Zaɓen 2023: Fafutikar lashe ƙuri'un jihar Legas

    • Marubuci, Nduka Orjinmo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
  • An wallafa

A yayin da Najeriya ke shirin gudanar da babban zaɓe a ranar 25 ga watan Fabrairu, Legas babban birnin kasuwancin ƙasar ya kasance jihar da ke da ɗumbin masu zaɓe da kuma za su iya tsara makomar ƙasar.

Legas da ta kasance mai yawan masu kaɗa kuri'a - kusan miliyan bakwai - ta zama wata muhimmiyar fagen daga a fafatawar da kowanne bangare ke samun goyon bayan matasa, da akasari suka fito daga gidajen da basu da abin a zo a gani da suka kasa samun aikin yi.

Jimoh Adesina, mai shekaru 40, direba ne a Legas, wanda ke goyon bayan Bola Tinubu, na jam'iyyar APC mai mulki, ya ce "Ya samar da ayyukan yi a baya kuma zai sake yin hakan."

Duk da yake tukin motar bas aiki ne mai kyau, ba aiki ne da mai matakin karatun digiri a kwalejin kimiyyar fasaha zai yi tsammanin yi ba, amma Mista Adesina ya yi farin ciki da kasancewa cikin aiki.

Rashin aikin yi da tattalin arziki sune manyan abubuwan da ke damun masu kaɗa kuri'a a zaɓen. Duk da kasancewarta ƙasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki da samar da mai a nahiyar Afirka, huɗu daga cikin mutum 10 na 'yan Najeriya na rayuwa a kasa da kangin talauci, a cewar bankin duniya.

Mista Tinubu ya ta'allaka yakin neman zaɓensa a kan irin ayyukan da ya yi lokacin da yake gwamnan jihar Legas, da kuma nasarorin da jam'iyyar da ya taimaka wajen kawo wa kan karagar mulki a 2015 ta samu. An fi ganin hakan a tsarin sufuri na motocin bas da ya kawo a Legas na BRT wanda ya sauƙaƙa cunkoson ababen hawa a birnin.

Tashar mota ta zamani ta bas ta maye gurbin al'amuran da suka tada hankula a babban wurin Oshodi, yayin da ake ci gaba da gudanar da gwajin sabon layin dogo na lantarki wanda ya wuce wani gidan wasan kwaikwayo na ƙasa da aka gyara.

A ɗaya gefen teku, akwai wani sabon layin dogo na ƙasa wanda ya haɗa Legas da birnin Ibadan ta tasha a Abeokuta, da kuma wata gada mai matukar muhimmanci a yanzu da ta kai kan babbar kasuwa ta Lekki Peninsula, inda matasa 'yan Najeriya masu kere-kere ke rayuwa cikin wasu gidaje.

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, yana gina matatar mai a wani yanki mai ciniki maras shinge na gwamnati, kusa da wata sabuwar tashar jiragen ruwa da ta fara aiki wanda China ta gina, ana kuma magana kan wata gada ta huɗu da za ta haɗe babban yankin masu aikin yi da sauran yankunan kasuwanci da ke tsibirin Legas.

Duka waɗannan sun canza Legas daga yanayin da take ciki kafin 1999.

Mista Tinubu ne ya kirkiro da yawancin wurare na zamani a Legas ko kuma waɗanda suke mara masa baya da suka gaje shi tun 2007 , ciki har da wani sabon birni na alfarma da ke gaɓar tekun Atlantika.

"Shi ne mahaifina," in ji Mista Adesina, wanda rayuwarsa ta haɗe da mutumin da ya ce ya biya masa kuɗin jarrabawa da na wasu a makarantun gwamnati a shekarar 2001, ya kuma ba shi wannan aiki a matsayin direba.

Yana ɗaya daga cikin mutane da dama a faɗin Najeriya waɗanda alherin mista Tinubu ya taɓa rayuwarsu, ta hanyar dukiyarsa ko albarkatun jihar. A cikin jerin sunayen sun haɗa da taurarin kwallon kafa da mawaƙa da 'yan siyasa da ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓensu da kuma 'yan kasuwa da ya ceto lokacin da suke kangin wahala.

Shi ya sa ya saka taken na zaɓensa mai suna Emi Lokan, wanda ke nufin Yanzu lokacina ne, a takaice kira ne na neman a biya masa bukatunsa ta hanyar goyon bayan takararsa ta shugaban ƙasa.

Yanzu mai naɗa sarki, yana son ya zama sarki.

Duk da cewa jam'iyyarsa ta rasa irin goyon baya da ya samu bayan mulki na tsawon shekara takwas, sai dai, irin wasu ayyuka da take yi a wasu sassan ƙasar yana cikin abubuwan da ke bai wa mista Tinubu ƙwarin gwiwar ganin ya zagaya zuwa dukkan jihohi da ke faɗin Najeriya.

"Waɗanda ya haɗu da su, a yanzu sun canza matuka, yana kyautata rayuwar mutanen ta kowacce hanya,'' in ji Adekanye Adetutu, wani mai goyon bayan Tinubu, wanda ya ce shi ya biya masa kuɗin makaranta lokacin da yake makarantar sakandare.

