Qatar 2022: An sauya lokacin buga wasa tsakanin Najeriya da Ghana

Super Eagles

Asalin hoton, MINISTRY OF SPORTS/ FACEBOOK

An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta sanar da takwararta ta Najeriya cewa an sauya ranakun da tawagar Super Eagles za ta kara da Black Stars na Ghana, a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya cikin watan Nuwamba.

Daraktan sadarwa na NFF Ademola Olajire ne ya fitar da sanarwar, wadda ke cewa ''an sauya lokacin da za a buga wasannin share fagen zuwa gasar cin kofin duniya na Qatar 2022 tsakanin Najeriya da Ghana.''

A baya an shirya cewa Super Eagles da Black Stars za su buga gida da waje a ranakun 24 da 27 ga watan Maris.

To amma yanzu za a fara buga wasan farko ne a filin Cape Coast na Ghana a ranar 25 ga watan na Maris, kafin a tafi filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a ranar 29 ga watan na Maris.

Bayan kammala wasannin biyu za a san wanda ya samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar cikin watan Nuwamba.

Kasashen biyu sun dade ana damawa da su a fagen kwallon kafa a nahiyar Afrika, to sai dai tafiyar su bata yi nisa ba a gasar cin kofin nahiyar ta AFCON da ba a jima da kammalawa ba a Kamaru.