

Ayar ta ce: "Za su yi yaƙi da ku amma ba za su ci nasara a kanku ba, domin ina tare da ku, zan cece ku, in ji Ubangiji."

Magoya bayan Mista Flynn na ganinsa a matsayin wanda aka yiwa sharrin siyasa a gwamnatin Obama mai barin gado a wancan lokacin don nuna gwamnatin shugaba Trump ba halastacciya ba ce.

Wani bincike na tsawon watanni 22 na sashen shari'ar Amurka a shekarar 2019 ya ce babu wata hujja da za ta tabbatar da cewa Mista Trump ko wani daga cikin muƙarrabansa sun haɗa kai da Kremlin don cin zaɓen 2016.

A farkon wannan shekarar, Mista Trump ya sauya hukuncin da kotu ta yanke wa ɗaya daga cikin makusantansa wato Roger Stone, wanda shi ma aka same shi da laifin yi wa majalisa karya, da kuma kawo tsaiko ga bincikenta dangane da wannan batu.