Najeriya da Ghana: Abokan hamayya kan dafa-duka za su kece raini don neman zuwa Gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Oluwashina Okeleji
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Marubuci kan wasanni a Najeriya
- An wallafa
Da ka ji an ambato Najeriya da Ghana abu biyu ke zuwa ran mutum cikin abubuwa da dama - hamayya kan kwallon ƙafa ko wanda ya fi iya shinkafa dafa-duka.
Duk da cewa muhawarar da ake tafkawa kan wanda ya fi iya girka shinkafa ta yi jajir, ta ji kayan ƙamshi abu ne da aka gagara samun maslaha a kansa, cacar-bakin da ake yi kan tamaula akalla ana iya samun mafita ta ɗan wani lokaci, idan aka kece-raini a filin wasa a ranakun 25 da 29 ga watan Maris.
Ƙasasashe biyu za su soma karawa ne a birnin Kumasi a ranar 25 ga watan Maris, yayin da makomar kowacce daga jikinsu ke cikin ƙila-wa-ƙala - wannan ne kuma karo na 50 da ake irin wannan karawar ta hamayya tsakanin manyan ƙasashen a Yammacin Afirka.
Wannan ita ce haɗuwar su ta farko bayan shekara 11 kuma ta farko a gasar neman gurbin shiga wasannin cin Kofin Duniya tun 2001.
Kwana hudu bayan wasan farko, Najeriya za ta karɓi baƙwancin gasar a karo na biyu a Abuja domin tantance ƙasar da za ta je Qatar 2022.
Tawagar Super Eagles na fatan samun nasarar zuwa gasar cin Kofin Duniyar a karo na hudu a jere, sannan sau shida a tarihi baki ɗaya, yayin da Ghana - da ta samu gurbin zuwa kasar sau uku - na fatan sake samun gurbi bayan rashin nasara da ta yi a hannun Rasha a 2018.
Babbar yaya, nasara kalilan
Akwai wasu wasanni kalilan da ke kunshe da wasu al'adu da suka yi tasiri wajen sosa rai a karawar Najeriya da Ghana.
Ƙasashen biyu sun tsaya wa juna kai da fata wajen yaƙin neman 'yanci daga turawan mulkin-mallaka a shekarun 1950, yayin da Ghana ke da al'ummarta mai yawa da ke ci-rani a Najeriya har zuwa shekarun 1980.

Asalin hoton, Getty Images
Idan aka taɓo batun yawan al'umma, Najeriya ke da al'umma mafi yawa a Afirka da mutum kusan miliyan 200 - don haka ita ce babba a tsakanin ƙasashen biyu.
Sai dai a ɓangaren ƙwallo, Ghana ta fi taka rawar gani saboda ta lashe kofin Afirka sau 4 sama da Najeriya mai 3, sannan ta taɓa kai matakin kwata fainal a gasar cin Kofin Duniya, sannan ta yi wa Najeriya ci 21-10 a karawarsu.
Akasarin wannan nasara ta same su ne a lokacin da Ghana ke kan ganiyarta a nahiyar Afirka tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980, amma karambatta tsakaninsu ta kasance mai zafi tun daga 1992 lokacin wani ci da tawagar Black Stars tayiwa Super Eagles 2-1 a wasan dab da na karshe na cin kofin nahiyar Afrika.
Najeriya daga wancan lokaci ta buɗe wuta wajen rike kambun Afirka a 1994 da 2013 kari kan wanda ta lashe a 1980, yayin da Ghana - wadda ta lashe kofin sau hudu - rabonta da nasara a gasar cin kofin Afirka tun 1982, kusan shekaru 40 kenan tana fafutika.
Wasa da zuciya
Gabanin karawar su mai zafi, Ghana ta rika jan-kafa wajen sanar da tawagar 'yan wasanta da za su fafata, a wani sabon salo na sauya tunanin Najeriya ko sanin irin 'yan wasan da za su fuskanta.
"Kuma sun rikice sosai," a cewar shugaban hukumar ƙwallon kafar Ghana, Sammy Anim Addo a tattaunawar sa da BBC kafin sanar da tawagarsu a farkon wannan makon.
"Ba za mu iya ci gaba da maimata abu guda ba a kullum, kuma a karon farko muna ganin wannan tsari ne da muke da yaƙinin zai yi mana aiki. Za mu doke Najeriya domin nasarar zuwa Qatar."
Karkashin jagorancin sabon kocinta Otto Addo da tsohon ɗan wasan Tottenham Chris Hughton da ke kula da harkokin tawagar a matsayin darakta, Ghana za ta buga wannan wasa ba tare da Kyaftin dinta da ke fuskantar dakatarwa ba Andre Ayew.
Ita ma Najeriya akwai 'yan wasanta da ba za su fafata a wasan ba irinsu Alex Iwobi, da ɗan wasan Leicester City Wildred Ndidi da ya ji rauni, amma kuma akwai wani ɗan wasan Leicester Ademola Lookman da ya sauya sheƙa daga Ingila ake ganin zai buga wasan.

