Zaɓen Amurka na 2020: Aminan Trump sun matsa masa lamba ya amince da shan kaye

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Manyan abokan Donald Trump sun shawarce shi da ya manta da yunƙurinsa na ƙoƙarin kawo tutsu ga nasarar da zaɓaɓɓan shugaban ƙasar Joe Biden ya yi.
Tsohon gwamnan New Jersey Chris Christie ya bayyana matakin da Trump ke shirin ɗauka a matsayin "wani abin kunya ga Amurka".
Shugaba Trump ya ƙi amincewa da faɗuwar zaɓen da ya yi, yana kuma ci gaba da ikirarin maguɗin zabe, zargin da ya gaza gabatar da hujja a kansa.
Da yawa daga cikin magoya bayan jam'iyyar Republican sun nuna goyan bayansu ga matakin shari'ar da ya ɗauka, sai dai wasu ƙalilan waɗanda adadinsu ke ƙaruwa sun yi watsi da wannan mataki.
A ranar Asabar ne Trump ya fuskanci wani mummunan abin kunya a jihar Pennsylvania, bayan da wani alƙali ya kori ƙarar da kwamtin neman zaɓensa ya shigar na son a soke miliyoyin ƙuri'un da aka kaɗa ta gidan waya.
A wani tsattsaurin hukunci, Mai Shari'a Mattew Brann ya ce an gabatar wa da kotu "wata ƙara da babu ƙwararan shaidu da za su goyi bayan zarge-zargen da ke cikinta".
Wannan mataki ya matuƙar share hanya kan tabbatar da nasarar Mista Biden a Pennsylvania a ranar Litinin - zaɓaɓɓen shugaban jami'iyyar Democrat wanda ke jagorantar zaɓen da kuri'a 80,000.
Amma duk da haka kwamitin neman zaɓen Trump na yunƙurin ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci.
A ƙuri'ar wakilai da aka kaɗa Mista Biden ya kayar da Shugaba Trump da kuri'a 306, Trump na da 232, wadda kuma da ita ce ake gane wanda ya lashe zaɓen - kuma tuni ya haura ƙuri'a 270 da ake buƙata don hakan.
Mece ce matsalar matakin shari'ar da Trump ya ɗauka?
Da yake magana da kafar yaɗa labarai ta ABC a ranar Lahadi, tsohon gwamnan New Jersey Mista Christie ya ce, babu wata jayayya wannan matakin na Shugaba Trump ba ƙaramin abin kunya ba ne ga Amurka".
Ya ce ko da yaushe kwamitin neman zaɓen Trump na zargin an yi maguɗin zaɓe "a waje ba a cikin kotu ba, amma da sun shiga ɗakin shari'a sai su kasa tabbatar da wannan zargi".
"Ni magoyin bayan shugaban ne, na zaɓe shi har sau biyu. Amma sakamakon zaɓe gaskiya ne, kuma ba za mu ci gaba da nuna kamar abin da ya faru bai taɓa faruwa ba sai a kanmu."

Asalin hoton, EPA
Mista Chritie ne mutum na farko da ya fara nuna goyon bayansa ga takarar Shugaba Trump a 2016. Kuma ya taimaka wa shugaban Amurka yayin muhawara da suka yi da Mista Biden a farkon wannan shekara.
Sidney Powell ta sanya shi cikin masu sukar Trump, wadda ita ce ta jagoranci taron manema labaran tawagar lauyoyinTrump a ranar Talata, sai dai ba a gabatar da wata hujja ba kan wannan zargi, cewa an ƙara wa mista Biden miliyoyin ƙuri'u ta gidan waya.
Sai dai a ranar Lahadi kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump ya nisanta kansa da wannan maganganu na Misi Powell, yana cewa "tana ɗaukar doka ne a hannunta" kuma " ba ta cikin kwamitin lauyoyin Trump".
Sai dai a wani saƙon Twitter da ya aika, Shugaba Trump ƙarara ya bayyana sunanta cikin tawagarsa.
A ranar Lahadi wasu ƴan jam'iyyar Repulcan sun shawarci Trump da ya haƙura da turjiyar da yake.
Gwamnan Maryland Larry Hogan ya shaida wa CNN a ranar Lahadi cewa, wannan faɗi tashin da kwamitin zaɓen Trump ke yi kan sakamakon zaɓe, "zai mayar da mu kamar jam'iyyar wasan yara".
A wani sakon Twitter da ya wallafa a baya, Gwamna Hogan ya ce Shugaba Trump ya daina wani "borin kunya kawai ya yarda ya sha ƙasa".
Me kwamitin Joe Biden ya sanya a gaba?
Shi dai Joe Biden na ci gaba da shirye-shiryen kama aiki, duk da cewa Trump yaƙi amincewa da kayen da ya sha, wanda hakan ke neman kawo ruɗani wajen shirye-shiryen karɓar mulkin
Zai sanar da sunan ministansa na farko a ranar Talata, kuma ana cewa ƙwararran masanin diflomasiyyar nan Antony Blinks mai shekara 58 za a sanar a matsayin sakataren gwamnati, wanda wannan ba ƙaramin babban matsayi ba ne a gwamnatin Amurka.
Mista Blinken ya daɗe a matsayin mataimakin na musamman ga Mista Biden, ya kuma rike mukamai da dama a ma'aikatar harkokin wajen Amurka a lokacin Obama.

Asalin hoton, Reuters
Zaɓen Ron Klain da Mista Biden ya yi a matsayin shugaban ma'aikatan Fadar White House na nufin gwamnatin Shugaba Trump ta fara shirin miƙa mulki.
"Da dama daga Amurkawa sun yi nuna ƙinsu da gwamnatin Shugaba Trump, kuma tun daga nan ne Trump ke Allah-awadai da dimokradiyya." ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta ABC.
Ya kuma bayyana cewa, kwamitin Biden na sassauta buri kan bikin rantsarwar da za a yi a ranar 20 ga watan Janairu saboda ƙazantar da annobar korona ke ƙara yi.











