Tsananin zafi da ƙarancin ruwa na barazana ga tattalin arzikin Nahiyar Turai
Gwamnatocin ƙasashen Turai na gargadin cewa matsanancin zafi da ƙarancin ruwan sama na haifar da babbar barazana ga tattalin arzikin nahiyar, yayin da ake fuskantar yanayin tsananin zafi karo na biyar a bana.
Wata ministar Faransa, Monique Barbut, ta yi ƙiyasin cewa asarar da wannan yanayi zai haddasa na iya kaiwa biliyoyin daloli.
Haka kuma, yawan ruwan wasu manyan koguna a Turai ya ragu matuƙa, ciki har da Kogin Danube.
Wannan ya tilasta rufe wata tashar samar da wutar lantarki ta nukiliya a Romania, wadda ke samar da kusan kashi 20 cikin 100 na wutar lantarkin ƙasar.
Ana sa ran za a cike giɓin da aka samu ta hanyar ƙara amfani da na'urorin samar da wutar lantarki daga hasken rana da kuma iska.
An saki sojojin Mali 82 da aka yi garkuwa da su
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Mali ta ce ta yi nasarar kuɓutar da sojoji 82 da aka yi garkuwa da su yayin wani mummunan hari da aka kai a arewacin ƙasar a watan Afrilu.
Sojojin na hannun masu garkuwa da mutane tun ranar 25 ga Afrilu, lokacin da ƙungiyar JNIM mai alaƙa da al-Qaeda tare da ƴan aware na ƙabilar Tuareg suka kai hare-hare a wasu wurare a arewacin Mali.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ranar Alhamis, ta ce sojojin da aka sako yanzu suna cikin aminci kuma hukumomin da abin ya shafa na ba su kulawa.
Ta ce an fara shirin kuɓutar da su ne tun bayan kama su, inda aka yi amfani da tsare-tsare da kuma haɗin gwiwar hukumomin tsaro wajen gudanar da aikin.
Mali na fama da hare-haren ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya tun shekarar 2012, musamman a arewa da gabashin ƙasar, inda gwamnati ke fama da matsalar rashin cikakken iko.
A cikin 'yan shekarun nan, ƙungiyar JNIM ta faɗaɗa hare-harenta daga arewacin Mali zuwa tsakiyar da kudancin ƙasar.
Dattijo mai shekara 102 ya mutu bayan an yi masa duka a mashaya
Asalin hoton, PA Media
Wani dattijo mai shekara 102, Phillip Ormerod, ya mutu bayan wani duka da aka kai masa a wata mashaya a kudancin Wales da ke Birtaniya.
An kai Ormerod, wanda ke zaune a Cwmbran da ke Torfaen, asibiti cikin mawuyacin hali bayan lamarin da ya faru a mashayar Crow's Nest ranar 1 ga Agusta.
'Yan sandan Gwent sun tabbatar a ranar Alhamis cewa ya mutu daga baya.
An kama wani mutum mai shekara 56 daga Llanelli bisa zargin shi ne ya yi wa Ormerod mummunan rauni, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin.
Ɗan Ormerod, Robert, ya ce mahaifinsa, wanda ba shi da aure yana zaune ne shi kaɗai, kuma an gano yana fama da cutar mantuwa.
Ya ce mahaifinsa yana yawan zuwa mashayar, inda ya shafe shekaru yana zuwa sau biyu ko uku a mako.
Robert, wanda tsohon injiniyan gine-gine ne, ya ce mahaifinsa sananne ne a wajen matasan da ke zuwa mashayar, har wasu kan saya masa giya idan ya zo.
“Ya kasance mashayin giya, kuma ina ganin wasu mutane suna kallonsa a matsayin abin koyi saboda shekarunsa.”
Musulmai da Kiristocin Najeriya sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya
Asalin hoton, Jamaatu Nasrul Islam
Shugabannin addinin Musulunci da Kiristoci fiye da 50 ne suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin mabiya addinan biyu a Najeriya,
An ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiya da za ta mayar da hankali wajen inganta fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin addinai, a taron da ƙungiyar Musulmi ta Duniya da ke da hedikwata a Saudiyya ta shirya a Abuja.
