Gwamna Ganduje ya kada kuri'a
Lokacin da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kada kuri'a.


Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.
Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu
Lokacin da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kada kuri'a.


Lokacin da mataimakin shugaban kasar Nigeria, Yemi Osinbajo ya kada kuri'a.

Asalin hoton, Nigeria
Dantakarar Gwamna a jamiyar APC a jihar Sokoto Ahmad Aliyu Sokoto yayin da yake kada kuriar sa a rumfar zabe mai lamba 19B a makarantar magajin Rafi sokoto.

Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce a matsayinsa na mai fafutikar ganin an wanzar da mulkin dimokradiyya, zai yi biyayya ga sakamakon zaben shugaban kasar.
Ya bayyana haka ne bayan ya kada kuri'arsa a birnin Yola na jihar Adamawa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya je wurin kada kuri'arsa ne tare da mai dakinsa, Hajiya Titi Atiku.
"Ina sa ran za a samu sauyin gwamnati cikin lafiya", in ji Atiku.
Da aka tambaye shi ko zai amince idan ya sha kaye, sai ya ce "Ni mai fafutukar kare dimokradiyya ne".


Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kada kuri'arsa a birnin Yola na jihar Adamawa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya je wurin kada kuri'arsa ne tare da mai dakinsa, Hajiya Titi Atiku.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kada kuri'arsa a jiharsa ta Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar.
Bayan zaben, bai fadi mutumin da ya zaba ba, inda ya gaya wa manema labarai cewa idan ya fadi mutumin da ya zaba wasu za su fassara hakan da cewa tamkar ya yi yakin neman zabe ne.
Mr Jonathan ya tsaya takara a zaben 2015 amma ya ha kashi a hannun Muhammadu Buhari.
Ana yi masa kallo a matsayin dattijo bayan da ya amince da shan kaye a zaben.

Zaben Najeriya shi ne ya kankane muhawara a shafukan sada zumunta minda a shain Twitter ake muhawara kan maudi'i daban-daban cikin su har da Trendsmap: #NigeriaDecides2019, #VoteNotFight da kuma #ElectionNotWar kamar yadda muka gani a Trendsmap.

Asalin hoton, Trendsmap


Asalin hoton, Zabe


Mata sun sa himma wajen yin ruwa da tsaki a zabar wanda zai shugabanci kasar nan



Asalin hoton, Zabe
Wata tsohuwa na jiran ta kada kuri'a a mazabar Gayam da ke Lafiya, Nasarawa.

Wata matashiya ce da ta je wajen zabe ba ta da katin da za ta gudanar da zabe sai ta shiga sayer da katin kira na waya a Abuja.



Yadda mutane suka yi layin kada kuri'a a makarantar Firamari a Jahun a jihar Bauchi.


Tsohon shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kada kuri'a tare da mai dakinsa.



Wasu matasa ne da aka tantance suke yin karta kafin su kada kuri'a a jihar Lehas.