Abubuwan da suka faru a Nigeria da sassan duniya kan coronavirus

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya, musamman rahotanni kan annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Karshen rahotannin kenan

    Masu bibiyarmu karshen rahotannin kenan.

    Muna godiya da kasancewa tare da mu tare da fatan Allah ya kawo mana karshen wannan annoba.

    Umar Mikail ke cewa mu zama.

  2. Labarai da dumi-dumi, Masu coronavirus a Nigeria sun haura 100

    An samu karin mutum 14 da suka harbu da cutar coronavirus a Najeriya, abin da ya kai jimillar adadin zuwa 111 a kasar, a cewar hukumar NCDC.

    Tara daga cikin wadanda suka kamun a Jihar Legas suke, biyar kuma a Abuja.

    Zuwa karfe 9:30 na daren Lahadi, mutum 111 ne suka kamu da cutar a Najeriya, yayin da mutum daya ya mutu kuma aka sallami uku.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Labarai da dumi-dumi, Buhari ya saka dokar hana fita a jihohin Abuja, Legas, Ogun

    Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    "Bisa shawarar da Ma'aikatar Lafiya da hukumar NCDC suka bayar, na yi umarni da a dakatar da duk wata zirga-zirga a Jihar Legas da Abuja na tsawon mako biyu da zai fara daga 11:00 na daren Litinin 30 ga watan Maris.

    "Wannan hanin zai hada da Jihar Ogun saboda kusancin da take da shi da Jihar Legas da kuma yawan zirga-zirga tsakanin jihohin. An sanar da gwamnonin Legas da Ogun da kuma ministan Abuja.

    "Lallai ne kowa ya kasance a cikin gidansa a wadannan yankunan. A katse tafiye-tafiye tsakanin jihohi. Dukkanin harkokin kasuwanci za a rufe su a tsawon wannan lokaci.

    "Za mu yi amfani da wannan dama wajen gano tare da killace dukkan wadanda suka yi mu'amala da mutanen da aka riga aka gano sun kamu da cutar. Za mu tabbatar da cewa an kula da wadanda suka kamu a asibiti yayin da za mu takaita yaduwarta zuwa sauran jihohi.

    "Wannan dokar ba ta shafi asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya ba da kuma wuraren da ake samar da rarraba magunguna.

    Haka nan ba ta shafi wuraren kasuwanci ba kamar su:a. Wajen sarrafa abinci da kamfanonin da ake sari;b. Wuraren da ake rarraba man fetur da masu sayarwa,c. Kamfanonin rarrabawa da samar da wutar lantarki;d. Kazalika ban da kamfanonin tsaro masu zaman kansuDuk da cewa dokar ba ta shafi wadannan wurare ba, to za a takaita ziyarrtarsu kuma za a sa ido.

    "A yaki da coronavirus, kowanne irin mataki muka dauka ba zai yi girma ba kuma ba zai yi kadan ba. Maganar kawai ita ce ta daukar matakin da ya dace a lokacin da ya dace daga kwararrun ma'aikata."

    "Don Haka, a matsayinmu na gwamnati, za mu ci gaba da dogara da shawarwarin masana da kwararru a ma’aikatar Lafiya da hukumar da ke kula da yaduwar cutuka, NCDC, da sauran hukumomi a wannan lokaci na tsaka mai wuya.

    "Ina kira ga duka ‘yan kasar nan da su bi dokokin da ake fitarwa lokaci zuwa lokaci.

    "Kamar yadda aka sani, Legas da Abuja ne garuruwan da ke da mafi yawan mutnen da aka samu dauke da cutar a Najeriya. Don haka mun mayar da hankali wajen gaggauta dakatar da yaduwar cutar, kuma mu taimaka wa sauran jihohin da yankuna iya karfinmu.

    "Kawo yanzu, a Legas da Abuja, mun dauki daruruwan ma’aikata na wucin gadi don kara karfin cibiyoyinmu na amsa waya da kuma tallafa wa kokarinmu na gano mutanen da ake tunanin suna dauke da cutar da kuma wadanda aka yi wa gwaji.