Asalin hoton, Getty Images
Magoya bayan Super Eagles dai zakuwar da suke nunawa da kwarin-gwiwa kan nasarar Najeriya ta ragu sosai tun da aka fitar da jadawalin karawar a watan Janairu.
A wannan ranar ana kallon Ghana a masatyin ɗaya daga cikin ƙasashen da ake ji da su, sai dai tawagar da ta lashe gasar kofin Afirka sau hudu an kore ta daga gasar cin kofin nahiyar Afrika a Kamaru.
Ghana ta dawo gida bayan kasancewa can karshen teburi a rukunnisu na C - inda Comoros ke gaba da ita - kuma sun yi rashin nasara a wasanni uku, ciki har da doke ta da ɗan karamin tsibirin ya yi.
Yayin da ita kuma Najeriya ta lashe dukkanin wasanninta uku da ta buga a matakin rukuni kuma ta kasance ta ɗaya a saman teburi abin da ya ba ta damar zuwa wasan zagaye na biyu na kasashe 16 da suka yi saura.
Sai dai tawagar da koci Augustine Eguavoen ke jagoranta an yi mata wani ci guda mai ban haushi wanda ya jijigata cikin yanayi na mamaki a hannun Tunisia a zagaye na biyun.
"Na dauki laifin abin da ya faru a Kamaru, amma abubuwa za su sauya a karawar mu da Ghana," a cewar Eguavoen lokacin tattaunawarsa da BBC.
"Abin da ba za mu yi wasa da shi ba shi ne gurbin wasan cin kofin duniya, domin babu abin da ya zarta hakan a yanzu. Na zabi mu sassauta maganganunmu mu mayar da hanakali kan filin wasa."
Daɗaɗɗiyar hamayya
Hamayya tsakanin Ghana da Najeriya ba wai sabon abu ba ne, daɗaɗɗiyar al'ada ce tsakanin ƙasashen biyu.
Ghana ta kasance kasar bakar-fata ta farko da ta samu 'yanci daga turawa a 1957, ita kuma Najeriya ta samu nata 'yanci ne a 1960; 'yan Najeriya dai na ganin su ya kamata a soma bai wa 'yanci saboda ba za a haɗa girmar kasar da Ghana ba.
Ƙasashen ba su haɗa iyaka ba saboda akwai ƙasashe irinsu Togo da Benin tsakaninsu, sai dai hamayyarsu da abokanta na inganta a kullum saboda harshen su ɗaya wato Turancin Ingilishi kuma sai ya kasance zagaye suke da makwaɓta masu Faransanci.

Asalin hoton, Getty Images
Hamayyarsu ta ƙwallo ta soma ne tun lokacin da suke fafutikar neman 'yanci, lokacin da Ghana ta lashe wasan sada zumunci a shekarun 1950, ciki harda lalasa tawagar Najeriya ta wancan lokaci da ake kira Red Devils da ci 7-0 a watan Yunin 1955.
Rikicin siyasa tsakanin ƙasashen na yammacin Afirka 'yan uwan juna ya soma ne lokacin da gwamnatin Ghana a 1969 ta buƙaci duk mutumin da ke zaman kasar ba shi da takardu ya fice.
Duk da cewa akwai 'yan sauran ƙasashe irinsu Togo da Burkina da Ivory coast da kuma Najeriya da ma wasu 'yan kasashen yammacin Afirka da ke zama a ƙasar - 'Yan Najeriya - galibi yarbawa - su suka fi yawa cikin bakin da ke zama a Ghana a wannan lokacin suna ci-rani.
Galibinsu na rayuwa a Ghana tsawon shekaru har an kai ga zuri'arsu ta farko ta gushe an shiga ta biyu da Uku, kuma 'yan Najeriya da suka wahala wajen dawowa gida - na ganin an tsara wannan abu ne saboda su.
Abubuwa sun sauya lokacin da arzikin man Najeriya ya bayyana, sannan tattalin arzikin Ghana ya ruguje, ma'ana daga shekarun 1974 yawan 'yan Ghana da ke tuɗaɗowa Najeriya neman aiki sun karu.
Bayan kusan shekara 10, tattalin arziki Najeriya ya shiga walagigi saboda matsalar da aka samu na fitar da fetur a duniya, wannan ya tilastawa gwamnatin umartar 'yan ci-rani sama da miliyan daga yammacin Afirka, akasari Ghana, barin Najeriya cikin kankanin lokaci da aka ba su a 1983.
'Yan ci-rani da suka shiga kasar daga yammacin Afirka suna neman aiki ba tare da takardu ba, a cewar gwamnati suna taka rawa wajen karuwar aikata muggan laifuka.
Waɗannan abubuwa da suka faru musamman na 1983 ya kasance kalmomin zolaye da ake amfani da su a lokacin irin wannan karawa ta hamayya a filin wasa, kuma da alama wasan da za su yi na wannan mako ya dɗn bambanta da wanda aka saba gani.











