Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019

Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu

  1. Saita Na'urori

    Na'urorin tantance masu kada kuri'a kenan watau card readers ake yi wa chargy da kuma saita su a gabannin zaben. Wannan hoton dai an dauke shi ne a ofishin hukumar zabe dake karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa

    Na'urorin tantance masu kada kuri'a
    Na'urorin tantance masu kada kuri'a
  2. Tantance kayayyakin zabe

    Tuni aka rarraba kayyayakin zabe a kananan hukumomin dake jihar Kano. Karamar hukumar Fagge kenan a lokacin da ma'aikatan zaben ke tantance kayayyakin.

    Kano
    Kano
  3. Ma'aikatan Zabe

    Ma'aikatan zabe na wucin gadi kenan a yayin da suke duba sunayensu a jihar Kano. Suna duba sunayen ne domin sanin rumfar zaben da za su gudanar da ayyukansu a ranar zaben.

    Ma'aikatan wucin gadi
    Ma'aikatan wucin gadi
  4. Rahoto kai tsaye

    Jama'a barkanmu da wannan lokaci, Mustapha Musa Kaita ne zai kawo maku bayanai kai tsaye a wannan shafin kan yadda ake shirye-shiryen gudanar da zaben Najeriya. Latsa nan domin bin mu a shafin mu na Facebook