Bayanan hoto, Peter Obi na samun goyon baya a Legas, da ta kasance mahaifa ga Bola Ahmed TinubuBayani kan maƙala
Marubuci, Nduka Orjinmo
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
An wallafa
A yayin da Najeriya ke shirin gudanar da babban zaɓe a ranar 25 ga watan Fabrairu, Legas babban birnin kasuwancin ƙasar ya kasance jihar da ke da ɗumbin masu zaɓe da kuma za su iya tsara makomar ƙasar.
Legas da ta kasance mai yawan masu kaɗa kuri'a - kusan miliyan bakwai - ta zama wata muhimmiyar fagen daga a fafatawar da kowanne bangare ke samun goyon bayan matasa, da akasari suka fito daga gidajen da basu da abin a zo a gani da suka kasa samun aikin yi.
Jimoh Adesina, mai shekaru 40, direba ne a Legas, wanda ke goyon bayan Bola Tinubu, na jam'iyyar APC mai mulki, ya ce "Ya samar da ayyukan yi a baya kuma zai sake yin hakan."
Duk da yake tukin motar bas aiki ne mai kyau, ba aiki ne da mai matakin karatun digiri a kwalejin kimiyyar fasaha zai yi tsammanin yi ba, amma Mista Adesina ya yi farin ciki da kasancewa cikin aiki.
Rashin aikin yi da tattalin arziki sune manyan abubuwan da ke damun masu kaɗa kuri'a a zaɓen. Duk da kasancewarta ƙasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki da samar da mai a nahiyar Afirka, huɗu daga cikin mutum 10 na 'yan Najeriya na rayuwa a kasa da kangin talauci, a cewar bankin duniya.
Mista Tinubu ya ta'allaka yakin neman zaɓensa a kan irin ayyukan da ya yi lokacin da yake gwamnan jihar Legas, da kuma nasarorin da jam'iyyar da ya taimaka wajen kawo wa kan karagar mulki a 2015 ta samu. An fi ganin hakan a tsarin sufuri na motocin bas da ya kawo a Legas na BRT wanda ya sauƙaƙa cunkoson ababen hawa a birnin.
Tashar mota ta zamani ta bas ta maye gurbin al'amuran da suka tada hankula a babban wurin Oshodi, yayin da ake ci gaba da gudanar da gwajin sabon layin dogo na lantarki wanda ya wuce wani gidan wasan kwaikwayo na ƙasa da aka gyara.
Bayanan hoto, Ana fatan cewa sabon layin dogon zai ƙara rage wahala na cunkoson ababen hawa a Legas
A ɗaya gefen teku, akwai wani sabon layin dogo na ƙasa wanda ya haɗa Legas da birnin Ibadan ta tasha a Abeokuta, da kuma wata gada mai matukar muhimmanci a yanzu da ta kai kan babbar kasuwa ta Lekki Peninsula, inda matasa 'yan Najeriya masu kere-kere ke rayuwa cikin wasu gidaje.
Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, yana gina matatar mai a wani yanki mai ciniki maras shinge na gwamnati, kusa da wata sabuwar tashar jiragen ruwa da ta fara aiki wanda China ta gina, ana kuma magana kan wata gada ta huɗu da za ta haɗe babban yankin masu aikin yi da sauran yankunan kasuwanci da ke tsibirin Legas.
Duka waɗannan sun canza Legas daga yanayin da take ciki kafin 1999.
Su wane ne ke takarar shugabancin Najeriya?
Karin bayani kan 'yan takarar shugaban ƙasa na Najeriya
Zaɓi ɗan takara don ganin bayanansa
Bola Tinubu
All Progressives Congress (APC)
Shekaru: 70
Ya yi karatun akanta a jami'ar Chicago State University.
Gwamnan Jihar Legas karo biyu daga 1999 zuwa 2007.
Ya wakilci Legas ta Kudu a Majalisar Dattijai daga 1992 zuwa 1993.
Gagarumin ɗan siyasa a Najeriya, wannan ne karon farko da yake yin takarar shugaban ƙasa.
