Benzema ya kai Madrid zagayen gaba a Champions League.

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta kai zagayen gaba a gasar Champions League, bayan da ta doke Borussia Monchengladbach da ci 2-0 ranar Laraba.

Karin Benzema ne ya ci wa Real kwallon farko a minti na tara da fara wasa, sannan ya kara na biyu saura minti 13 su je hutu.

Dan kwallon Faransa ya kuma yi kan-kan-kan da Roberto Carlos wajen buga wa Real wasa 527.

Kuma kwallo biyun da ya ci a ranar Laraba ya sa yana da 257 a raga.

Cristiano Ronaldo shi ne na farko kan ci wa Madrid kwallaye da 451 a raga, Raul da 323, sai Alfredo di Stefano da 308 da kuma Santillana da ya ci 290.

Da wannan sakamakon Real ce ta ja ragamar rukuni na biyu da maki 10, sai Monchengladbach ta biyu da makinta takwas.

Shakhtar Donesk ma maki takwas ne da ita a matsayi na uku, sai Inter ta hudu ta karshe mai maki shida.

'Yan wasan Real 21 da ta fuskanci Borussia Monchengladbach.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da E. Militão da Sergio Ramos da R. Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Isco da kuma Arribas.

Masu cin kwallo: Benzema da Asensio da Lucas V. da Vini Jr. da kuma Rodrygo.