Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. Yadda wata tsohuwa ke jefa kuri'arta a Bayelsa

    Wata tsohuwa kenan da aka goyo a baya don ta kada kuri'a a wata rumfa a garin Yenagoa da ke jihar Bayelsa.

  2. Karancin kayan zabe

    Bidiyon yadda wasu a mazabar Garko da ke jihar Gombe suka koka kan yadda suka samu karancin kayan zabe a mazabarsu.

  3. Bidiyon yadda aka mari wakiliyar BBC a Legas

  4. Zan amince da sakamako idan na fadi- Gwamnan Bauchi

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar kuma wanda shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar ya ce zai amince da sakamakon zabe idan ya ci ko ya fadi.

  5. Ganduje ya kada kuri'arsa

    Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kuma dan takarar jam'iyyar APC a jihar a yayin da yake kokarin jefa kuri'arsa,

  6. EFCC ta yi ram da mai sayan kuri'a

    A kokarin da hukumar EFCC take yi na dakile sayan kuri'a, hukumar ta yi nasarar damke wani mai suna Abdulkareem Abdulsalam a ya yin da yake raba kudi a ranar zabe a jihar Kwara

  7. Rikici a wata rumfar zabe a Kano

  8. Labarai da dumi-dumi, Fitaccen dan siyasa ya wanka wa wakiliyar BBC mari

    Wani fitaccen dan siyasa a Legas Segun Adewale ya wanke wakiliyar BBC da mari.

    Wakiliyar ta BBC mai suna Ajoke da ke sashen turancin pidgin ta bayyana cewa dan siyasar ya kai mata hari ne bayan ta ganshi yana raba Naira dubu 1 ga masu zabe.

    Bayan ya mare ta 'yan barandansa sun karbe mata waya a wannan lokaci, sai daga baya 'yan sanda suka kawo mata dauki.

    Adewale dan siyasa ne a Legas da a baya ya yi kokarin zama gwamna a jihar Ekiti.

    Kawo yanzu ba a ji ta bakin dan siyasar ba

  9. An samu karancin takardun kada kuri'a

    Gidim Bogo akwati mai lamba 022, mazabar Garko, Akko, har yanzu ba a fara kada kuri'a sakamakon karancin kuri'u.

    Mutum 705 za su yi zabe a akwatin amma takardar kuri'u 500 ne aka tanada.

    Mallam Muhammadu Aji Ladan, yace sun dakata da zaben, domin katin zaben basu isa ba. Sama da mutum 20 ne suka fara zabe daga baya aka dakatar gudanar da aikin.

  10. An fara zabe a wasu mazabun a Najeriya

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    Ya'u Jibrin na sauraren labarai kan yadda ake gudanar da zabe a lokacin da yake kan layi zai kada kuri'a.

  11. Mata ba su fita zaben gwamna sosai ba a wasu sassan Gombe

  12. El Rufa'i zai yi zabe a mazabarsa

    El Rufa'i na kan layi zai yi zabe a mazabarsa a unguwar Sarki a jihar Kaduna.

  13. Yadda ake kada kuri'a a Benue

  14. An fara zabe a wasu rumfuna a jihar Bauchi

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    An soma kada kuri’a a rumfar zabe ta Makama Development Area dake birnin Bauchi

  15. Ra'ayoyin wasu mazauna Kano kan zaben gwamna

  16. Birnin Lafiya a jihar Nasarawa

    Rashin zuwan wakilan jam'iyu ya sa ba a fara tantance masu zabe a wata makarantar Firamari a birnin Lafiya a jihar Nasarawa.

  17. Birnin Kebbi mazabar Galadima

    Wasu masu kada kuri'a na jiran a fara zabe a mazabar Galadima a Birnin Kebbi.

  18. Jihar Benue wasu na sauraren labarai kan yin zabe

    Usman Adamu da wasu mutane na sauraren sashen Hausa na BBC a mazabar Ndabagi a Katungu a jihar, Makurdi.

  19. Yadda mutane ke duba sunayensu a mazabunsu

  20. Ba zaben gwamna a jihar Kogi sai na majalisar dokoki

    Daya daga cikin jihohin da ba za a gudanar da zaben gwamna cikinta a yau ba, ita ce Kogi wadda ke yankin tsakiyar arewacin Nijeriya.

    Ko da yake, jama'ar jihar ba za su yi zaben gwamna ba, amma za su fita rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dokokin jihar.

    Bayanai dai sun ce ana zabar 'yan majalisar jiha guda 25 a cikin kananan hukumomi guda 21, inda wasu kananan hukumomin kamar Lokoja ke fitar da 'yan majalisa guda biyu.