An kama wata mota makare da kudi a Sokoto
An kama wata mota makare da kudi a jihar Sokoto.
Hukumar yaki da cin hanci da zagon kasa tare da jami'an tsaro ne suka kama mota kirar Jeep makare da kudi da ake zargin za a yi amfani da su ne wajen sayen kuri'u a jihar Sokoto.
An kama motar mai lamba ABC 924 LU a kan titin Garba Duba da ke Sokoto a daren Juma'a da karfe 10:30 inda aka kai motar hedikwatar 'yan sanda a jihar Sokoto.
Daga nan ne aka fito da buhunhunan kudi domin yin bincike. An yi ta kokarin jin ta bakin kakakin 'yan nda kan lamarin, yayin da jami'an tsaron suka hana daukar hotunan kudin.