Adawa da mulkin soja.
Ya ninka kuɗin shigar Jihar Legas na shekara-shekara sama da sau huɗu daga biliyan N22.2 a 1999 zuwa biliyan N220.9 a 2007.
Ya fara aiki a matsayin mai binciken kuɗi da kuma ma'aji a kamfanin Mobil Producing Nigeria, ɗaya daga cikin kamfanonin man fetur mafiya girma a ƙasar.
Inganta harkokin fitar da kaya daga Najeriya zuwa ƙasashen waje da kuma rage dogaro da sayen kaya daga waje.
Rage rabin adadi na rashin aikin yi tsakanin matasa cikin shekara huɗu da kuma ƙirƙirar ayyukan yi miliyan ɗaya a ɓangaren sadarwa cikin shekara biyu.
Gyara tsarin shari'a don mayar da hankali kan kare afkuwar laifuka da kuma inganta yarda kan jami'an tsaro.
Atiku Abubakar
Peoples Democratic Party (PDP)
Shekaru: 76
Ya rike mukamin mataimakin shugaban Najeriya daga 1999 - 2007.
Ya samu digiri na biyu a ɓangaren alaƙa tsakanin ƙasashe daga jami'ar Anglia Ruskin University da ke Ingila.
Tsohon jami'in kwastam ne wanda ya shiga siyasa a farkon shekarun 1980.
Sau biyar yana yin takarar shugaban ƙasa ba tare da nasara ba; a 1993, 2007, 2011, 2015, da kuma 2019.
Ya kafa jami'ar American University of Nigeria, wadda ta bai wa 'yan matan Chibock tallafin karatu bayan Boko Haram ta sake su.
Hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke da jari a harkokin fetur da noma da bankuna da sashen haɗa magunguna.
Ƙudirin sayar da kadarorin gwamnati.
Bai wa 'yan kasuwa ƙarin dama wajen haɓaka tattalin arziki.
Inganta haɗin kan ƙasa ta hanyar daidaito, da adalci tsakanin ƙabilun Najeriya.
Sauya tsarin tafiyar da gwamnati.
Peter Obi
Labour Party (LP)
Shekaru: 60
Gwamnan Jihar Anambra sau biyu daga 2007 zuwa 2014.
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019.
Ɗan kasuwa ne da ya karanta fannin falsafa a Jami'ar Najeriya, Nsukka.
Ya kafa wata gidauniya mai kuɗi dala miliyan 156 ƙunshe da kadarori ya zuwa lokacin da ya bar gwamnati.
Ya sauya Anambra daga matsayi na 26 zuwa na 1 a jerin jihohin da suka fi cin jarrabawar fita daga sakandare ta NECO da WAEC.
Ya mallaki harkokin hada-hada da suka samar da dubban ayyukan yi.
Tabbatar da sa ido a aikin gwamnati da kuma yaƙi da rashawa.
Mayar da Najeriya ƙasa mai sayarwa maimakon mai saye.
Fifita rayuwar ɗan Adam ta hanyar zuba jari a ɓangaren ilimin-komai-da-ruwanka na STEM, da sashen lafiya, da kuma ayyukan raya ƙasa.
Rabiu Kwankwaso
New Nigeria Peoples Party (NNPP)
Shekaru: 66
Ministan Tsaro daga 2003 zuwa 2007
Gwamnan Jihar Kano daga 1999 zuwa 2003, da kuma 2011 zuwa 2015.
Ya wakilci Mazaɓar Madobi a Majalisar Wakilai a 1992 da kuma Mazaɓar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.
Yana da digirin digirgir a injiniyanci daga jami'ar Sharda University da ke Indiya.
Ba da tallafin karatu da yunƙurin taimaka wa mutane.
Ƙara yawan ɗaliban firamare a 2011 daga miliyan ɗaya zuwa miliyan uku a 2015 lokacin da ya bar ofis.
Ya ƙaddamar da ciyar da ɗalibai 'yan firamare da ba su kayan makaranta kyauta.
