Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019

Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu

  1. 'Yan bangar siyasa sun hana kai sakamako hukumar zabe a Kogi

    'Yan bangar siyasa sun tare wa jami'an INEC hanyar don hana su kai sakamakon zabuka zuwa hedikwatar hukumar da ke Jihar Kogi.

    Wakilin BBC na wucin gadi da ke wajen ya ce tuni 'yan sanda da sojoji suka isa yankin don shawo kan lamarin wanda ke faruwa a yankin Kogi ta Yamma.

    Kazalika kuma ana samun tashe-tahsen a Kogi ta Gabas sakamakon hana kai sakamakon zabe zuwa hukumar INEc ta jiha, abun da ke ta jawo tsaiko wajen tattara bayanan sakamakon 'yan majalisar dattijai da na jihar.

    Kwamishinan zabe na jihar Kogi James Apam ya ce har yanzu ba su samu sakamako ko daya ba daga kananan hukumomi 21 na jihar. A yanzu dai rahotanni na cewa ana cike da fargabar abun da ka iya faruwa na rikici a jihar.

    Sakamakon zaben Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

  2. An soma tattara sakamakon zabe a Maiduguri

    An soma tattara sakamakon zabe a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
  3. Ana tattara sakamakon zaben Benue

    Ma'aikatan hukumar zaben Najeriya reshen jihar Benue sun soma isa Makurdi, babban birnin jihar inda ake tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya da aka gudanar ranar Asabar.

    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
  4. Labarai da dumi-dumi, Za a soma tattara sakamakon zaben Abuja

    Hukumar zaben Najeriya ta ce da misalin karfe biyu na rana a agogon kasar ne za a soma tattara sakamakon zaben da aka yi ranar Asabar. Za a rika karbar sakamakon zaben ne dada wurin jami'an zabe na jihohi.

  5. Titunan birnin Fatakwal sun zama fayau

    Titunan birnin Fatakwal, babban birnin jihr Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya sun kasance fayau bayan zaben da aka yi ranar Asabar.

    Ba a samu tashin hankali a Fatakwal ba, sai dai rahotanni daga wasu kananan hukumomi kamar su Okrika, Ikwerre, Emohua, Abua/Odual, Andoni, Asari Toru, Akuku Toru da kuma Bonny sun ce an samu yamutsi.

    Hukumar zabe ta kasa reshen jihar ta ce za ta sanar da ranar da za a gudanar da zabe a Akuku Toru, Bonny da wasu mazabu na Okrika, inda ba a yi zabe ranar Asabar ba saboda barkewar rikici.

    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
  6. Ana tattara sakamakon zaben Ekiti

    Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta reshen jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin kasar ta soma tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majlaisar dokokin tarayya da aka yi ranar Asabar.

    Nan gaba kadan za ta soma bayyana sakamakon zaben.

    Sakamakon zaben Najeriya
  7. Matashin da ya mutu bayan ya kada kuri'a

    Ku saurari tattaunawar da abokin aikinmu Is'haq Khalid ya yi da Alhaji Mamman Tela, mahaifin Muhammadu Bashar, matashi dan shekara 25 da ya mutu jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a mazabar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jefa kuri'arsa.

    Bayanan bidiyo, Daga bakin mahaifin yaron da ya rasu bayan ya kada kuri'arsa
  8. Ana dakon sakamakon zabe a Nasarawa

    Al'umar jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya na can suna dakon sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yanb majalisar dokokin tarayya inda ma'aikatan zabe suka hallara a wuraren tattara sakamakon zaben domin soma bayyana shi. Wakiliyarmu Raliya Zubairu ta aiko mana da bayanai da hotuna daga Lafiya, babban birnin jihar.

    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
  9. An sake bude kasuwanni a Najeriya

    'Yan kasuwa a sassa daban-daban na Najeriya sun bude shagunansu kwana guda bayan gudanar da zaben kasar, kamar yadda kuke gani a wadannan hotunan da wakilinmu a Adamawa, Muktari Adamu Bawa ya aiko mana daga kasuwar Jimeta.

    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
  10. An soma tattara sakamakon zaben Gombe

    Wakiliyarmu ta wucingadi a Gombe, Rebecca Mu'azu, tana Mallam Sidi, hedikwatar karamar hukumar Kwami, inda aka soma tattara sakamakon zaben yankin Gombe ta Arewa. Gombe ta Arewa na da kananan hukumomi biyar - Dukku, Funa Kaye, Gombe, Kwami da Nafada. A nan ne ake tara sakamakon zabe. Yanzu dai ana kan kawo sakamakon, sai dai wurare kamar Gadam, Bojude, Konfulata, da Kwami basu zo da nasu sakamakon ba tukuna, domin wasu wuraren sun yi nisa da wurin tara sakamakon, wasu kuma kamar Konfulata tana da mazaba da yawa.

    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
  11. 'Yan sanda sun kama barayin akwatun zabe a Kano

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce jami'anta sun kama mutum takwas da take zargi da satar akwatun zabe ranar Asabar.

