Wadanne kungiyoyi ne za su fara Gasar Zakarun Turai?

Champions League final Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Real Madrid ce ta dauki kofin a kakar bara bayan ta doke Liverpool a wasan karshe na gasar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A ranar Talata ne kungiyoyin gasar Firimiya biyu, Liverpool da Spurs, za su fara wasansu a gasar Zakarun Turai, a ranar da ake fara gasar ta wannan kakar.

Tottenham ce za ta fara karawa da Inter Milan ne da misalin karfe 5:55 agogon Najeriya, a kasar Italiya.

Ita kuwa Liverpool za ta karbi bakuncin PSG ne a gida a wasan da za su buga karfe 8:00 na dare agogon Najeriya.

Kungiyar Barcelona ta Messi kuwa za ta karbi bakuncin PSV Eindhoven a wasan da za su yi karfe 5:55 na yamma agogon Najeriya.

Borussia Dortmund za ta kai ziyara Club Brugge ne a wasan da za su fafata da karfe takwas agogon Najeriya.

A karfe 8:00 agogon Najeriya da Nijar din ne dai Monaco za ta kara da Atletico Madrid, Red Star Begrade da Napoli, Shalke da FC Porto ita kuma Galatasaray za ta kara da Locomotic Moscow.

Yadda 'yan wasan gaban Liverpool da PSG suka ci kwallo a kakar 2017-2018
Bayanan hoto, Yadda 'yan wasan gaban Liverpool da PSG suka ci kwallo a kakar 2017-2018

Dan wasan gaba na kungiyar Spurs, Harry Kane, ya ce kungiyarsa tana bukatar ta wuce inda ta kai a gasar bara.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Kane ya ce lokaci ya yi da ya kamata kungiyarsa ta sake zage dantse.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Real Madrid's Spanish coach Julen Lopetegui (C) takes part in a training session at the Valdebebas training ground in Madrid on September 18, 2018 on the eve of the UEFA Champions' League football match Real Madrid CF against AS Roma.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kocin Real Madrid Julen Lopetegui yana atisaye tare da 'yan wasansa a filin atisaye na Valdebebas a Birnin Madrid ranar Litinin, kwana guda kafin fara gasar Zakarun Turai