Yarjejeniyar ta zo ne watanni bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Najeriya da gaza kare Kiristoci daga hare-haren ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi, tare da yin barazanar daukar matakin soji kan ƙasar.
Sai dai ba a yi magana kan kalaman Trump ba a taron da aka sanya hannu kan yarjejeniyar.
Sakatare Janar na ƙungiyar Musulmi ta Duniya, Mohammad Al-Issa, yana cewa dukkanin mabiya addinan biyu na maraba da wannan tsari da ya ce ya "buɗe sabon shafi".
Shugabannin Musulmi da Kiristocin da suka halarci taron sun ce yarjejeniyar za ta iya taimakawa wajen rage kalaman ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.
Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu wajen bikin, ya ce gwamnati ta kuduri aniyar ganin Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunƙulalliyar ƙasa duk da bambance-bambancen da ke tsakaninta.
Za mu fito da ƙarfinmu idan yaƙin ya sake dawowa sabo - Iran
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar juyin juya halin Iran ta yi barazanar ɗaukar matakai masu tsauri da ƙarfin hare-hare idan har wani sabon yaƙi ya sake ɓarkewa tsakanin Iran da Amurka.
Kamfanin dillancin labarai na Fars, ya ambato wani babban jami'in rundunar, Rasoul Sanaei-Rad na cewa:
“Maƙiya na tunanin cewa ta hanyar haddasa rarrabuwar kawuna a cikin gida da matsin tattalin arziki za su iya maimaita irin abubuwan da suka faru a watan Janairu, kuma suna ɗaukar matakan cimma wannan buri.”
A jiya kuma, mataimakin babban hafsan hafsoshin sojojin Iran, Alireza Sheikh, ya bayyana cewa ƙasarsa ta shirya domin dogon yaƙi da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan soji.
Ya ce manufar tsaron Iran ta sauya daga ta kare kai kawai zuwa manufar hana maƙiyi da kuma ɗaukar mataki kai tsaye idan buƙata ta taso.
Haka kuma ya ce ƙarfin Iran wajen ƙera makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa na daga cikin manyan abubuwan da ke ba ta damar ci gaba da gudanar da ayyukan soji na dogon lokaci.
Kakakin Donald Trump za ta ajiye aiki
Asalin hoton, Reuters
Kakakin Fadar White House ta Amurka, Karoline Leavitt, za ta ajiye mukaminta a ƙarshen wannan wata, kamar yadda Shugaba Donald Trump ya sanar.
Trump ya ce Leavitt, wadda yake kira ɗaya daga cikin mataimakansa da ya fi yarda da su, ta yanke shawarar barin aikin domin samun ƙarin lokaci tare da ƴaƴanta da iyalinta.
Ya ce ya fahimci matakin kuma yana mutunta shawarar da ta yanke.
Trump ya ƙara da cewa Leavitt za ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan masu ba shi shawara a wajen gwamnati, tare da taka rawa wajen jam'iyyar Republican.
Leavitt mai shekaru 28 ta fara aiki a matsayin kakakin Fadar White House a bara, inda ta zama mafi ƙanƙantar shekaru da ya taɓa riƙe wannan matsayi.
Har yanzu ba a bayyana wanda zai maye gurbinta ba.
Leavitt ta haifi ɗiyarta ta biyu a watan Mayu tare da mijinta, Nicholas Riccio. Tana kuma da ɗa mai shekaru biyu.
Ta dawo bakin aiki a watan da ya gabata bayan kammala hutun haihuwa.
Bayan sanarwar Trump, Leavitt ta rubuta a shafin X cewa riƙe mukamin kakakin Fadar White House ya kasance “abin girmamawa da kuma kasadar rayuwa mafi girma” a gare ta.
Firaministan Indiya ya gayyaci Tinubu taron BRICS
Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya gayyaci Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zuwa taron ƙasashen BRICS na bana, a wani mataki na ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban tsakanin asashen biyu.
Gayyatar na zuwa ne bayan Najeriya ta shiga ƙungiyar a matsayin abokiyar hulɗa a 2025.
Sai dai har yanzu ba cikakkiyar mamba ba ce, duk da cewa tana halartar wasu tarurruka da shirye-shiryen ƙungiyar.
