Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019

Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu

  1. An gama kada kuri'u a wasu rumfunan zabe

    Tuni dai aka gama kada kuri'u a wasu rumfunan zabe a fadin Najeriya. Akasarin

    rumfunan da aka gama kada kuri'a a yanzu haka ana rarrabewa kafin a fara kirgawa.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zaben ta bayyyana cewa ta kara lokaci ga wasu rumfunan zaben da aka samu jinkiri.

    Ajiya Ward
    Ajiya Ward
  2. Wasu daga cikin ra'ayoyinku daga Facebook

  3. Jihohin da mutane suka fi fitowa kada kuri'a a yanzu haka

    Jihar Katsina ce ta zo farko wajen tururuwar fitar jama'a inda aka samu nasarar tantance mutane da kusan nasarar kashi 100 bisa 100.

    Jihohin Ekiti da Kebbi da Ogun da Adamawa an samu kusan kashi 34 cikin 100 da misalin karfe 12:00 na rana.

    Sauran jihohin da ba'a samu fitowar mutane ba sun hada da jihohin Delta da kashi 32 sai Borno 35 da Sokoto 31 da Zamfara 31 sai Plateau kashi 40 cikin 100.

  4. INEC ta kara lokacin zabe a rumfunan da aka samu jinkiri

    Hukumar zabe a Najeriya ta kara lokaci musamman ga rumfunan zaben da aka samu jinkiri kafin fara zabe.

    Jami'in hukumar mai kula da wayar da kan masu zabe da kuma watsa labarai Festus Okoye ya bayyana haka.

    Ya ce za a kara lokacin ne daidai da jinkirin da aka yi a kowace rumfar zabe. Ya bada misali inda ya ce rumfar da aka fara tantance masu zabe karfe 9:00 sai karfe 3:00 za a gama tantancewar.

    Mista Okoye ya ce dalilan da yasa aka samu jinkirin sun hada da matsalar da aka samu da na'urar card reader a wasu wurare sai kuma rashin takardun rubuta sakamako da kuma jinkiri da aka samu da direbobin mota.

  5. Ma'aikata na jiran masu zabe

    IMa'aikatan hukumar zabe a mazabar Mushin a jihar Legas ne ke zaune suna jiran masu kada kuria'a.

    zabe
  6. Wasu rumfunan zabe a Azare har yanzu ba kai kayan zabe ba.

    Wasu rumfunan zabe a Azare, jihar Bauchi, wadanda har yanzu ba kai kayan zabe ba.

    Mazabun sun hada da urban maternity 041,da Sule Dan makera 042 da S/malamai 043 da Gwani Gambo,

    Zabe
    Zabe
    Zabe
    Zabe
  7. An ci karo da tsaiko a Adaka da ke Makurdi a jihar Benue

    An ci karo da tsaiko a mazabar Adaka da ke Makurdi a jihar Benue, bayan da ba a biya wasu ma'aikatan wucin gadin zabe alawus din su ba,,.

    Hakan ya sa suka ki yin aiki har sai an biya su. An kuma samu tsaiko wajen raba kayan aiki, sakamakon karancin sufurin da za a aike da kayan zabe..

    Wadan da suka je yin zabe a mazabar ta Adaka sun samu gindin inuwa sun zauna da zummar kada kuri'a da zarar an kamo bakin zaren.

    zabe
  8. An fara kada kuri'a a mazabar Ciroma

    Sai yanzu ne aka fara kada kuri'a a mazabar Ciroma da ke jihar Nasarawa.

    zabe
  9. Mazabar Ngurore da ke Yola jihar Adamawa

    zabe
    zabe
  10. Saraki ya jefa kuri'arsa

    Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki, ya jefa kuri'arsa a mazabarsa da ke unguwar Agbaji, a karamar hukumar Ilori ta Yamma da ke jihar Kwara.

    Daga bisani, Saraki ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriyar da ba su yi zabe ba su je su kada kuri'unsu cikin kwanciyar hankali.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Abdussalam ya kada kuri'arsa

    Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya kada kuri'arsa a Minna, babban birnin jihar Naija.

    Ya yi kira ga 'yan takara su amince da sakamakon zaben.

    Janar Abubakar ya yaba da irin fitowar da masu zabe suka yi domin kada kuri'unsu.

    Ya yi mulki daga watan Yunin 1998. Ya mika mulki ga Olusegun Obasanjo a watan Mayun 1999, bayan an yi zabe.

    zabe
    zabe
  12. Fitacciyar mawakiya Tiwa Savage ta kada kuri'a

    Fitacciyar mawakiyar nan 'yar Najeriya Tiwa Savage ta kada kuri'arta.

    Hoton da ta wallafa a shfinta na Twitter ya nuna ta tana dora babban yatsanta kan na'urar card reader.

    Tiwa Savage ta yi wakoki da dama cikin har da All over, Get It Now da kuma Once Upon a Time.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Zaben Najeriya: Labari cikin hotuna

    Bayanan bidiyo, Zaben 2019: labari a cikin hotuna
  14. Fashola ya kada kuri'a

    Ministan ma'aikatar ayyuka da gidaje da samar da hasken lantarki, Babatunde Fashola da matarsa Emmanuella Abimbola Fashola lokacin da suke kada kuri'a a mazabarsa ta kan titin Itolo a Surulere a Legas.

    zabe
    zabe
    zabe
  15. Faduwa zabe kaddara ce daga Allah — Tambuwal

    Gwamna Aminu waziri Tambuwal ya ce idan jamiyar PDP ta fadi zabe zasu dauke shi a matsayin kaddara daga Allah. Ya fadi haka jim kadan bayan jefa kuri'arsa a rumfar zabe mai lamba 011 a garin Tambuwal na jihar Sokoto.

    Zaben Najeriya
  16. Mataimakin Atiku ya kada kuri'arsa

    Dan takarar mataimakin shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Peter Obi, ya shaida wa BBC cewa tsarin zaben kasar da matukar "wahala".

    Ya shaida wa wakiliyar sashen Igbo na BBC Chioma Obianinwa a Anambra bayan ya kada kuri'arsa cewa ya yi zabe a kauyensa na Amatutu.

    "Tsarin zaben yana da sarkakiya, ba shi da saukin da na yi tsammani za a samu. An dauki lokaci kafin mu iya kada kuria," in ji shi.

    Zaben Najeriya
  17. Dogara ya yi zabe a mazabarsa ta Gwarangah

    Shugaban majalissar wakilai Hon. Yakubu Dogara ya kada kuri'arsa tare da mai dakinsa Gimbiya Dogara a mazabarsu ta Gwarangah karamar hukumar Bogoro da ke jihar Bauchi.

    zabe
    zabe
    zabe
  18. Ana zabe a karamar hukumar Geidam

    Duk da tashin bama bamai mutane sun fito domin kada 'kuria a karamar hukumar Geidam a jihar Yobe.

    Zabe
  19. Zabe na tafiya daidai a Lagos

    Wakilin BBC a Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya, ya ziyarci rumfunan zabe a Ikeja inda ya dauki hotunan yadda zabe ke gudana ba tare da matsala ba.

    Ana iya ganin masu kada kuri'a suna dora hannunsu kan na'urar card reader wavcce ke tantance su.

    Zaben Najeriya
    Zaben Najeriya
  20. Kayan zabe a Unguwar Sarki a jihar Kaduna

    Wani sashen da za a kada kuri'a a Unguwar Sarki a birnin Kaduna.

    Zabe
    Zabe
    Zabe
    Zabe