Ya kafa Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil da kuma jami'ar Northwest, waɗanda su ne jami'o'in gwamnatin Kano kawai zuwa yanzu.
Samar da ayyuka ta hanyar zuba jari a ɓangaren noma.
Mista Tinubu ne ya kirkiro da yawancin wurare na zamani a Legas ko kuma waɗanda suke mara masa baya da suka gaje shi tun 2007 , ciki har da wani sabon birni na alfarma da ke gaɓar tekun Atlantika.
"Shi ne mahaifina," in ji Mista Adesina, wanda rayuwarsa ta haɗe da mutumin da ya ce ya biya masa kuɗin jarrabawa da na wasu a makarantun gwamnati a shekarar 2001, ya kuma ba shi wannan aiki a matsayin direba.
Yana ɗaya daga cikin mutane da dama a faɗin Najeriya waɗanda alherin mista Tinubu ya taɓa rayuwarsu, ta hanyar dukiyarsa ko albarkatun jihar. A cikin jerin sunayen sun haɗa da taurarin kwallon kafa da mawaƙa da 'yan siyasa da ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓensu da kuma 'yan kasuwa da ya ceto lokacin da suke kangin wahala.
Shi ya sa ya saka taken na zaɓensa mai suna Emi Lokan, wanda ke nufin Yanzu lokacina ne, a takaice kira ne na neman a biya masa bukatunsa ta hanyar goyon bayan takararsa ta shugaban ƙasa.
Asalin hoton, Nduka Orjinmo/ BBC
Bayanan hoto, Jimoh Adesina ya ce ba zai manta da Bola Tinubu ba saboda shi ya biya masa kuɗin makaranta da kuma samar masa aiki
Yanzu mai naɗa sarki, yana son ya zama sarki.
Duk da cewa jam'iyyarsa ta rasa irin goyon baya da ya samu bayan mulki na tsawon shekara takwas, sai dai, irin wasu ayyuka da take yi a wasu sassan ƙasar yana cikin abubuwan da ke bai wa mista Tinubu ƙwarin gwiwar ganin ya zagaya zuwa dukkan jihohi da ke faɗin Najeriya.
"Waɗanda ya haɗu da su, a yanzu sun canza matuka, yana kyautata rayuwar mutanen ta kowacce hanya,'' in ji Adekanye Adetutu, wani mai goyon bayan Tinubu, wanda ya ce shi ya biya masa kuɗin makaranta lokacin da yake makarantar sakandare.
Sai dai, 'yan adawa sun ce Tinubu, ya yi amfani da irin wannan alherin wajen kafa tsarin ba da goyon baya don samar da goyon bayan masu aminci da gina daular siyasa da kuma rike dukiyar ƙasa.
"Ya kamata Tinubu ya rabu da mu," in ji Daniella Brodie-Mends, 'yar shekara 25, wacce za ta yi zaɓe a karon farko, a wani tsohon dandalin 'yan mulkin mallaka da ke Legas, inda dubban mutane suka taru domin gangamin karshe na ɗan takarar jam'iyyar Labour, Peter. Obi.
Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam'iyyu suka yi muku
Tsare tsaren Jam'iyyu
All Progressives Congress
Manyan muradu
Bunƙasa fitar da kaya daga Najeriya da kuma rage dogaro kan shigo da kaya
Rage adadin matasa marasa aikin yi da kashi hamsin cikin ɗari a cikin shekara huɗu da kuma samar da ayyuka miliyan ɗaya a ɓangaren sadarwa na zamani.
Ɗaukar matakan tabbatar da cin gashin kan ɓangaren shari'a ta fannin kuɗi da gudanarwa.
Tattalin arziki
Tallafa wa masana'antun cikin gida ta hanyar sauƙaƙa musu kuɗin haraji.
Kula da farashin kaya domin rage hauhawar farashi
Cire tallafi kan gas cikin wata shida da kuma ƙara yawan gas ɗin da ake samarwa da kashi 20%.