    "A yayin da muka shirya domin tursasa wa mutane bin wadannan dokoki, ya kamata mu yi la’akari cewa wannan wata gudunmawar kashin-kai ce da za mu bayar wajen yaki da COVID-19. Kasashe da dama sun dauki matakan da suka fi namu tsauri wadanda suka ga amfaninsu a kokarinsu na hana yaduwar wannan cuta..

    "Daga yanzu zuwa makonnin da ke tafe za mu bayar da kayan agaji ga mutanen da ke zaune a yankunan karkara da ke kusa da Legas da Abuja, wadanda za su shiga mawuyacin hali sanadiyar matakan da muka dauka.

  4. Jawabin Shugaba Buhari ga 'yan Najeriya kan coronavirus

    Jawabin Shugaba Buhari ga 'yan Najeriya kan coronavirus

  5. Kamuwa da coronavirus ba mutuwa ba ce – Atiku

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Twitter/Atiku ABubakar

    "[Coronavirus] ba mutuwa ba ce," sakon Alhaji Atiku Abubakar kenan ga Gwamnan Bauchi Bala Mohammed da Nasir El-Rufai na Kaduna da Muhammad Babandede shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya (Immigration).

    Dukkanin mutanen da tsohon mataimakin shugaban kasar ya lissafo gwaji ya nuna cewa suna dauke da coronavirus, kuma Atiku ya yaba masu saboda "bayyana [kamuwa da cutar]" da suka yi.

    "Ina so na jinjina masu bisa bayyana [harbuwa da cutar da suka yi]. Za mu iya kawo karshen annobar nan ta hanyar yin bayani da ilimantar da mutane da killace kai da kuma yin gwaji. Ba mutuwa ba ce. Duka za mu warke," Atiku ya bayyana a shafinsa na Twitter.

    A makon da ya gabata ne dan gidan Atiku Abubakar mai suna Mohammed ya kamu da cutar bayan ya koma Najeriya daga kasar waje.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Labarai da dumi-dumi, Italiya na ci gaba da fuskantar bala'in coronavirus

    Italiya ta bayar da sanarwar mutum 756 da suka mutu a cikin awa 24 - adadin wadanda suka mutu a fadin kasar ya zama 10,779.

  7. Labarai da dumi-dumi, Za a gina sabbin dakunan gwajin coronavirus a jihohi 7 na Najeriya

    Hukumar da ke yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta bayyana cewa tana kokari wajen samar da sabbin dakunan gwaje-gwaje bakwai a fadin kasar domin taimakawa wajen gwajin cutar coronavirus.

    Hukumar ta ce tana fatan yin hakan a cikin mako uku masu zuwa.

    Ta bayyana cewa garuruwan da za a gina wadannan dakunan sun hada da Abakaliki da Maiduguri da Kano da Sakoto da Fatakwal da Jos da kuma Kaduna.

    A halin yanzu dakunan gwaje-gwajen shida ne a fadin Najeriya wadanda ke jihohi uku.

    Idan hukumar ta yi nasarar gina sababbi guda bakwai, wuraren gwajin za su zama 13 kenan a Najeriya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Mutum 97 ne suka kamu da coronavirus a Najeriya. Ga jihohinsu:

    • Lagos - 59
    • Abuja - 16
    • Ogun - 3
    • Enugu - 2
    • Ekiti - 1
    • Oyo - 7
    • Edo - 2
    • Bauchi - 2
    • Osun -2
    • Rivers -1
    • Benue - 1
    • Kaduna - 1
  8. Amurkawa 100,000 zuwa 200,000 ka iya mutuwa saboda coronavirus

    Babban jami'in cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta Amurka ya gargadi gwamnatin kasar cewa annobar cutar coronavirus ka iya salwantar da ran Amurkawa 100,000 zuwa 200,000.

    Dr Anthony Fauci, wanda mamba ne a kwamitin musamman kan coronavirus na Shugaba Donald Trump, ya bayyana wa CNN cewa miliyoyin mutane za su iya harbuwa da cutar.

    Babban darakta a cibiyar National Institute of Allergy and Infectious Diseases, Dr Fauci ya kara da cewa, sai dai "ba na son na fiya fadar hakan...Saboda abu ne da ke sauyawa da za a iya yin kuskure kuma a batar da mutane".