    Kakakin rundunar, DSP Haruna Abdullahi, ya ce sun kama mutum hudu ne dauke da katin zabe na dindindin a yankin Sabon Gari yayin da suka cafke sauran mutum hudun a Gabasawa bayan sun lalata wasu akwatun zabe.

    Ya kara da cewa an tsare dukkan mutanen a sashen binciken masu laifuka na rundunar.

    Sakamakon zaben Najeriya
  12. Sojoji sun kashe 'yan bangar siyasa a Rivers

    Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan bangar siyasa a jihar Rivers da ke kudu maso kudancin kasar.

    Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Kanar Sagir Musa ya fitar ta ce an kashe 'yan bangar siyasar ne bayan sun kai farmaki kan dakarun sojojin da ke aikin tabbatar da tsaro lokacin zabukan ranar Asabar.

    Ta kara da cewa an kashe soja daya a arangamar da aka yi tsakaninsu da 'yan bangar siyasar.

    Sakamakon zaben Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Sakkwatawa na shirin sanin sakamakon zabe

    Hukumar zabe mai zaman kanta reshen jihar Sokoto na can tana shirin soma bayyana sakamakon zabukan da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu. Wakilinmu na wucingadi, Usman Binji, ya ce akasarin sakamakon zaben ya kammala.

    Sakamakon zaben Najeriya
  14. An shirya bayyana sakamakon zaben Kaduna

    Jami'an hukumar zaben Najeriya da ke cibiyar tattara sakamakon zabe ta Badarawa a Arewacin Kaduna sun shirya tsaf domin soma bayyana sakamakon zabe, kamar yadda wakilinmu na wucingadi, Umar Malali ya aiko mana a wadannan hotuna.

    Sakamakon zaben Najeriya
    Sakamakon zaben Najeriya
  15. Yemi Osinbajo ya sha kaye a rumfarsa

    Tun da farko mun kawo muku rahotanni kan sakamakon zabukan wasu mazabu, ciki har da wanda jam'iyyar PDP ta lashe zaben shugaban kasa a rumfar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

    Kazalika jam'iyyar ta PDP ta yi nasara a rumfar zaben dan takarar gwamnan Lagos na jam'iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu.

    Dan takarar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya samu yawan kuri'u 384, a rumfar dan takarar mataimakin shugaban kasar na jam'iyyar APC a Lagos.

    A akwatu mai lamba Ward 019 da ke mazabar Lateef Jakande/Femi Okunnu a unguwar Ikoyi inda Sanwo-Olu ya kada kuri'a, PDP ta samu 52, yayin da APC ta samu 48.

    Zaben Najeriya
    Zaben Najeriya

    Asalin hoton, Twitter/@jidesanwoolu

  16. Barkanmu da wannan lokaci

    Da fatan kun wayi gari lafiya. Nasidi Adamu Yahaya ne zai kawo muku labarai da rahotanni har ma da hotuna da bidiyo kan yadda ake tattara sakamakon zaben Najeriya da aka gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu. Za ku iya tafka muhawara a shafinmu na Facebook a BBC Hausa

  17. Sai kuma gobe

    A nan za mu yi sallama da ku inda za mu dakatar da kawo rahotanni da bayanai da muke kawo wa kai-tsaye dangane da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a Najeriya.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu inda za mu ci gaba da kawo bayanai kai tsaye da suka shafi sakamakon zaben da 'yan Najeriya yanzu suke jira daga Hukumar zabe INEC.

    Da fatan za ku ci gaba da kasance wa da mu.

    Awwal Janyau da Abdulbaqi Jari ne ke maku sallama.

    Ma'aikatan BBC
  18. Ana jin karar harbe-harbe a Lagos

    Mazauna unguwar Ikoyi a Lagos sun ce an shafe sa'o'i suna jin karar harbe-harbe.

    Amma daga baya an girke jami'an tsaro.

  19. Yadda muke kawo maku bayanai, Zaben shugaban kasa a Najeriya

    Awwal Ahmad Janyau da Abdulbaqi Jari ke kawo maku bayanai kai-tsaye game da zaben Najeriya.

    Ma'aikatan BBC
  20. Me kada Buhari a fadarsa yake nufi?, Zaben shugaban kasa a Najeriya

    Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya kada abokin hamayyarsa Shugaba Muhammadu Buhari na APC a daya daga cikin rumfunan fadar shugaban kasar.

    Wakilin BBC a fadar Shugaban Najeriya Haruna Shehu Tangaza shi ne ya tabbatar da sakamakon inda ya ce PDP ta lashe rumfa mai lamba 022 yayin da kuma APC ta ci rumfa mai lamba 021, mazabun da ke cikin fadar shugaban kasa.

    PDP ta samu kuri'u 525 a rumfa mai lamba 022, yayin da APC ta samu kuri'a 465.

    A rumfa ta biyu kuma mai lamba 021, APC ta samu kuri'u ne 552, yayin da PDP ta samu 502.

    PDP ce kuma ta fi yawan kuri'u a zaben majalisar dattawa a mazabar.

    Buhari da Atiku

    Asalin hoton, Getty Images