Manchester City ta ci wasa na 19 a jere a dukkan fafatawa

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta yi nasarar doke Borussia Monchengladbach da ci 2-0 a wasan zagayen farko a Champions League da suka fafata ranar Laraba.
City ta fara cin kwallo ta hannun Bernardo Silva a minti na 29 da take leda, sannan ta kara na biyu ta hannun Gabriel Jesus bayan zagaye na biyu.
Wannan nasarar ita ce ta 19 da Manchester City ta yi a dukkan karawa a wasannin bana.
Kuma jumulla kungiyar ta Etihad ta yi wasa 26 ba tare da an yi nasara a kanta ba, tun 1-1 da ta buga da West Brom a gasar Premier cikin Disamba, daga nan ta jere wasa 19 ba tare da an doke ta ba.
Wasan da aka yi nasara a kan City shi ne wanda Tottenham ta doke ta 2-0 cikin watan Nuwamba, daga nan ne ta yi wasa 26 ba tare da an doke ta ba.
Kawo yanzu ta yi nasara a wasan Premier League 13 da a Champions League daya da fafatawar Caraboa Cup biyu da kuma FA Cup uku a jerin gumurzu 19 da ci a jere.
City wadda take ta daya a kan teburin Premier League da tazarar maki 10 tsakaninta da Manchester United ta biyu za ta karbi bakuncin West Ham ranar 27 ga watan Fabrairu.
Ga jerin wasa 19 da Manchester City ta ci kawo yanzu a bana:
Premier League 19 ga watan Disamba 2020
- Southampton 0 - 1 Man City
EFL CUP 22 ga watan Disamba 2020
- Arsenal 1 - 4 Man City
Premier League 26 ga watan Disamba 2020
- Man City 2 - 0 Newcastle
Premier League 3 ga watan Janairu 2021
- Chelsea 1 - 3 Man City
EFL CUP 6 ga watan Janairu 2021
- Man Utd 0 - 2 Man City
FA CUP 10 ga watan Janairu 2021
- Man City 3 - 0 Birmingham
Premier League 13 ga watan Janairu 2021
- Man City 1 - 0 Brighton
Premier League 17 ga watan Janairu 2021
- Man City 4 - 0 Crystal Palace
Premier League 20 ga watan Janairu 2021
- Man City 2 - 0 Aston Villa
FA CUP 23 ga watan Janairu 2021
- Cheltenham 1 - 3 Man City
Premier League 26 ga watan Janairu 2021
- West Brom 0 - 5 Man City
Premier League 30 ga watan Janairu 2021
- Man City 1 - 0 Sheff Utd
Premier League 3 ga watan Fabrairu 2021
- Burnley 0 - 2 Man City
Premier League 7 ga watan Fabrairu 2021
- Liverpool 1 - 4 Man City
FA CUP 10 ga watan Fabrairu 2021
- Swansea 1 - 3 Man City
Premier League 13 ga watan Fabrairu 2021
- Man City 3 - 0 Tottenham
Premier League 17 ga watan Fabrairu 2021
- Everton 1 - 3 Man City
Premier League 21 ga watan Fabrairu 2021
- Arsenal 0 - 1 Man City
Champions League 24 ga watan Fabrairu 2021
- Borussia Munchengladbach 0 - 2 Man City











