Zaɓen Amurka na 2020: Me zai faru idan Trump ya ƙi fita daga Fadar White House?

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Trump na Amurka ya sha kaye a kokarinsa na neman wa'adin mulki na biyu
An wallafa

A tarihin Amurka mai tsawon shekara 244, ba a taɓa samun shugaban da ya ƙi amincewa ya bar fadar Shugaban Ƙasa ba bayan ya faɗi a zabe.

Hanyar da aka saba da ita tsararriya kuma wadda doka ta samar ta mika mulki cikin lumana na ɗaya daga cikin ginshiƙan tsarin dimokuradiyyar Amurka masu ƙayatarwa.

A kan wannan dalilin ne sanarwar da Donald Trump ya fitar cewa ya ki amincewa da sakamakon zaben da Joe Biden ya kayar da shi ya haifar da wani yanayin mai ɗaure kai - irin wanda ba a taɓa gani ba a ƙasar.

Yanayin ya kuma tayar da wasu batutuwan da a baya ba a taɓa fuskanta ba a siyasar ƙasar.

"Ba a kammala zabe ba"

Shugaban Trump na buga wasan Golf a wajen birnin Washington DC lokacin da yawancin kafofin yada labarai suka bayyana cewa Joe Biden ya yi nasara ranar 7 ga watan Nuwamba.

Jim kadan bayan faruwar haka, sai ofishin yakin neman zaben shugaban ya fitar da wata sanarwa da ke nanata matsayar shugaban cewa "ba a kammala zaben ba."

Donald Trump playing golf.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trump na wasan Golf lokacin da aka bayyana Joe Biden ya yi nasara

"Dukkanmu mun san dalilin da ya sa JOe Biden ke ruge-rugen yin karyar shi ne ya lashe zabe, kuma abokansa 'yan jarida na taimaka ma sa: ba sa son a bayyana gaskiyar lamarin," kamar yadda ya ce cikin wata sanarwa. "Har zuwa yanzu ba a gama wannan zaben ba."

Tsarin mulkin Amurka ya fayyace cewa wa'adin mulkin shugaba mai ci zai kare ne "ranar 20 ga watan Janairu da karfe 12 na rana."

Joe biden ya lashe fiye da kuri'u 270 na wakilan masu zabe wadda aka fi sani da Electoral College. Saboda haka yake da damar zama shugaban kasa na shekara hudu mai zuwa.

Trump with his team in the White House's Oval Office

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Me zai faru idan Trump ya ƙi fita daga Fadar White House?

Muƙamin da aka tallata

Dama can Trump ya sha bayyana cewa ba zai amince da sakamakon zabe ba idan bai sami nasara ba.

Saboda haka kasar ta fara duba matakan da za a iya dauka idan ya kafe cewa ba zai sauka daga karagar mulki ba.

Wannan abu ne da Joe BIden ma ya tabo yayin da ake yin zabe.

A wata hira ta talabijin da yayi da mai wasan barkwancin nan Trevor Noah ranar 11 ga watan Yuni, ya bayyana abin da zai iya faruwa idan Trum ya ki mika ficewa daga fadar shugaban kasa.

"Lallai na yi tunanin aukuwar haka," inji Biden, kuma ya kara da cewa ya san sojojin kasar za su dauki matakin hana shi ci gaba da zama a Fadar White House.

Donald Trump with a member of the Secret Service at the White House

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Idan ya ki ficewa daga Fadar White House, dakarun da ke tsaron lafiyarsa na iya tilasta ma sa yin haka.

Kuma tun da alamun nasarar Biden a fagen zabe suka bayyana, jami'an tsaron da aka ba shi sun karu zuwa kusan daidai da na shugaban kasa, duk da Trump ma cewa an kayar da dan jam'iyyar Democrat din.

Shin akwai yiwuwar ɓarkewar rikici yayin jiran Trump ya sauka?

Wani malamin jami'a ya bayyana fargabarsa kan halin da kasar za ta iya shiga.

Farfesa Rudesill ya ce; " Na yi rubuce-rubuce kan yiwuwar Shugaba Trump zai yi amani da dokar shugabna kasa, ko ya yi amfani da ma'aikatar shari'a ta kasar wadda abokansa na siyasa ne ke iko da ita, domin bangaren shugaban kasar ya ci gaba da hulda da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai ya ce wannan ba abu ne da zai karbu ba a wajen 'yan kasar.

"A bukaci sojoji su ci gaba da sara wa shugaban bayan karfe 12 na rana na yinin 20 gawa tan Janairu zai sanya su cikin tsaka mai wuya."

A Trump follower in Minnesota on 7 November

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rikici na iya barkewa a Amurka idan Shugaba Trump ya ki sauka daga mukaminsa.

Masu nazarin siyasar Amurka na ganin rikici na iya barkewa a Amurka idan Shugaba Trump ya ki sauka daga mukaminsa.

BBC ta lura da yadda a wasu biranen Amurka, masu zanga-zanga suka rika bayyana dauke da muggan makamai suna nuna goyon bayansu ga shugaban. Wannan matashiya ce ga irin rikicin da ka iya barkewa wanda zai biyo bayan dambarwar siyasar da ke faruwa a Amurka.

raya separatoria