Didier Deschamps: Pogba ba zai samu fnatsuwa ba Man United

Asalin hoton, EPA
Paul Pogba ba zai samu kwanciyar hankali a Manchester United ba a halin da ya tsinci kansa, in ji kocin Faransa Didier Deschamps.
Pogba ya buga wa United wasa 11 a kungiyar ta Old Trafford, wacce ta fara karawa biyar da shi a tamaula a bana, sauran a canji yake shiga.
A wasan Everton ma a benci ya zauna, kuma saura minti takwas a tashi daga fafatawar aka saka shi a wasan da United ta yi nasara da ci 3-1 ranar Asabar a Gasar Premier League.
Pogba yana cikin 'yan wasan da tawagar Faransa ta gayyata fafatawar da za ta yi da Finland da Portugal da kuma Sweden.
''Yana cikin yanayin da ba zai samu farinciki a kungiyar ba, ko dai don rashin buga wasanni kamar yadda ya kamata ko kuma gurbin da ake saka shi a wasa'', in ji Deschamps.
''Baya kan ganiyarsa, ya yi fama da jinya ga kuma cutar korona da ta tayar masa da hankali. Ya kamata ya kara sa kwazo a wasanninsa a shekarar nan.
''A nan muna tare ba shi bai da wata damuwa, Daan wasa kan rasa samun kwanciyar hankali a kungiyarsa, amma sai kaga ya samu natsuwar buga wa kasarsa tamaula''.
''Ya kan gayamin damuwarsa kuma kamar yadda na san halinsa, sai kaga ya dauki lamarin da kyakkywar niya.''
Pogba ya sake komawa United da taka leda daga Juventus a 2016 kan fam miliyan 89.
Wasan karshe da ya yi wa Faransa shi ne a cikin watan Oktoba, ya kuma ce yana mafarkin wata rana zai buga wa Real Madrid kwallo.
Da jin haka sai United ta kara tsawaita yarjejeniyar dan kwallon zuwa shekara daya, wacce za ta kare a karshen kakar 2022.