Aikin yi
Samar da ayyuka miliyan guda ta ɓangaren sadarwar zamani a cikin watanni 24 na farkon gwamnati.
Rage adadin matasa marasa aikin yi da kashi hamsin cikin ɗari a cikin shekara huɗu.
Tallafa wa masu sana'a miliyan biyu da kuma ƙwararru domin horas da matasa hanyoyin samun aiki da fara kasuwanci.
Kiwon lafiya
Aiwatar da shirin inshorar lafiya na tilas wanda kashi 40 cikin 100 na jama'a za su amfana a cikin shekara biyu.
Ƙara adadi da kuma inganta ma'aikatan lafiya musamman waɗanda suke aiki a matakin farko.
Aiki tare da gwamnatin jihohi da ƙananan hukumomi don samar da asibitocin tafi da gidanka domin tabbatar da cewa kowa na da asibiti aƙalla kilomita uku a kusa ko kuma tafiyar minti 30.
Ƙarfafa gwiwa don samar da magunguna da rigakafi a cikin Najeriya.
Tsaro
Ƙara Inganta albashi da walwalar ma'aikatan tsaro da kuma samar da wani shiri na musamman domin bayar da alawus ga sojoji da suka samu rauni da kuma waɗanda suka rasu a kan aiki.
Samar da makamai masu inganci, da inganta ɓangaren sadarwa da sufuri a sansanonin sojoji.
Ƙara dauka da horas da sabbin ma'aikatan soji da ƴan sanda da jami'an tsaron sirri da sauran masu kayan sarki.
Kawar da kai hare-hare kan muhimman wurare na gwamnati
Ilimi
Samar da sabbin hanyoyin tantance ingancin duka cibiyoyin ilimi tun daga firamare har zuwa jami'a.
Samar da shirin gwaji na bayar da bashi ga ɗalibai.
Samar da wani asusun ɗalibai na musamman wanda babu lamunin gwamnati a ciki.
Cin hanci da rashawa
Ƙayyade adadin kuɗaɗen da za a iya kashewa kan samar da gine-ginen gwamnati da albashi da kuma kan zaɓaɓɓun shugabanni da ma'aikatan gwamnati.
Ƙara samar da haraji ta hanyar rage kuɗaɗen da suke zurarewa daga ɓangaren kuɗin.
Saka wa masu aiki tuƙuru da kawar da ayyuka da ma'aikatan bogi.
Kawo sauyi ɓangaren aikin gwamnati domin rage abubuwan da ke kawo cikas, ko rashin ingancin aiki, da kuma ɓarna.
Labour Party
Manyan muradu
Gudanar da sauye-sauye a aikin gwamnati da ɓangaren shari'a domin tabbatar da bin doka, da yaƙi da rashawa da kuma tsimin kuɗi wurin tafiyar da gwamnati.
Mayar da Najeriya ƙasar da ke sana'anta abubuwan buƙata a maimakon sayowa daga wasu ƙasashe.
Fifita bunƙasa al'umma ta hanyar zuba jari a ɓangaren ilimin kimiyya da lafiya, abubuwan kawo ci gaba.
Tattalin arziki
Ɗora tattalin arziƙin Najeriya a kan tafarkin ƙirƙira da samar da kamfanoni ta yadda ƙasar za ta rinƙa fitar da kaya zuwa waje.
Rage tashin farashin kaya, da tabbatar da cin gashin kai na babban bankin ƙasar, da kyautata tsarin biyan haraji.
Rage dogaron da Najeriya ke yi kan man fetur ta hanyar inganta ɓangaren masana'antu.
Sassauta takunkumi kan kayan da ake shigowa da su daga ƙasashen waje da canjin kuɗi, tare kuma da samar da tsarin musayar kuɗi guda ɗaya.
Aikin yi
Faɗaɗa hanyoyin samar da kuɗi ga ƙanana da matsakaitan sana'o'i, da mata da matasa domin rage matsalar rashin aikin yi.
Zuba jari a ɓangaren bunƙasa al'umma.