Masana na kallon gayyatar a matsayin wata dama da Najeriya za ta yi amfani da ita wajen bunƙasa cinikayya da zuba jari da haɗin gwiwar fasaha da Indiya da sauran ƙasashe masu tasowa.
Babban Jami’in Diflomasiyyar Indiya a Najeriya, Abhishek Singh, ya ce haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya wuce kasuwanci kawai har ma da fannonin makamashi da tsaro da lafiya da noma da fasaha da kuma harkokin tsaron teku.
Iran ce ke da cikakken iko da mashigar Hormuz - Iran
Asalin hoton, Getty Images
Sabon shugaban rundunar Basij, wani reshe ne rundunar juyin juya halin Iran, Hossein Taeb ya ce mashigar Hormuz na ƙarƙashin ikon Iran:
"Mashigar Hormuz tana ƙarƙashin kulawa da ikon Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma ƙasar na ci gaba da tafiya a kan turbar ta cikin cikakken tsaro," in ji shi.
A kwanakin baya ne sabon jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei, ya naɗa Mista Taeb a matsayin shugaban rundunar Basij.
Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran su ce a yau ne Taeb ya kai ziyara birnin Qom domin ganawa da malamai da manyan jagororin addini.
A yayin ziyarar ya bayyana jana'izar tsohon jagoran Jamhuriyar Musulunci a Iraƙi a matsayin wata alama ta “ƙarfin Juyin Juya Halin Musulunci” da kuma “ƙarfin tasirin Iran a yankin.”
Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa Amurka tana da “cikakken iko” a kan mashigar Hormuz.
Air Indiya zai fara gwajin shaye-shaye ga matuƙansa jirginsa
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin jiragen sama na Air India ya sanar da cewa zai fara gudanar da gwajin shan ƙwayoyi na dole ga dukkan matuƙan jiragensa, bayan da wani jirginsa ya ya rasa hanya yayin da yake sararin samaniya.
Daga baya, gwajin da aka yi wa matuƙin jirgin ya nuna cewa ya ha tabar wiwi gabanin tashin jirgin.
A ƙarƙashin dokokin da ake bi a yanzu, kamfanonin jiragen sama suna da wajibcin gudanar da gwajin miyagun ƙwayoyi ga aƙalla kashi 10 cikin 100 na ma’aikatan jirgi a kowace shekara.
Sai dai Air India ta ce sabon tsarin da za ta aiwatar zai bai wa fasinjoji ƙarin ƙwarin gwiwa da tabbacin tsaro yayin tafiye-tafiyensu.
NAHCON ta zaɓi kamfanonin jirage 5 da za su yi jigilar maniyyatan 2027
Asalin hoton, NAHCON/X
Hukumar Alhazan Najeriya, NAHCON ta ce ta zaɓa tare da amincewa da kamfanonin jiragen sama biyar da za su yi jigilar maniyyatan ƙasar na 2027.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta zaɓi jiragen ne bayan jerin tantancewar da ta yi wa kamfanonin jiragen da ya ƙunshi, tsarin tsaron fasinjoji da ingancin jiragen da ma ƙa'idojin kuɗi na kamfanonin.
NAHCON ta ce ta yi amfani da dokokinta da na hukumar kula da sufurin jirage ta Najeriya da na hukumar sufurin jiragen Saudiyya wajen tantance kamfanonin da za su yi jigilar.
Kamfanonin jiragen samar da suka yi nasara a tantancewar su ne:
Air Peace Limited.
Flynas.
Max Air Limited.
Saudi Air.
UMZA Limited.
Ya kamata Amurka ta yi taka-tsantsan kan mashigar Hormuz - Araqchi
Asalin hoton, Getty Images
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce ya kamata Amurka ta “yi taka-tsantsan da bayanan ƙarya kan mashigar Hormuz.”
A wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, wanda ya yi wa jami’an Amurka, Araqchi ya ce Amurka “ta dade tana fama da maimaita kuskuren lissafi sakamakon raunin bayanan sirri da take da su.”
Ya bayyana yaƙin baya-bayan nan da Isra’ila da Amurka suka yi da Iran a matsayin “bayyanannen misali na hakan,” yana mai cewa Amurka “yanzu ta sake yin wani kuskure mafi girma dangane da mashigar Hormuz.”
