Sojoji sun zama likitoci a Zimbabwe

Asalin hoton, Getty Images
Mahukunta a Zimbabwe sun tura sojoji likitoci zuwa asibitocin gwamnati bayan ma'aikatan lafiya sun fara yajin aiki a fadin kasar.
Likitocin kasar sun kaurace wa asibitoci a ranar Talata bisa zargin sace shugaban kungiyarsu, Peter Magombeyi.
A makonnin da suka gabata, Dokta Magombeyi ya sha kiran likitocin kasar su shiga yajin aiki saboda rashin kyan albashi da yanayin aiki maras kyau.
A ranar Asabar, ya tura sakon WhatsApp cewa wasu mutum uku sun sace shi. Daga nan ba'a kara ganin shi ba.
Wani minista a kasar, Kazembe Kazembe, ya ce babu wani abun da ke nuna cewa sace shugaban likitocin aka yi.
Amma likitocin sun ce ba za su koma bakin aiki ba sai an gano shugaban nasu.
Ministan lafiyar kasar, Obadiah Moyo, ya ce likitoci sojoji za su kula da marasa lafiya a asibitoci a matakin wucin gadi.






