Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. Jihar Kebbi

    Yadda ake raba kayayakin zabe a jihar Kebbi ga kananan hukumomi.

  2. Jihar Zamfara

    Wakiliyar hukumar zabe ta Najeriya a jihar Zamfara uwargida Asmau Sani Maikudi tana gabatar da jawabi ga wakilan jam'iyun jihar kan zaben gwamna da na 'yan majalissun dokoki da kuma shirin raba kayayyakin zabe ga kananan hukumomin jihar.

  3. Jihar Benue

    Yadda wakilan hukumar zabe ke hada lissafi a Makurdi kan yadda za a raba kayan zabe da motocin da za a yi aikin da su.

  4. An fara raba kayan zabe a wasu jihohin

    Muhimman kayan zabe a babban bankin Najeriya wato CBN na Jihar Bauchi.

    Inda za a raba kayayyakin zuwa kananan hukumomi 20 dake jihar.

  5. Ranar Asabar 9 ga watan Maris za a gudanar da zabukan

    Kimanin jihohi 29 ne za su gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalissu, bayan nan a fara tattara kuri'un da aka yi zabe.

    Daga nan ne za a fara kidayar kuri'un sannan asa ran bayyana sakamako.

  6. Barkanmu da saduwa a shirin yadda za a gudanar da zabukan gwamnonin jihohin Najeriya da na 'yan majalissar dokoki da za a yi a ranar Asabar.

    Za mu dunga kawo muku bayanai kai tsaye kan yadda za a yi zabukan a fadin Najeriya.

    Za ku iya bayar da gudunmawarku a BBCHausa Facebook ko a Tuwita ta twitter.com/bbchausa ko kuma ta Instagram ta Instagram.com/bbchausa.

    Mandu'inmu shi ne #BBCNigeria2019 #NigeriaDecide2019