Afcon 2021: Najeriya ce kadai ta hada maki tara a rukuni a bana

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Alhamis aka kammala wasannin zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta Afirka da Kamaru ke karbar bakunci tun daga ranar 9 ga watan Janairu.
Kungiyoyi 16 ne za su ci gaba da fafatawar mataki na biyu, domin neman lashe kofin bana da ake fatan buga wasan karshe ranar 6 ga watan Fabrairu a Yaounde.
Kawo yanzu an buga wasa 36 da kuma cin kwallo 68, kenan ana zura kwallo 1.89 a raga a duk wasa kenan.
Cikin wadanda suka yi bajinta bayan kammala karawar cikin rukuni, Super Eagles ce kadai ta ci dukkan wasanninta da ta kara a bana a rukuni na hudu.
Super Eagles ta fara da cin Masar 1-0 da doke Sudan 3-1 da kuma nasara a kan Guinea Bissau 2-0;
Karon farko da ta yi wannan bajintar tun bayan 2006.
Wadanda suka yi bajinta, bayan kammala zagayen farko:
Wanda ke kan gaba a cin kwallaye: Vincent Abubakar (Cameroon) - kwallo biyar
Tawagar da ta hada maki da yawa: Nigeria - maki tara
Wadda ba ta da maki: Mauritania - ba maki
Wadda ke kan gaba a zura kwallaye: Cameroon - kwallo bakwai
Wadanda suka kasa cin kwallo: Guinea Bissau, Mauritania
Wadda aka zura mata kwallo da dama: Mauritania - kwallo bakwai
Wadda kwallo bai shiga ragarta ba: Senegal