Inganta hanyar sauƙaƙa yin kasuwanci a ƙasar domin janyo masu zuba jari ta yadda za a samar da kamfanoni.
Samar da yanayi mai kyau na bunƙasar ƙananan sana'o'i.
Kiwon lafiya
Inganta albashi da kuma yanayin aikin ma'aikatan lafiya.
Samar da inshorar lafiya ga talakawan Najeriya miliyan 133, musamman mata masu ciki, da yara, da tsofaffi da kuma masu lalurar nakasa.
Ƙara wa malaman lafiya ilimi ta hanyar bayar da horo.
Samar da kiwon lafiya mai sauƙi ga kowa.
Tsaro
Kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga da na masu tayar da ƙayar baya.
Haɗa kai da ƙasashen yammaci da na tsakiyar nahiyar Afirka domin inganta tsaro na kan iyaka, musamman ƙasashen Chadi da Jamhuriyar Nijar, da Kamaru.
Haɗa hannu da majalisar dokoki domin samar da jami'an tsaro na cikin al'umma.
Ƙara yawan jami'an soji, da ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro, da samar masu da kayan aiki, da ba su horaswa, da samar masu da kuɗaɗe ta yadda za su iya magance barazanar tsaro.
Ilimi
Zuba jari a ɓangaren koyar da sana'o'i, da wasannin motsa jiki, da horaswa kan ilimin fasahar zamani daga makarantun firamare zuwa sakandare.
Tsarin ilimi wanda 'ba za a bar kowane yaro a baya ba'
Samar da tsarin biyan harajin kamfanoni ta hanyar kula da makarantu mallakin gwamnati, samar da tsarin karatu da kula da ayyukansu.
Ware kashi 14% na kasafin kuɗi ga ɓangaren ilimi.
Cin hanci da rashawa
Yin biyayya ga dokoki na tsarin kuɗi.
Binciken harkokin kuɗi na kowane fallen gwamnati a kai-a kai
Toshe duk wasu hanyoyin zurarewar kuɗi da kawo ƙarshen tallafin man fetur.
Tafiyar da lamurran gwamnati a bayyane.
New Nigeria Peoples Party
Manyan muradu
Samar da ayyukan yi ta hanyar bunƙasa noma.
Magance matsalar tsao.
Martaba doka da bin ƙa'ida.
Tattalin arziki
Yaƙi da rashawa a ma'aikatu da hukumomin gwamnati domin bunƙasa kuɗaɗen shiga.
Kawo sauyi a kasuwar hannayen jari ta ƙasar domin inganta ta ta yadda za ta zamo hanyar samun kuɗaɗen kasuwanci.
Neman ingantacciyar hanyar tafiyar da kasuwar musayar kuɗi.
Aikin yi
Zaftare yawan marasa aikin yi.
Ƙarfafa wa matasa gwiwa domin shiga harkar noma.
Ƙarfafa wa ɓangaren ƴan kasuwa gwiwa domin su kafa kamfanonin sarrafa amfanin gona domin samar da aikin yi ga matasa.
Kiwon lafiya
Kawo sauyi a shirin inshorar lafiya na ƙasa.
Rage yawan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje domin neman lafiya, ta hanyar bunƙasa asibitoci, da bunƙasa yadda ake gudanar da aiki, da bayar da horo ga ma'aikatan lafiya.
Samar da ƙarin kuɗi ga ɓangaren kiwon lafiya a cikin kasafin kuɗi.
Tsaro
Samar da isassun kayan aiki da tattara bayanan sirri domin magance matsalar tsaro.
Bunƙasa fahimtar juna da yafiya a tsakanin al'umma.
Yi wa al'umma cikakken bayani kan ayyukan gwamnati.
Ilimi
Samar da isassun kuɗi ga ɓangaren ilimi.
Bunƙasa manyan makarantu kafin samar da sabbi.
Tallafa wa ƙananan hukumomi domin su iya samar da muhalli ga yara sama da miliyan 20 waɗanda ba su zuwa makaranta kuma suke yawo kan titi.
