Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019
Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gonarsa bayan zabe

Asalin hoton, FACEBOOK/ BUHARI SALLAU

Asalin hoton, FACEBOOK/ BUHARI SALLAU
An dage tattara sakamakon zabe na kasa sai Litinin
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Najeriya Mahmud Yakubu ya ce an dage tattara sakamakon zabe na kasa sai ranar litinin.
Ya ce tattara sakamakon zai fara ne ranar Litinin 25 ga watan Fabrairun 2019 da misalin 11:00 na safe.

Asalin hoton, Getty Images
Yaushe Buhari da Atiku za su san matsayinsu?, Daga Yusuf Ibrahim Yakasai

Yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a Najeriya, hankula sun karkata ne zuwa lokacin da za a bayyana sakamakon zaben.
Zai yi wuya dai a iya cewa ga lokacin da hukumar zabe INEC za ta bayyana sakamakon na zaben shugaban kasa.
A bisa dokokin Najeriya, shugaban hukumar zabe ta kasa ne kawai zai iya bayyana sakamakon zaben, bayan ya gama karbar sakamako daga turawan zabe na jihohi.
A zaben 2015 dai an bayyana sakamakon zaben na shugaban kasa ne ranar Talata, ma’ana kwana uku bayan zaben.
Sai dai a bana babu tabbas ko za a iya bayyana sakamakon a ranar Litinin din ko kuma za a wuce lokacin, musamman ma duba da cewa ana sake zaben a wasu yankunan Najeriya ranar Lahadi.
Watakila abin da zai iya janyo tsaiko wajen sanar da sakamakon zaben na bana shi ne tashe-tashen hankulan da suka faru a wasu jihohin kasar.
Alal misali har zuwa yammacin Lahadi ba a iya kai sakamakon ko da karamar hukuma daya ba, a ofishin hukumar zabe inda daga nan ne za a tattara sakamakon sannan a kai Abuja.
Rahotanni daga Kogi sun ce wasu ‘yan daba ne suka tare hanyoyi suka hana kai sakamakon, duk kuwa da kokarin da jami’an tsaro suke yi na tarwatsa su.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta Kogi ta tabbatar da mutuwar mutum uku a tashin hankalin da ya barke a ranar Lahadi.
Haka kuma rikicin da ya barke a jihar Rivers ma ranar Asabar da aka gudanar da zaben zai iya kawo jinkiri wajen samun cikakken samakon zaben a kan kari.
An ba da rahotannin samun asarar rayuka a Abonnema, da ke karamar hukumar Akuku Toru a jihar Rivers, abin da ya hana gudanar da zaben ranar Asabar kamar yadda aka tsakara.
A karamar hukumar Bonny ta jihar Rivers din ma an samu tashin hankali da kuma harbe-harbe, lamarin da ya hana gudanar da zaben a wasu sassan yankin.
Azamar da hukumar zaben kasar INEC za ta yi wajen sake gudanar da zabuka a yankunan da suka gagara, da samar da cikakken tsaro na daga abubuwan da za su iya takaita dogon jira wajen bayyana sakamakon zaben, da a yanzu shi ne ya fi komai muhimmanci ga ‘yan Najeriya.
Yadda za ku saurari shirinmu na rediyo kai tsaye
Latsa nan domin sauraren shirinmu na musamman kan zabe kai tsaye.

Kole Shettima a kan zaben Najeriya
Bayanan bidiyo, Kole Shettima a kan zaben Najeriya An kama Buba Galadima a Abuja

An kama Buba Galadima a Abuja ranar Lahadi, kamar yadda iyalansa suka shaida wa BBC.
Wani makusancinsa ya ce suna zargin jami’an tsaron farin kaya ne na DSS suka kama dan siyasar da rana jim kadan bayan ya fita daga gidansa.
Wani makusancin dan siyasa a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugabacin Najeriya a jam’iyyar PDP da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun tura wakilansu zuwa ofishin DSS domin bincika dalilin kama Buba Galadima.
Sai dai har kawo yanzu babu wani bayani daga hukumar ta DSS kan zargin kama jigon a bangaren hamayya.
A ranar Asabar, Festus Keyamo da ke magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Muhammmadu Buhari ya yi kira da a kama Buba Galadima, bisa zargin yana shirin bayyana sakamakon zabe na boge.
Buba Galadima dai shi ne shugaban R-APC wani bangare da suka balle daga jam’iyyar APC.
Kuma yana cikin masu magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar da ke takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP.
An soke sakamakon zabuka a rumfuna 12 dake karamar hukumar Kaltungo a jihar Gombe.
Rumfunan na da masu rajistar zabe dubu 8559. Rumfuna 10 suna a Kaltungo, biyu kuma na Tula.
An soke zabukan ne sakamakon matsala da aka samu da na'urorin tantance masu kada kuri'a watau card readers.
Wasu daga cikin ma'aikatan BBC
Wasu daga cikin ma'aikatan BBC a bakin aiki yayin da 'yan Najeriya ke jiran bayanai kan sakamakon zabe.