  9. 'Babu mai fita daga Najeriya kan harkar lafiya sai da izinin asibitin koyarwa'

    Jirgin Turkish Airlines

    Asalin hoton, @hadisirika

    Gwamnatin Najeriya ta ce duk wani jrigin kasar waje na difilomasiyya ba zai shiga kasar ba sai da sanin ma'aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya, a cewar Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.

    Har wa yau, gwamnati ta shardanta cewa duk wanda zai fita daga Najeriya da sunan neman lafiya sai wani asibitin koyarwa a Najeriya ya sahale masa.

    Kazalika wajibi ne ma'aikatan cikin jirgi su kasance a cikin jirgin a kowane lokaci - kada su leko waje idan sun sauka a Najeriya.

    Zuwa karfe 10:40 na daren ranar Asabar, mutum 97 ne suka kamu da coronavirus a Najeriya, in ji hukumar NCDC, inda ta ce mutum daya ya mutu, kuma an sallami uku.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Jerin jihohin da cutar ta bulla:

    Lagos- 59

    Abuja- 16

    Ogun- 3

    Enugu- 2

    Ekiti- 1

    Oyo- 7

    Edo- 2

    Bauchi- 2

    Osun-2

    Rivers-1

    Benue- 1

    Kaduna- 1

  10. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: An kama Fasto a Abuja saboda bude coci ranar Lahadi

    .

    Asalin hoton, FCTA

    Runduna ta musamman da ke tabbatar da bin dokoki karkashin jagorancin hukumar gudanarwa ta birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta yi awon gaba da wani fasto sakamakon bijirewa doka.

    Tun a makon da ya gabata ne dai aka saka dokar hana sallar Juma'a da kuma taron addu'o'i na ranar Lahadi a Abuja da wasu jihohin Najeriya a yunkurin dakile annobar Coronavirus.

    Fasto U Uden, shi ne wanda hukumar ta kama a ranar Lahadi, bayan ya tara jama'a a cocinsa da ke Unguwar Apo a Abuja.

    Ko a ranar Asabar sai da aka kama limamai biyu a jihar Kaduna sakamakon sallar Juma'a da suka gudanar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Adadin wadanda suka mutu a Netherlands ya kai 771

    Adadin wadanda suka mutu a kasar Netherlands ya karu da mutum 132 a cikin awa 24 - jumullar adadin ya zama 771.

    Jumullar wadanda suka kamu da cutar a kasar, mai adadin al'umma kusan miliyan 17, ya kai 10,866 bayan an samu karin mutum 1,104 da suka kamu a cikin awa 24.

  12. Sabbin bayanai daga Gabas ta Tsakiya

    Iran ta bayar da sanarawar karin mutum 123 da suka mutu, abin da ya kai jumullar adadin zuwa 2,640. Wadanda suka kamu da cutar kuma sun kai 38,309, a cewar hukumomi.

    A gefe guda kuma, Saudiyya ta rufe birnin Jeddah sannan ta saka dokar hana fita a birnin da za ta fara aiki daga karfe 3:00 agogon kasar, ba karfe 7:00 ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya rawaito.

    Saudiyyar ta dauki irin wannan mataki a babban birnin kasar, Riyadh da Makka da Madina - kasar ce ke da mafi yawan wadanda suka kamu da coronavirus a yankin Gulf bayan Iran.

  13. Labarai da dumi-dumi, Karin mutum 209 sun mutu a Birtaniya

    An samu karin mutum 209 da suka mutu a Birtaniya sakamakon annobar coronavirus.

    Jumullar wadanda suka mutu daga cutar yanzu sun kai 1,228.

  14. Labarai da dumi-dumi, Shugaba Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya

    .

    Asalin hoton, FACEBOOK/BUHARI SALLAU

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya a daren yau Lahadi.

    Sakataren watsa labarai na shugaban Femi Adesina ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook inda ya bayyana cewa shugaban zai yi jawabin ne ta gidajen talabijin da rediyo na kasar wato NTA da kuma FRCN, kuma ana sa ran sauran gidajen talabijin da rediyo za su yada jawabin shugaban kai-tsaye.

    Shugaban dai zai yi jawabin ne da misalin karfe 7:00 na dare agogon Najeriya.

    Duk da cewa Mista Femi Adesina bai bayyana mau'du'in da shugaban kasar zai tattauna a kai ba, amma ana ganin cewa shugaban zai fi mayar da hankali ne kan batun cutar coronavirus wadda ta zama annoba a fadin duniya.