Cin hanci da rashawa
Sauyawa da ƙarfafa hukumomin yaƙi da rashawa.
Tafiyar da ayyukan gwamnati cikin adalci.
Amfani da fasahar zamani domin daƙile ayyukan rashawa.
Peoples Democratic Party
Manyan muradu
Bai wa masana'antu masu zaman kansu fifiko wurin haɓɓaka tattalin arziki.
Ƙara haɗa kan ƴan ƙasa ta hanyar yin raba-dai-dai tsakanin yankunan ƙasar a wurin bayar da muƙamai.
Sauya fasalin gwamnatin Najeriya
Tattalin arziki
Tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da zama giwar Afrika da tabbatar da cewa ma'aunin GDP ya ruɓanya zuwa $5,000 zuwa 2030.
Haɓɓaka zuba jari ta ɓangaren ababen more rayuwa zuwa kaso 50 na ma'aunin GDP zuwa 2027, kaso 70 kuma zuwa 2023.
Ƙara yawan man fetur ɗin da ake tacewa zuwa ganga miliyan biyu a rana zuwa 2027.
Aikin yi
Samar da ayyukan yi miliyan uku da tsamo mutum miliyan goma daga talauci a duk shekara.
Ƙaddamar da shiri na musamman ingantacce mai rahusa kuma mai dorewa domin samar da aikin yi da kuma sana'o'i.
Samar da wuraren horaswa ga matsakaita da manyan masu sana'o'i.
Kiwon lafiya
Ƙara hanzarta shirin Najeriya na samar da ingantaccen kiwon lafiya kuma mai sauƙi zuwa 2030.
Jawo hankalin likitocin Najeriya da ke ƙasashen waje su dawo gida.
Ƙarfafa gwiwar matsakaita da manyan kamfanonin samar da magunguna da su ƙara adadin magungunan da suke samarwa na cikin gida da ake nema.
Tsaro
Haɓɓaka rajistar haihuwa domin rage aikata laifuka da kuma kare ƴan Najeriya.
Ɗaukar jami'an ƴan sanda miliyan ɗaya domin cimma muradun MDD na kowane mutum 450 ɗan sanda 1.
Ƙara yauƙaƙa dangantaka tsakanin farar hula da sojoji.
Sauya fasalin cibiyoyin tsaro.
Ilimi
Ƙara haɓɓaka karatun kimiyya da fasaha domin samar da dabaru ga sabon tattalin arziki.
Samar da wata hukuma wadda za ta sa ido kan manyan makarantu.
Ƙara zuba jari ta ɓangaren ababen more rayuwa na gwamnatin tarayya da kuma jihohi.
Cin hanci da rashawa
Sake bitar tsarin saka wa ma'aikatan gwamnati masu ƙwazo.
Zamanantar da ayyukan gwamnati domin gano cin hanci.
Tabbatar da cewa hukumomin da suka dace sun aiwatar da hukunci da ake yankewa kan laifukan rashawa.
End of Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam'iyyu suka yi muku
Jama'ar da suka taru a dandalin Tafawa Balewa, sun yi kama da waɗanda suka taru a dandalin Lekki lokacin zanga-zangar EndSars a shekarar 2020, wadda waɗanda suka taru suka nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda sannan zanga-zangar ta rikiɗe zuwa ta neman ingantaccen shugabanci a ƙasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Afirka.
Su matasa ne, masu ƙwarin gwiwa kuma da yawa suna da wadata, suna rike da sabbin wayoyi kirar iPhone da sanye da takalma masu tsada tare da huda hanci, duk da yake ba a keɓance tallafinsa ga matsakaitan mutane ba.
Da yawa ba a haifesu ba lokacin da mista Tinubu da wasu suka yi faɗa da gwamnatin soja ta Sani Abacha a shekarun 1990, ko kuma jarirai ne lokacin da yake gwamna tsakanin 1999-2007.
