Neymar ya bude kofarsa ga Man United

gareth Bale da James Rodriguez

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real madrid na shirye-shiyen kaddamar da wani shiri mai suna Operation 200 a kokarinta na tara kudin sayan Paul Pogba.

A karkashin shirin, kamar yadda Jaridar Sun ta ruwaito, za a sayar da Gareth Bale mai shekara 30 da james Rodriguez mai shekara 28.

AS kuwa ta ruwaito wakilin Pogba din Mino Raiola inda ya ki kawar da yiyuwar komawar dan wasan zuwa Juventus.

Neymar ya bude kofarsa ga Manchester United a yunkurinsa na barin kungiyar PSG ta Faransa ta kowane hali, in ji rahoton jaridar Sun.

Kazalika, Barcelona na duba yiwuwar daukar Neymar din ko kuma ta karbi aronsa, inda daga bisani kuma za ta saye shi cikin shekara guda, kamar yadda Express ta ruwaito.

Sabon kocin Chelsea Frank Lampard ne zai yanke hukunci kan ko za a sabunta kwatarangin Willian a kungiyar. Yanzu dai saura shekara daya yarjejeniyarsa ta kawo karshe a Stamford Bridge kuma Barcelona na son dan wasan kan kudi fan miliyan £30. (Express)

Kocin Leicester City Brenden Rodgers ya gargadi Manchester United cewa akwai iyakar lokaci kan dan wasan bayanta Harry Maguire mai shekara 26, domin kuwa kungiyar ba ta son ta kaskantar da kanta, in ji jaridar Star.

Jaridar Independent ma ta ruwaito shi yana yabon dan wasan cewa "bai damu ba" game da komawarsa Man United din.

Ita kuwa Liverpool da kyar ne idan za ta sayar da Simon Mignolet mai shekara 31 sannan kuma ba ta da niyyar tura shi wata kungiyar a matsayin aro. (Liverpool Echo)

Manchester United sun shiga neman daukar matashin dan wasan tsakiyar Roma mai shekara 20 mai suna Nicolo Zaniolo, in ji Mirror.