  15. 'Sanusi da matansa ba su da coronavirus'

    .

    Asalin hoton, Majeeda Studio

    Tun bayan da gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya kamu da cutar coronavirus, jama'a da dama musamman a shafukan sada zumunta suka fito suna rade-radin wata kila Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na dauke da cutar sakamakon ziyarar da gwamnan Kadunan ya kai masa a garin Awe na jihar Nasarawa.

    A ranar Lahadi ne dai Ashraf Lamido Sanusi wanda da ne ga tsohon sarkin ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa mahaifinsa da kuma iyayensa mata ba su dauke da cutar ta Covid-19.

    Ashraf ya shaida cewa tun a ranar 25 ga watan Maris aka dauki samfarin gwajin iyayen nasa domin yin gwaji kuma ko da sakamako ya fito, babu alamun wannan cuta a tattare da su.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Coronavirus: Mutum 257 cutar ta kashe a Switzerland

    Yawan mutanen da suka mutu a kasar Switzerland sun kai 257 kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kasar sun kai 14,336.

    Hakan ya sa kasar ta Switzerland ta zama cikin manyan kasashen da cutar ta fi yi wa illa a nahiyar Turai bayan Italy da Spain da Jamus da Faransa da kuma Birtaniya.

  17. Ba ni da coronavirus – Gwamnan Neja

    .

    Asalin hoton, @abusbello

    Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa ya yi gwajin cutar coronavirus kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa bai dauke da cutar.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twiiter inda ya yi godiya ga al'umma bisa addu'o'insu .

    Ya kuma kara bada hakuri ga jama'ar jihar dangane da halin da suke ciki sakamakon dokar hana fita da aka saka a jihar inda ya ce an yi hakan ne domin kare lafiyar al'umma baki daya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Korea ta Kudu ta fito da sabbin tsare-tsare kan coronavirus

    A wani sabon tsari da ta fitar, Korea ta Kudu ta bayyana cewa duk wasu matafiya da suka isa kasar sai an killace su na kwanaki 14.

    Ta bayyana cewa idan baki da ke shiga kasar suka saba wannan doka za a fitar da su karfi da yaji, 'yan kasar kuma da suka dawo suka saba doka kuma za a ci su tara.

    Wannan sabuwar dokar dai za ta fara aiki ne 1 ga watan Afrilu.

    Dokar kuma za ta tilasta wa duk wani wanda ya shiga kasar dole sai ya sauke wata manhaja a wayarsa da za ta taimaka wajen sanya wa mutum ido domin ganin ko yana bin ka'idojin killacewa.

    Kusan rabin wadanda aka samu labarin sun kamu da cutar a 'yan kwanakin nan a kasar baki ne da suka shigo daga wata kasa.

  19. Covid-19 ta hallaka mutum fiye da 2,000 a Amurka

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar annobar coronavirus a Amurka ya zarce 2,000, hakan na nufin adadin ya ninka cikin kwana biyu.

    Ya zuwa yanzu, mutum dubu 120 ne suka kamu da cutar covid-19 a kasar.

    Sai dai Shugaba Trump ya janye kudirin sanya dokar hana fita a New York da New Jersey - wuraren da cutar ta fi kamari.

    Gwamnonin jihohin biyu sun bayyana takaicinsu game da ra'ayin na Trump inda gwamna Andrew Cuomo na New York ya bayyana cewa matakin zai iya jefa fargaba a zukatan jama'a tare da kara tabarbara kasuwannin hada-hadar kudi.

  20. Covid-19: Za a tsayar da albashin 'yan wasan Juventus na watanni 4

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus da kuma kocin kungiyar Maurizio Sarri, sun amince da a tsayar da albashinsu na watanni hudu domin ragewa kungiyar asara da kusan Euro miliyan 90 sakamakon cutar coronavirus da ta zama annoba.

    An dakatar da duk wata harka ta wasanni a Italy sai zuwa watakila 3 ga watan Afrilu.

    Manyan 'yan wasan kungiyar irin su dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo da kuma dan wasan tsakiya na Wales Aaron Ramsey ba za su karbi cikakken albashinsu ba a watan Maris da Afrilu da Mayu da kuma watan Yuni.