Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. APC ta lashe sakamakon zaben kujerun majalisa 21 a Kogi

    Hukumar INEC ta bayyana sakamakon kujerun 'yan majalisa 21 cikin 25 na jihar Kogi inda jam'iyyar APC ta lashe kujeru 21 sai kuma kananan hukumomi uku ba a kammala ba.

    Kananan hukumomin da ba a kammala ba sun hada da Lokoja 1 da Igalamela-Odolu da Omala. A yanzu haka ana tattara sakamakon karamar hukumar Mopamuro wace ita ce ta rage.

  2. Badaru ya lashe zaben Jigawa

    Hukumar INEC ta bayyana Mohammadu Badaru Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Jigawa

  3. Ana takaddama kan sakamako a Bauchi

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    Ana ci gaba da takaddama kan sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

    Baturiyar zabe ta ce an samu tashin hankali inda aka yi barazana ga rayuwar jami’an zabe a cibiyar tattara sakamako ta Tafawa Balewa inda wasu ’bata-gari’ suka tilasta mata bayyana wani sakamako a wurin. An kuma samu ta’adin wasu takardun sakamako don haka suka yi amfani da alkaluman da suke da shi a kwamfyuta.

    Babban jami’in hukumar zabe mai bayyana sakamako na jihar, Farfesa Kyari Muhammad ya ce ba za a karbi sakamakon Tafawa Balewa ba kuma akwai yiwuwar a sake zabe a yankin. Takaddamar ta taso ne bayan da wakilin APC ya ce bai gamsu da sakamakon ba saboda zargin an sauya sakamakon.

    To amma wani wakilin PDP ya ce suna so a karbi sakamakon kuma a bayyana.

    Kawo yanzu ana jiran hukuncin babban baturen bayyana sakamako na jiha kan ko tabbas za a sake zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa ko kuma ba za a sake ba.

  4. Labarai da dumi-dumi, Dan majalisa ya mutu 'yan sa'o'i bayan lashe zabe

    Dan majalisar dokoki na jam'iyyar APC mai wakiltar mazabar Pengana da ke karamar hukumar Bassa ta jihar Filato Ezekiel Bauda Afom ya mutu 'yan sa'o'i bayan ya lashe zabe.

  5. Tambuwal ya ci Tambuwal

    Dan takarar jam'iyyar PDP Aminu Waziri Tambuwal ya lashe maihafarsa karamar hukumar Tambuwal inda ya samu kuri'u 42,830 sai kuma Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC ya samu 29,081.

  6. Bayero Nafada ya fadi a Gombe

    Dan takarar jam'iyyar APC a Gombe Inuwa Yahaya ya lashe zaben jihar da kuriu' 364,179 inda Usman Bayero Nafada na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 222,868.

  7. PDP ta lashe karamar hukumar Gudu a Sokoto

    Jami'iyyar PDP a jihar Sokoto ta lashe zaben gwamna a karamar hukumar Gudu a jihar Sokoto inda ta samu kuri'u 14,901 sai kuma jam'iyyar APC ta samu 12,022.

  8. Waye a gaba?

  9. Ra'ayoyi daga shafin Twitter

  10. An fara tattara sakamako a jihar Nasarawa

    A Jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya, Ofishin hukumar zabe ta kasa da ke jihar ya fara tattara sakamakon zaben gwamna da `yan majalisar dokoki daga wasu kananan hukumomi.

    Kananan hukumomi 13 ne a jihar, kuma a kalla mutum 27 ne ke takarar mukamin gwamna.

  11. APC ta lashe zaben gwamnan Kwara

    Dan takarar jam'iyar APC, Abdulrahman Abdulrazaq ya lashe zaben gwamnan jihar Kwara, bayan da ya samu kuri'u 331,546. Shi kuwa Abdulrazaq Atunwa na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 115,310.

  12. An kai hari karamar hukumar Warawa jihar Kano

    Yayin da ake aikin tattara sakamakon zabe a Kano, ana samun rahotannin tunzuri a wasu sassan jihar.

    Tun a safiyar yau dai an ba da rahoton cewa wasu mutane sanye da kayan sojoji sun bude wuta a kan mutanen da suka taru a cibiyar tattara sakamakon zabe ta karamar hukumar Warawa.

  13. El Rufai ya lashe Giwa

    Dan takarar APC Nasir El Rufai ya lashe karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna inda ya samu kuri'u 51,455 sai kuma Isa Ashiru na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 19,834.

  14. APC ta lashe Rano a Kano

    Jam'iyyar APC ta lashe karamar hukumar Rano a Kano da kuri'u 16,694 sai kuma jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 14, 892.

  15. PDP ta lashe Alkaleri a Bauchi

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    Jam'iyyar PDP a jihar Bauchi ta lashe karamar hukumar Alkaleri da ke jihar da kuri'u 34,625 inda jam'iyyar APC ta samu kuri'u 27,238.

  16. Yadda ake tattara sakamakon zabe a Kano

  17. PDP ta lashe Misau a Bauchi

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    Dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Bauchi ya lashe karamar hukumar Missau inda ya samu kuri'u 19,928 sai kuma dan takarar APC kuma gwamnan jihar Muhammed Abubakar ya samu kuri'u 16,282

  18. Yadda ma'aikatan BBC suke bakin aiki

  19. Ba a fara sanar da sakamakon Fatakwal ba

    Hukumar zabe INEC reshen Rivers a babban birnin Fatakwal ba ta fara sanar da sakamakon zaben gwamna da na majalisa ba.

    Jami'an tsaro suna kula da shiga da fice na mutane.

  20. El Rufa'i ya lashe zaben karamar hukumar Kudan

    El Rufa'i ya lashe karamar hukumar Dan takarar jam'iyar APC, Nasiru El Rufa'i ya lashe zabenn gwamna a karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, bayan da ya samu kuri'u 28,624, yayin da na jam'iyyar PDP, Isa Ashiru ya samu 22,022.