A ƙarshen saƙonsa, Ministan Harkokin Wajen na Iran ya rubuta cewa:
“Abin da ya fi muni fiye da labarai marasa tushe shi ne bayanan ƙarya. Ku yi hattara.”
Ana ganin wannan jawabi na Araqchi a matsayin martani ga wasu kalaman shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya ce Amurka ce ke iko da mashigar Hormuz.
ADC ta zargi hukumomi da yunƙurin kama Aregbesola
Asalin hoton, Rauf Aregbesola/X
Jam'iyyar ADC mai hamayya a Najeriya ta zargi hukumomin tsaron ƙasar da kitsa kama sakatarenta na ƙasa, Rauf Aregbesola gabanin zaɓen gwamnan jiharsa ta Osun da ke tafe.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta ce ta samu ''sahihan bayanan sirri'' na shirin kama sakataren jam'iyyar na ƙasa, wanda kuma shi ne tsohon gwamnan jihar Osun.
Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta, ko wata hukumar tsaro a ƙasar da ta tabbatar da wannan zargi.
Sai dai jam'iyyar ta bayyana cewa zargin shirin na da matuƙar tayar da hankali, musamman idan aka yi la’akari da abin da ta kira ci gaba da tsoratarwa da muzgunawa da kuma amfani da cibiyoyin gwamnati ta hanyoyin da ba su dace ba don muzguna wa ƴan hamayya.
Aregbesola ya kasance gwamnan Jihar Osun daga shekarar 2010 zuwa 2018, sannan daga ya zama ministan cikin gida zamanin gwamnatin Buhari.
Gwamnatin Sokoto za ta raba wa jami’an tsaro babura 1,000 domin inganta tsaro
Asalin hoton, Gwamnatin jihar Sokoto
Gwamnatin Jihar
Sokoto ta amince da kashe Naira biliyan 1,759,250,000 domin sayen babura ƙirar Bajaj guda 1,000 da za a raba wa hukumomin tsaro a jihar, domin
ƙarfafa yaƙi da ƴanbindiga.
A cewar daraktan janar
na yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, an
amince da wannan buƙatar ne a majalisar zartarwar jihar.
Bawa ya ce, “Sayen
babura guda 1,000 na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka domin ƙara
wa jami’an tsaro kayan aiki da za su taimaka wajen gudanar da ayyukansu a
wuraren da matsalar ƴanbindiga ta fi ƙamari.”
Ya ƙara da cewa
sayen baburan zai kasance ƙarin tallafi ne ga motocin yaƙi masu sulke guda 62
da gwamnatin jihar ta saya kwanan nan, waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan
27.
A cewar Bawa, “Gwamnatin
jihar ta riga ta samar da motocin sulke guda 62 da aka raba wa hukumomin tsaro,
kuma wannan sabon shirin na sayen babura zai ƙara ƙarfafa ayyukan sintiri da
sauran ayyukan tabbatar da tsaro.”
Baya ga batun
tsaro, Majalisar Zartarwar Jihar ta amince da wasu ayyuka da dama da suka shafi
ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa da bunƙasa sana'o'i.
Daga cikin
ayyukan akwai ware Naira miliyan 723,171,671.23 domin gyara makarantar Government Technical College da ke Runjin
Sambo, yayin da aka amince da kashe Naira miliyan 498,995,000 domin gyaran A.A.
Raji Special School.
Haka kuma, an
ware Naira miliyan 489,319,380 domin gyaran kashi na farko na College of
Nursing Sciences, sannan Naira miliyan 229,363,455 domin gyaran dakunan kwanan
dalibai maza da mata na College of Basic and Remedial Studies.
A fannin noma, an
amince da Naira miliyan 174,642,000 domin gyaran gidajen ma'aikata da inganta
katangar College of Agriculture and Animal Science da ke Wurno.
Majalisar ta kuma
amince da Naira miliyan 133,665,861.32 domin gina katangar Wamakko Primary
Health Centre.
A kokarin ƙarfafa
sana'o'in mata, gwamnatin jihar ta amince da kashe Naira miliyan 93,880,000
domin sayen kayan koyon sana'a ga cibiyoyin koyon sana'a na mata guda 46 da ke
faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar.
