EFCC na duba kayayyakin zabe
Jami'an hukumar EFCC a Najeriya kenan ke duba kayayyakin zabe a filin jirgin sama dake Maiduguri a jihar Borno a yunkurin da suke yi na yaki da sayan kuri'a a zaben da za a gudanar a ranar Asabar.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.
Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau
Jami'an hukumar EFCC a Najeriya kenan ke duba kayayyakin zabe a filin jirgin sama dake Maiduguri a jihar Borno a yunkurin da suke yi na yaki da sayan kuri'a a zaben da za a gudanar a ranar Asabar.
Kayayyakin zabe suna ta isa a mazabu dake fadin Najeriya. Yanzu haka wadannan wasu daga cikin kayayyakin zabe ne da ke mazabar Jos Jarawa dake jihar Filato.
Hukumar INEC ce ta wallafa a shafinta na Twitter domin tuni a kan cewa duk wanda aka kama ya saci kayan zabe zai fuskanci shari'a inda ake sa ran zai sha dauri na shekaru biyu.
Rundanar ’yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta musanta zargin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi cewa jami’anta na musguna wa ’yan adawa a jihar gabanin zaben gwamna da na ’yan majalisar jiha. Kwamishinan ’yansanda na jihar, Ali Janga, ya shaida wa wani taron manema labarai a hedikwatar rundunar dake Bauchi cewa zargin ba gaskiya ba ne. Tun farko dan takarar gwamna na jam’iyyar ta PDP, Sanata Bala Muhammad Kaura ya shaida wa BBC cewa jami’an tsaro da hadin bakin gwamnatin APC a jihar, sun kama magoya bayan ’yan adawa fiye da 300 da nufin gallaza masu. To amma kwamishinan ’yan sandan ya ce mutanen da yan sanda suka kama ba su kai 300 ba. ’Mun kama mutane fiye da 100 ne’ inji shi. Ya kara da cewa wadanda aka kama ba magoya bayan PDP ba ne kadai, sun hada da na wasu jam’iyyun ciki har da APC da kuma ’yan Sara-suka. Ana zarginsu ne da laifuka da suka shafi keta doka da yunkurin tayar da zaune tsaye.
Yadda wasu mazauna jihar Benue ke fatan yin zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki lafiya da za a gudanar ranar Asabar 9 ga watan Maris.
Yadda aka yi wa 'yan horon kasa bita kan zaben gwamna da za a gudanar a jihar Ogun da na 'yan majalissar dokoki.
An kuma ba su bitar kan yadda ya kamata su gudanar da aikinsu, an kuma bukaci da su kaucewa duk wasu abubuwan da za su jawo hayaniya.
Wakilan BBC da ke sassa daban-daban a Najeriya sun shaida mana cewa sun ga yadda 'yan siyasa ke ta faman raba kayayyakin masarufi ga masu kada kuri'a gabanin zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki da za a yi gobe Asabar.
A jihar Kwara an ga yadda ake raba wa mutane kananzir da taliya da sikari.
A Legas kuma an fi raba shinkafa ne mai dauke da hoton 'yan takara.
Yadda ake tantance kayayyakin zabe kenan a ofishin hukumar zabe da ke Makurdin jihar Benue gabannin zaben gwamna a ranar Asabar
Ofishin hukumar zabe na karamar hukumar Ibesikpo Asutan da ke jihar Akwa Ibom ya kone, kuma kawo yanzu ba a san musabbabin gobarar ba.
Jami'in zabe na jihar Mike Igini ya ziyarci ofishin domin ganin barnar da gobarar ta yi.
Ana ta cin karo da kalubale a jihar Akwa Ibom musamman a zaben gwamna da Udom Emmanuel na PDP ke son yin tazarce.
Dangane da zaben da za a gudanar a fadin jihohin Najeria na gwamnoni da kuma 'yan majalissar dokoki da muke kawo muku sharhi da bayanai kai tsaye, sauran sashen BBC na Yarukan Najeria suna gudanar da shiri na kai tsaye a shafukansu.
za ku iya bibiya ta:
Igbo https://bbc.com.im/igbo/live/afirika-47493450%3C/a%3E%3C/p%3E%3C/div%3E%3Cdiv dir="ltr" class="css-1k9op6x e17x9cvu0">
Pidgin https://bbc.com.im/pidgin/live/tori-47468810%3C/a%3E%3C/p%3E%3C/div%3E%3C/div%3E%3C/article%3E%3C/li%3E%3Cli class="css-xxlek1">
Dogon layi a sakatariyar APC a Makurdi, jihar Benue inda mutane ke karbar sukari da taliya da sauran kayayyakin amfanin gida.
Tun a ranar Alhamis aka fara raba kayayyakin.
Hukumar zabe ta jihar Cross Rivers ta ce ta kammala shirin fara zaben gwamna da na 'yan majalissar dokoki a jihar da za a gudanar ranar Asabar 9 ga watan Maris.
'Yan takara 25 ke neman kujerar gwamnan, yayin da 'yan takara 265 ke neman kujerun majalissar dokokin jihar.