Bayanan hoto, Badriyya Kalarawa da Ahmed Abba Abdullahi sai kuma Auwwal Isa Rafsanjani (mai sharhi) 
Bayanan hoto, Yusuf Tijjani 
Bayanan hoto, Habiba Adamu Shugaban INEC yana yi wa 'yan Najeriya jawabi
Shugaban hukumar Mahmud Yakubu ya ce ''Muna sane da duk irin hatsaniyar da aka samu a wasu jihohi da kuma yadda aka far wa jami'anmu da kuma 'yan hidimar kasa. ''Mun yi Allah wadai da wannan lamari kuma muna fatan hukumomi za su dauki mataki kan bata garin da suka jawo hakan. ''Muna fatan Allah ya ji kan wadanda suka rasu.''
A cikin bayanin na shugaban, ya bayyana cewa akwai ma'aikaciyar hukumar zaben da aka harba da bindiga a jihar Ribas.
Ya bayyana cewa yanzu haka sakamakon jihar Ekiti na kan hanya zuwa Abuja.
Jihar Ekiti ce ta farko wajen kammala tattara sakamakon zabe.
Ya kuma kuma ce labarun da ake yadawa na an soke zabe a Abuja ba gaskiya bane.

Shin mutane na da hurumin bayyana sakamakon zabe a intanet?
Kakakin hukumar zabe a Najeriya Aliyu Bello yayi bayani danagane da hakan a wannan bidiyon.
An fara kammala zabe a rumfunan da ake gudanar da zabe ranar Lahadi
Kamar yadda hukumar zabe a Najeriya ta bayyana cewa za a gudanar da zabuka a wasu rumfunan zabe a kasar ranar Lahadi sakamakon matsaloli da aka fuskanta ranar Asabar, yanzu haka an kammala zabe a rumfar zabe ta Zawan A dake jihar Filato a kasar.

Yadda ake muhawara a shafin Twitter kan zabe
'Yan Najeriya na tafka muhawara a Twiiter da maudu'in #BuhariIsWinning da #AtikuIsWinning. Shin menene ra'ayinku?

Wasu ra'ayoyi daga shafin Twitter
Kauce wa X, 1Ya kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Kauce wa X, 2Ya kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Kauce wa X, 3Ya kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Rahoto kai tsaye
Jama'a barkanmu da wannan lokaci, Mustapha Musa Kaita ne zai kawo maku bayanai kai tsaye a wannan shafin kan yadda ake tattara sakamakon zabe da kuma sauran bayanai dangane da zaben Najeriya. Latsa nan domin bin mu a shafin mu na Facebook

'Yan ta'adda sun kai hari ga ofishin zabe a Osun
Yadda 'yan ta'adda suka kai hari a wani ofishin hukumar zabe dake Ijebu-Jesha a karamar hukumar Oriade dake jihar Osun a daren Asabar.


Ana shirin bayyana sakamakon zaben Kano
Tuni hukumar zaben Najeriya reshen jihar Kano ta kimtsa zauren tattara sakamako na jihar domin fara karbar sakamakon daga kananan hukumomi a fadin jihar.


Ra'ayoyinku a BBC Hausa Facebook
Masu bibiyar shafinmu na Facebook suna can suna tafka muhawara kan tattara sakamakon zaben Najeriya. Ga sakonnin wasu daga cikinsu:
Isah Major Major Allah ya sa a bayyana sakamakon zabukan da muka yi cikin adalci.
Ahmad Shukrat Mu dai zaben bana Alhamdullah, komai ya tafi daidai sai dai matsalar guda daya ce ta rashin fitowar jama'a musamman mata.
Isah Isah Kwafsi Asarara Hakika hankali akasarin 'yan Najeriya ya karkata a kan hukumar zabe ta kasa, don haka muna fatan za ta kamanta gaskiya da adalci a yayin fitar da sakamakon zabe.
Za a sake gudanar da zabe a Zamfara
Hukumar zabe a Najeriya ta bayyana cewa akwai wasu kananan hukumomin da za a gudanar da zabe a ranar Lahadi bayan jinkirin da aka samu a wasu wurare.
Hakan na zuwa ne bayan an samu jinkiri wajen kai kaya da kuma matsalar tsaro a wasu sassan kasar.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar zaben a kasar, Malam Aliyu Bello, ya shaida wa BBC cewa za a gudanar da zabe a kusan kananan hukumomi takwa na jihar.

Bidiyon cibiyoyin tattara sakamakon zabe
Ku kalli bidiyon cibiyoyi daban-daban na tattara sakamakon zaben Najeriya.
Bayanan bidiyo, Daga cibiyar tattara kuri'u na wasu jihohi
