An ba likita $150,000 domin ayyukan jin kai

Dokta Evan Atar na Sudan ta Kudu

Asalin hoton, HANNAH MCNEISH

An wallafa

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta zabi wani likitan Sudan ta Kudu a matsayin wanda ya lashe kyautar Nansen ta wannan shekarar.

Hukumar kan mika wannan lambar yabon ne ga mutumin da a ganinta ya kamanta wata bajinta wajen taimaka wa jama'ar da rikici ya raba da muhallansu.

An ba likitan dala 150,000 na Amurka domin inganta ayyukan jin kai da yake yi.

Likitan fidan mai suna Dokta Evan Atar na da wani asibiti a garin Bunj da ke arewa maso gabashin Sudan ta Kudu.

Wannan asibitin ne daya tilo da ke aiki a yankin kuma ya kan kula da kusa mutum dubu 250, wadanda yawancinsu yakin basasar kasar da yunwa sun raba su da muhallansu.

Asibitin Dokta Atar kan yi ayyukan fida da suka kai guda 58 a kowane mako., bayan da lura da masu cutar AIDS wato SIDA da tarin fika. Sannan asibitin na kula da amata masu juna biyu da masu haihuwa.

Kana asibitin na aiki na sa'a 24 ne a kowace rana, kuma gadon kwanciya yayi karanci matuka.

Aiki ne mai bukatar dukkan lokacin da Likita Evan ke da shi, lamarin da ya shafi dangantakarsa da iyalinsa wadanda ke zaune a kasar Kenya, kuma ya kan yi watanni ba tare da ya gansu ba.

Yakin basasan kasar wanda ya fara jim kadan bayan kasar ta sami 'yancin kanta a 2011, ya saka kashi daya cikin uku cikin wani mawuyacin halin rayuwa.