Dafadukar wace kasa Yarima Charles na Ingila ya fi so?

Shinkafar Dafaduka
Bayanan hoto, Ana hada dafadukar shinkafa ne da tumatur da kayan kanshi
An wallafa

Yarima Charles na Ingila ya bayyana ra'ayinsa game da mahawarar da ake yi kan ko wace dafaduka ce tafi dadi, amma ya kauce zabar wadda yafi so.

A lokacin da ya isa Najeriya, ya ce:

"Bayan na ziyarci Gambiya da Ghana a makon jiya, to ziyarar mu zuwa Najeriya ta bamu damar kwatantawa - idan akwai wanda zai iya yin wannan gagarumin aikin! - game da wace shinkafa dafaduka ce ta fi dadi...amma domin kaucewa tayar da wata husuma ta diflomasiyya, ina ganin zan kyale kowa ya yanke hukunci da kansa a kan dafadukar da tafi dadi!"

Jamie Oliver shi ne babban mutumin Birtaniya na baya-bayan nan da ya bayyana ra'ayinsa kan dafadukar shinkafar Najeriya da Ghana.

Kalamansa sun sa 'yan kasashen biyu sun hadu wuri guda suna kushe salon girkinsa.

Muna ganin an ankarar da Yarima mai jiran gado Charles game da wannan takaddama ta dafadukar shinkafar Najeriya da Ghana, domin yadda ya ki fitowa fili ya bayyana wadda ya fi so.

Akwai ma wata waka da wata mawakiyar Ghana ta rera akan dafadukar shinkafar Najeriya, wadda a ciki ta ke kushe ta.

Mawakiyar mai suna Sister Deborah ta bayyana cewa kishin da ke tsakanin Najeriya da Ghana ba mai tsanani ba ne - ta ce irin na 'yan uwan juna ne.

Yarima Cherles da Sarki Sanusi

Asalin hoton, Ayo Bello

Bayanan hoto, Yarima Charles da Sarkin Kano Muhammad Sanusi yayin ziyarar yariman mai jiran gado Najeriya ranar Talata