Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya
Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.
Rahoto kai-tsaye
Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau
Za a fara kidaya kuri'u a Benue
Ana shirye-shiryen fara kidaya kuri'u a rumfar zaben gidan gwamnatin jihar Benue.
Atiku Abubakar ya kada kuri'a
Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya kada kuri'arsa a garin Yola na jihar Adamawa ranar Asabar.
An fara kidaya kuri'u a Kano
An fara kidaya kuri'u a wata mazabar da ke unguwar Shagari Quarters a jihar Kano, kamar yadda wakilinmu Mansur Abubakar ya tabbatar mana.
Abba Kabir Yusuf ya kada kuri'arsa
Dan takarar jam'iyyar PDP a Kano Abba Kabir Yusuf ya kada kuri'arsa a Kano.
Ba kasuwa ga masu talla a rumfunan zabe a Abuja
Zaben shugaban kasa da aka gudanar a Najeriya na 23 na shugaban kasa ya sha bamban da na gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi da ake yi a halin yanzu.
A wannan karon an samu karancin fitowar jama'a a birnin tarayyar Najeriya Abuja inda ake zaben kananan hukumomi.
Masu sana'o'i daban-daban na kokawa kan yadda suka fito da kayan talla amma ba kasuwa.
Rumfar zabe a fadar shugaban kasa
An samu karancin fitowar mutane a rumfunan zabe a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Wani mai bukata ta musamman a rumfar zabe
Wani mai bukata ta musamman kenan mai suna Atsen Azi a rumfar zaben Zarazo da ke karamar Hukumar Jos ta Gabas.
Yadda ake cinikin gurasa a rumfar zabe
Bidiyon yadda mai sayar da gurasa ke sana'arsa a wata rumfar zabe a Kano.
Tambuwal ya kada kuri'arsa
Mata na sassaka a Gezawa a jihar Kano
Masallatai na kira a fito zabe a Jos
Masallatai a Dogon karfe da ke Jos sun yi amfani da lasifikarsu domin kiran mutane a fito a kada kuri'a.
Sun yi hakan ne sakamakon karancin fitowar mutanen da aka samu a ranar zabe.
Rahotanni dai sun bayyana cewa bayan kiran da masallatan suka yi, jama'a da dama sun yiu tururuwa domin zuwa rumfunan zabe su kada kuri'arsu.
Yadda wasu ke hidimarsu a ranar zabe a Legas
Saraki ya kada kuri'arsa
Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya kada kuri'arsa a rumfar zabe mai lamba 005/006 da ke Agbaji a karamar hukumar Ilorin ta yamma a jihar.
Bola Tinubu ya kada kuri'a
Tsohon gwamnan Legas kuma jigo a jam'iyyar APC Bola Tinubu ya kada kuri'a.
Wamakko ya kada kuri'arsa
Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma jigo a jam'iyyar APC Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kenan a lokacin da ya ke kada kuri'arsa.
Yadda Sanwo-Olu ya kada kuri'arsa
Dan takarar gwamna a jihar Legas na jam'iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu a lokacin da yake kada kuri'arsa.
Jonathan da Patience sun kada kuri'unsu
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da matarsa Patience sun kada kuri'a a mazabar Otuoke da ke jihar Bayelsa.
Bidiyon yadda EFCC ta kama makudan kudade a jihar Benue
Bidiyon yadda Buhari ya kada kuri'arsa
Shugaban Najeriya kenan Muhammadu Buhari a yayin da yake kada kur'arsa a mazabarsa da ke Kofar Baru a Daura