Gwamnatin Pakistan ta bukaci jama'a su rage yawan shan shayi

Shayi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pakistan ce kasar da tafi sayen ganyen shayi daga waje a duk duniya
An wallafa

Pakistan ta bukaci jama'ar kasar da su rage yawan shayin da suke sha domin su taimaka wa gwamnati rage yawan kudin da take kashewa wajen sayo ganyen shayi daga waje.

Wani babban minista Ahsan Iqbal, wanda ya yi kiran ya ce gwamnati na ciyo bashin kudi domin ta sayo ganyen shayin, wanda abu ne da mutane ke so sosai.

Kuma idan har jama'a za su rage yawan shayin da suke sha da kofi daya ko biyu a rana, hakan zai taimaka wa tattalin arzikin kasar.

Wannan batu na shan shayi ya fito da matsalar tattalin arziki da Pakistan ke ciki a yanzu, fili.

Kasar ta kasance wadda ta fi kowace kasa a duniya sayen ganyen shayi daga waje, inda a bara kadai ta kashe sama da dala miliyan 600 wajen sayo ganyen shayi.

Kiran da ministan ya yi na a rage yawan shayin da ake sha, ya bazu sosai a shafukan intanet, inda 'yan kasar ta Pakistan da dama ke mayar masa da martani da cewa, rage yawan shayin da ake sha ba zai magance matsalar tattalin arzikin kasar ba.

Ministan ya kuma bayar da shawara ga 'yan kasuwa da su rika rufe shagunansu da karfe takwas da rabi na dare, domin rage yawan wutar lantarkin da suke amfani da ita.

Karin yawan kudaden da Pakistan ke kashewa wajen sayo kaya daga waje ya jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki da ke bukatar gaggauta daukar mataki.

Yawan kudin ajiyarta na waje na ko-ta-kwana ya ragu daga kusan dala miliyan dubu 16 a watan Fabrairu zuwa kusan kasa da dala miliyan dubu goma a watan farko na watan nan na Yuni.

Wanda hakan kusan ba lalle ya ishe ta sayo kayayyakin da take bukata ba daga waje tsawon wata biyu.

Tuni daman gwamnati ta takaita sayo kayayyakin kawa wadanda ba su zama dole ba, domin daidaita tattalin arzikin.

Matsalar tattalin arzikin babban kalubale ne ga gwamnatin Shehbaz Sharif, wanda ya maye gurbin Imran Khan a matsayin firaminista a majalisa bayan da majalisa ta kada kuri'ar waje da tsohuwar gwamnatin a watan Afrilu.

Jim kadan da rantsar da shi, Mista Sharif ya zargi gwamnatin Imran Khan mai barin-gado a lokacin da laifin bannata tattalin arzikin.

Kuma ya ce ba karamin aiki ba ne, dawo da tattalin arzikin kan turba.

A makon da ya gabata gwamnatinsa ta bude sabon kasafin kudi na dala miliyan dubu 47, da nufin shawo kan Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF, domin samun damar dawo da wani shirin ceto tattalin arzikin na dala miliyan dubu shida da Asusun ya dakatar.

A shekara ta 2019 kasar ta kulla yarjejeniya da asusun na IMF, domin sassauta wata matsalar ta tattalin arziki wadda kasar ta samu kanta a ciki a sakamakon rashin isassun kudade a asusunta na waje na ko-ta-kwana, da kuma rashin cigaba tsawon shekaru.