Amma ba su da lokaci don tabbatar da ƙwarewarsa a bangaren dimokraɗiyya, suna wakiltar jajircewar sabbin matasan Najeriya waɗanda ake ganin cewa tsofaffin 'yan siyasar da ke tafiyar da mulkin ƙasar sun yi abin da za su iya don haka su bayar da wuri ga sabbin jini.
Asalin hoton, Nduka Orjinmo/ BBC
Bayanan hoto, Yawancin magoya bayan Peter Obi sun kasance matasa masu kwarin gwiwa da kuma ke da rufin asiri
Sun kasance basa biyayya ga kowa, ba sa son hannu daga jihar ko ayyukan masu shara a titi da masu kula da zirga-zirga da kula da wuraren shakatawa ta inda mista Tinubu ya ɗauki dubban mutane aiki a Legas.
Suna abokantaka ne da 'yan kasuwa matasa masu sana'ar fasahar zamani a birnin, kuma sun san irin ɗimbin damarmaki da Legas za ta iya bayarwa, amma kuma da alama sun fuskanci cin zarafin 'yan sanda da ganin yajin aikin da ya katse karatunsu na jami'a, sannan kuma yanayin hauhawar farashin kayayyaki na shafarsu matuka.
"Na kasance ina hutu a Turai duk lokacin bazara kafin APC ta hau mulki," in ji wani mutum da ya zo wurin taron ɗauke da dubban huluna, da ke da alamar jam'iyyar Labour.
Duk da kasancewarsa a baya da babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ana kallon mista Obi a matsayin bare idan aka kwatanta da 'yan siyasar da magoya bayansa ke zargi da mayar da Najeriya baya.
Obi mai shekara 61, ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samar da yanayi mai kyau na fitar da kayayyaki, inda kuma ya gina yaƙin neman zaɓensa kan yadda ya tafiyar da kuɗaɗen al'umma lokacin da ya yi mulki sau biyu a matsayin gwamnan jihar Anambra.
Ya gudanar da yakin neman zaɓe, inda ya ziyarci talakawan ƙauye a lunguna da sako da ya shahara da shigowar sa Legas, a lokacin da ya hau buɗaɗɗiyar mota daga wani bangare na birnin, inda ya ji kamar faretin nasara ya yi.
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Magoya bayan APC sun ce Bola Tinubu zai kawo ci gaba a Najeriya kamar yadda ya yi a Legas
Sai dai, a wata alama da ke nuna damuwa gabanin ranar zaben, an kai wa magoya bayansa da dama hari tare da raunata su a kan hanyar zuwa wurin.
Wannan dai wani salo ne da aka taɓa gani a baya, musamman a zaɓukan 2019 , inda aka kawo cikas a wuraren zaɓen da 'yan adawa suka fi karfi a Legas, inda aka hana masu kaɗa kuri'a da dama yin zaɓe.
Yawanci matasa ne 'yan bangar siyasa da ke da karfi a titunan Legas da kuma ake samunsu a tashoshin mota da kasuwanni ke kai irin waɗannan hare-hare.
Mutane da dama basa fatan haduwa da irinsu a Legas, amma suna aiwatar da ayyukan tattara haraji ga ƙananan hukumomi, musamman daga waɗanda ke cikin ɓangaren tattalin arziƙin yau da kullun, kamar masu hawan keke da 'yan kasuwa.
Tun a shekarar 1999, Legas ke bin mista Tinubu kuma duk jam'iyyar da ya zaɓa, tana samun nasara a dukkan zaɓukan jihohi da na tarayya. Sai dai, kuma rata na ta raguwa, inda jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar ke yi wa takara a wannan zaɓe da jam'iyyar Labour ke ƙara samun magoya baya.
Wannan birni ya ga canji da yawa a cikin shekaru da yawa, amma a yanzu yana jin kamar za a yi fito-na-fito tsakanin tsohon da na sabo. Kuma ta fuskoki da dama, sakamakon zaɓen da ke tafe, zai nuna makomar Najeriya da kuma inda ta dosa a nan gaba.