'Mayaƙan Houthi da na al-Shabab na yunƙurin ƙwace Mashigar Bab al-Mandab'
Asalin hoton, Mohammed Hamoud/Getty Images
Jaridar The Telegraph ta Birtaniya ta wallafa wani rahoto mai taken: "Mayaƙan Houthi na shirin buɗe sabon babi a yaƙin Iran, bayan yunƙurin rufe wata muhimmiyar mashigar ruwa ta biyu."
Jaridar ta ce mayaƙan Houthi, waɗanda a yanzu ake kallonsu a matsayin mafiya ƙarfi cikin ƙungiyoyi masu alaƙa da Iran a yankin, suna shirye-shiryen rufe mashigar Bab al-Mandab domin amfanin Iran, da nufin ƙara matsin lamba kan shugaban Amurka Donald Trump, lamarin da zai iya ƙara jefa tattalin arzikin duniya cikin matsala.
Rahoton ya ce akwai haɗin gwiwa tsakanin mayaƙan na Houthi da ƙungiyar al-Shabaab da ke Somalia, wanda manufarsu ita ce mallake ɓangarori biyu na mashigar Bab al-Mandab tare da rufe ta idan Iran ta yanke shawarar yin hakan.
Rahoton ya ambato wata majiya da ta ce mayaƙan Houthi na miƙa fasahar ƙera da amfani da jiragen sama marasa matuƙa (drones) na Iran ga ƙungiyar al-Shabaab bisa umarnin Tehran.
Manufar hakan, in ji rahoton, ita ce haifar da yanayi a Bab al-Mandab mai kama da wanda ake gani a mashigar Hormuz.
Jaridar ta ce kimanin kashi 10 zuwa 12 cikin 100 na cinikayyar duniya na bi ta mashigar Bab al-Mandab, wadda ke haɗuwa da Mashigar Suez.
Telegraph ta yi gargaɗin cewa idan aka rufe mashigar, jiragen ruwa za su tilasta bin wata hanya ta daban wadda za ta ƙara musu makonni suna zagayawa ta kudancin Afirka, lamarin da zai ƙara kuɗaɗen sufuri.
Al'ummar Zambiya na zaɓen sabon shugaban ƙasa
Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Zambiya na gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin ƙasar.
Ana kallon zaɓen a matsayin ma'aunin gwajin ingancin dimokuraɗiyya a ƙasar mai tarihin 'ɗorewar tsarin dimokuraɗiyya a Afrika.
Shugaban ƙasar Hakainde Hichilemana wanda ke neman wa'adi na biyu na da farin jini sakamakon rawar da ya taka lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki.
Akwai damuwa game da ƙaruwar rashin aikin yi.
Ana ganin za a fafata ne tsakanin shugaban ƙasar da jagoran adawa Brian Mundibile wanda magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu ke mara wa baya.
Ɗan takarar shugaban ƙasa dai na buƙatar sama da kashi 50 na ƙuri'u kafin ya yi nasara.
Amurka ta soki Isra'ila kan ci gaba da zaman sojojinta a Lebanon
Asalin hoton, EPA
Amurka ta yi Allah wadai da ƙawarta Isra'ila, a wani yanayi da ba kasafai ake ganin irinsa ba, bayan ministan tsaron Isra'ila ya dage sojojinsa za su ci gaba da zama a kudancin Lebanon.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana sa rai Isra'ila za ta yi amfani da tsarin yarjejeniyar janye sojoji.
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ne ya yi waɗannan kalamai yayin da ya ziyarci kudancin Lebanon, inda ya tabbatar da yadda sojojinsa ke rusa dukkan gidajen yankin.
Firaministan Lebanon, Nawaf Salam, ya ce ɓarnar da Isra'ila ke yi ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Yarjejeniyar ta ƙunshi janye dakarun Isra'ila daga yankunan yayin da sojin Lebanon za su ƙwace makaman ƴan Hezbollah.
Ministocin Isra'ila na ƙara zafafan kalaman ne a lokacin da zaɓe ke ƙaratowa.
Assalamu alaikum
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Ahamis.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.