Masu kada kuri'a sun yi sammako a Ekiti
A can birnin Ekiti da ke jihar Ekiti ta kudu maso yammacin Najeirya, masu kada kuri'a sun yi sammako kamar yadda kuke gani a wadannan hotuna da aka dauk a rumfar zabe mai lamba 10 da 7 a Ekiti.


Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.
Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu
A can birnin Ekiti da ke jihar Ekiti ta kudu maso yammacin Najeirya, masu kada kuri'a sun yi sammako kamar yadda kuke gani a wadannan hotuna da aka dauk a rumfar zabe mai lamba 10 da 7 a Ekiti.


Masu kada kuri'a na ci gaba da tudada rumfunan zabe a sassa daban-daban na Najeriya. Wadannan masu kada kuri'ar a rumfar zabe ta Shagari Clinic da ke Bole /Yolde Pate a Yola South ta jihar Adamawa sun fita tun da karfe shida na safe. Suna jira a soma tantance su.



Wakilinmu da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Abdou Halilou, ya aiko mana rahoton da ke cewa ana can ana jin karar harbe-harbe a birnin. Har yanzu babu cikakken bayani kan irin barnar da harbe-harben suka yi, ko kuma wadanda suke yin su. Amma da ma birnin ya sha fama da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.
Masu zabe sun yi sammakon zuwa rumfunan zabe a sassa daban-daban na Najeriya, inda wasu suka fita tun da asubahi kamar yadda wadannan masu kada kuri'a a wata rumfar zabe ta Gajawa 1 da 2 a birnin Jalingo na jihar Taraba.

Asalin hoton, Sani Suleiman
'Yan takara sama da 6300 neman kujerun majalisar dokoki ta tarayyar Najeriya.
Za a zabi 'yan majalisar dattawa 109 da kuma 'yan majalisar wakilai 360.
Ana ganin zaben 2019, shi ne mafi girma a tarihin Afrika inda ake sa ran mutum miliyan 84 za su kada kuri'a a zaben na Najeriya kasa mafi girma a nahiyar Afirka.

'Yan takara sama da 70 ne ke neman darewa kujerar shugaban kasa a zaben, amma Shugaba Muhammadu Buhari na APC mai shekara 76, da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP, mai shekara 72 ne suka fi jan hankali a zaben.
Shugaba Buhari ya ce ya aza tubalin ci gaban kasar, amma Atiku Abubakar ya ce an samu koma-baya kan sha'anin tsaro da tattalin arziki da makamantasu a gwamnatin Buhari.

Asalin hoton, AFP
Barkanmu da warhaka, Nasidi Adamu Yahaya ne zai kawo muku bayanai kai tsaye a wannan shafin kan yadda ake gudanar da zaben Najeriya. Latsa nan domin tafka muhawara a shafinmu na Facebook.
Ku kasance tare da mu gobe da safe domin za mu ci gaba da kawo maku shirye-shirye kai tsaye a kan yadda zaben Najeriya zai gudana. Sunana Mustapha Musa Kaita.
Mammam Ngurore kenan dake kauyen Ngurore a kudancin jihar Adamawa inda yake bayyanawa wakilinmu Mukhtar Adamu Bawa shirinsa na zuwa rumfar zabe domin kada kuri'a,


A ci gaban da ake yi na shirye-shiryen zabe, rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta kama wasu da ake zargi da tayar da rikici gabannin zabe. A cikin wadanda aka kama harda dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji dake Kano.
Ci gaba da rarraba ma'aikatan zabe kenan daga karamar hukumar Demsa ta jihar Adamawa zuwa mazabu. Tuni aka fara rarraba kayayyakin zabe zuwa mazabu a jihar.



A nan ana raba kayan ne a matakin mazabu a cikin karamar hukumar Daura. Ma’aikatan zabe ne ke karbar kayayyaki domin zuwa rumfunan zabe. Akan ba su kayakin ne bayan an tantance yawan kayakin sannan ma’aikaci ya sanya hannu a kan takarda dake tabbatar da adadin kayan da aka ba shi.



Ma'aikatan zabe kenan a hukumar zabe reshen Lafiya dake jihar Nasarawa inda wasu suke jiran a basu alawus-alawus dinsu wasu kuma tuni an basu. Hukumar ta ce komai na tafiya dai-dai kuma tana sa ran kammala biyansu da misalin karfe shida na yammaci.


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Katsina inda daga nan zai tafi mahaifarsa Daura.
A ranar Asabar ne ake sa ran gudanar da zaben Shugaban kasa a Najeriya inda Shugaba Buhari ne dan takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar APC.

Asalin hoton, Buhari Sallau/Facebook

Asalin hoton, Buhari Sallau/Facebook

Asalin hoton, Buhari Sallau/Facebook
Wasu masu motocin haya sun rage kudin da fasinjoji za su biya domin tafiya zabe wasu kuma ba su rage ba.
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya reshen jihar Makurdi da ke Benue ta fara shirin kai ma'aikatanta musamman na wucin gadi zuwa mazabu da ke karkashin kananan hukumomi.




Itama jihar Kaduna ta dau harma wajen shirye-shiryen zaben. A lokacin da aka dauki wannan hoto, hukumar zaben tana shirye-shiryen fara rarraba kayayyakin zuwa kananan hukumomin dake jihar.



A ranar Juma'a ne hukumar zaben Najeriya wato INEC ta amince da masu yin takara a karkashin jam'iyyar APC a jihar Zamfara bayan an dade ana samun hukunce-hukunce masu cin karo da juna daga kotuna daban-daban a kasar.
A yanzu dai hukumar zaben kasar ta ce ta bi umarnin kotu kuma ta mayar da 'yan takarar majalisar tarayya da na jiha da kuma na gwamna a jihar.

Asalin hoton, INEC Nigeria/Twitter