Abin da ya kamata ku sani kan wasan Palace da Man United

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United za ta ziyarci Crystal Palace, domin buga wasan Premier League ranar Laraba a Selhust Park.

United tana ta biyu a teburin bana da maki 50, ita kuwa Palace mai maki 33 tana ta 13 a kasan teburin gasar Ingila.

Kungiyoyin sun kara a gasar Premier ranar 19 ga watan Satumba a wasan farko, inda Palace ta doke United da ci 3-1 a Old Trafford.

Palace ta ci kwallayenta ta hannun Andros Townsend da Wilfried Zaha wanda ya ci biyu daya daga ciki a bugun fenariti.

United ta zare kwallo daya ne ta hannun Donny van de Beek, wanda ya shiga karawar daga baya.

Fafatawa tsakanin kungiyoyin biyu:

Crystal Palace ba ta yi nasara a wasa 12 a gida da ta kara da Manchester United tun bayan 1991 ba, wadda ta yi canjaras uku da shan kashi a fafatawa tara.

Manchester United ta ci wasan Premier League hudu a jere da ta fafata a gidan Crystal Palace.

Sai dai watakila Palace ta yi nasara a kan United gida da waje kuma a karon farko a tarihin gasar.

United ta ci wasa biyar daga shida da ta hadu da Palace a Premier har da hudu a baya-bayan nan.

Bajintar Crystal Palace:

Wilfred Zaha

Asalin hoton, Getty Images

Maki 33 da Palace ta hada shi ne mafi yawa da kungiyar ta samu, bayan buga wasa 26 a karon farko tun bayan 1991/92 a lokacin da ta hada maki 36.

Palace ba ta ci wasa ba a karawa 19 a gida da ta yi da kungiyoyin da ke shidan farko a kan teburi, tun bayan doke Chelsea a Oktoban 2017, wadda ta yi canjaras biyar da rashin nasara 14.

Rabin kwallayen da aka zura a ragar Palace a bana wato 21 daga 43 an ci su ne a farkon minti 15 da fara tamaula ko kuma sauran minti 15 a tashi daga wasa.

Palace ba ta yi nasara a wasa 17 a gasar Premier League daga 22 da ta buga idan ba Wilfred Zaha ba, inda ta ci wasa uku da canjaras daya aka doke ta 18 ba tare da Zaha ba.

Kwazon Manchester United:

Ole Gunnar Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images

Wasa daya Manchester United ta yi rashin nasara daga 20 da ta buga a Premier League, inda ta ci 12 da canjaras bakwai.

Har yanzu United ba ta yi rashin nasara ba a wasannin waje a gasar Premier League a bana ba, wadda cikin karawa 20 ta ci fafatawa 13 da zanjaras bakwai.

Ita ce kan gaba a wasannin bana da ta ci kwallo 31, bayan an koma zagaye na biyu wato bayan hutu a Premier League.

United wadda Ole Gunnar ke jan ragama ta ci wasa tara daga 11 data buga a tsakiyar mako a Premier League, ciki har da lashe dukkan karawa shida da ta yi a waje.