Sai dai, 'yan adawa sun ce Tinubu, ya yi amfani da irin wannan alherin wajen kafa tsarin ba da goyon baya don samar da goyon bayan masu aminci da gina daular siyasa da kuma rike dukiyar ƙasa.

"Ya kamata Tinubu ya rabu da mu," in ji Daniella Brodie-Mends, 'yar shekara 25, wacce za ta yi zaɓe a karon farko, a wani tsohon dandalin 'yan mulkin mallaka da ke Legas, inda dubban mutane suka taru domin gangamin karshe na ɗan takarar jam'iyyar Labour, Peter. Obi.

Jama'ar da suka taru a dandalin Tafawa Balewa, sun yi kama da waɗanda suka taru a dandalin Lekki lokacin zanga-zangar EndSars a shekarar 2020, wadda waɗanda suka taru suka nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda sannan zanga-zangar ta rikiɗe zuwa ta neman ingantaccen shugabanci a ƙasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Afirka.

Su matasa ne, masu ƙwarin gwiwa kuma da yawa suna da wadata, suna rike da sabbin wayoyi kirar iPhone da sanye da takalma masu tsada tare da huda hanci, duk da yake ba a keɓance tallafinsa ga matsakaitan mutane ba.

Da yawa ba a haifesu ba lokacin da mista Tinubu da wasu suka yi faɗa da gwamnatin soja ta Sani Abacha a shekarun 1990, ko kuma jarirai ne lokacin da yake gwamna tsakanin 1999-2007.

Amma ba su da lokaci don tabbatar da ƙwarewarsa a bangaren dimokraɗiyya, suna wakiltar jajircewar sabbin matasan Najeriya waɗanda ake ganin cewa tsofaffin 'yan siyasar da ke tafiyar da mulkin ƙasar sun yi abin da za su iya don haka su bayar da wuri ga sabbin jini.

Sun kasance basa biyayya ga kowa, ba sa son hannu daga jihar ko ayyukan masu shara a titi da masu kula da zirga-zirga da kula da wuraren shakatawa ta inda mista Tinubu ya ɗauki dubban mutane aiki a Legas.

Suna abokantaka ne da 'yan kasuwa matasa masu sana'ar fasahar zamani a birnin, kuma sun san irin ɗimbin damarmaki da Legas za ta iya bayarwa, amma kuma da alama sun fuskanci cin zarafin 'yan sanda da ganin yajin aikin da ya katse karatunsu na jami'a, sannan kuma yanayin hauhawar farashin kayayyaki na shafarsu matuka.

"Na kasance ina hutu a Turai duk lokacin bazara kafin APC ta hau mulki," in ji wani mutum da ya zo wurin taron ɗauke da dubban huluna, da ke da alamar jam'iyyar Labour.

Duk da kasancewarsa a baya da babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ana kallon mista Obi a matsayin bare idan aka kwatanta da 'yan siyasar da magoya bayansa ke zargi da mayar da Najeriya baya.

Obi mai shekara 61, ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samar da yanayi mai kyau na fitar da kayayyaki, inda kuma ya gina yaƙin neman zaɓensa kan yadda ya tafiyar da kuɗaɗen al'umma lokacin da ya yi mulki sau biyu a matsayin gwamnan jihar Anambra.

Ya gudanar da yakin neman zaɓe, inda ya ziyarci talakawan ƙauye a lunguna da sako da ya shahara da shigowar sa Legas, a lokacin da ya hau buɗaɗɗiyar mota daga wani bangare na birnin, inda ya ji kamar faretin nasara ya yi.

Sai dai, a wata alama da ke nuna damuwa gabanin ranar zaben, an kai wa magoya bayansa da dama hari tare da raunata su a kan hanyar zuwa wurin.

Wannan dai wani salo ne da aka taɓa gani a baya, musamman a zaɓukan 2019 , inda aka kawo cikas a wuraren zaɓen da 'yan adawa suka fi karfi a Legas, inda aka hana masu kaɗa kuri'a da dama yin zaɓe.

Yawanci matasa ne 'yan bangar siyasa da ke da karfi a titunan Legas da kuma ake samunsu a tashoshin mota da kasuwanni ke kai irin waɗannan hare-hare.

Mutane da dama basa fatan haduwa da irinsu a Legas, amma suna aiwatar da ayyukan tattara haraji ga ƙananan hukumomi, musamman daga waɗanda ke cikin ɓangaren tattalin arziƙin yau da kullun, kamar masu hawan keke da 'yan kasuwa.

Tun a shekarar 1999, Legas ke bin mista Tinubu kuma duk jam'iyyar da ya zaɓa, tana samun nasara a dukkan zaɓukan jihohi da na tarayya. Sai dai, kuma rata na ta raguwa, inda jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar ke yi wa takara a wannan zaɓe da jam'iyyar Labour ke ƙara samun magoya baya.

Wannan birni ya ga canji da yawa a cikin shekaru da yawa, amma a yanzu yana jin kamar za a yi fito-na-fito tsakanin tsohon da na sabo. Kuma ta fuskoki da dama, sakamakon zaɓen da ke tafe, zai nuna makomar Najeriya da kuma inda ta dosa a nan gaba.