'Yan 16 da za su buga zagaye na biyu a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An samu kungiyoyi 16 da za su buga zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League ta bana.

Wadanda suka ja ragamar rukuninsu sun hada da Bayern Munich da Chelsea da Borussia Dortmund da Juventus da Liverpool da Manchester City.

Sauran sun hada da Paris St Germain da kuma Real Madrid.

Wadanda suka yi na biyu a rukunai sun hada da Atalanta da Atletico Madrid da Barcelona da Lazio da RB Leipzig da Borussia Monchengladbach da FC Porto da kuma Sevilla.

Kunyiyoyi uku ne a Ingila suka kai zagayen gaba da suka hada da Manchester City da Chelsea da kuma Liverpool, bayan da ka fitar da Manchester United.

Spaniya kuwa kungiyoyi hudu ne ke wakiltarta da suka hada da Real Madrid da Barcelona da Atletico Madrid da kuma Sevilla.

Jamus ma tana da kungiya hudu da suka hada da mai rike da kofi Bayern Munich da Dortmund da Monchengladbach da kuma RB Leipzig.

Juventus da Atalanta da kuma Lazio ne ke wakiltar Italiya, bayan da aka yi wajerod da Inter Milan.

Paris St Germain ce kadai daga Faransa da kuma FC Porto daga Portugal.

Za a raba jadawalin wasannin zagaye na biyu ranar Litinin 14 ga watan Disamba a birnin Nyon, Switzerland.

Manchester United da za ta koma buga Europa League itama Krasnodar da Club Brugge da kuma Dynamo Kiev za su koma gasar ta bana.