Pakistan: Dusar ƙankara ta yi sanadin mutuwar mutane cikin motocinsu

Bayanan bidiyo, Bidiyo: motoci 1,000 ne suka maƙale a garin Murree na Pakistan
An wallafa

A arewacin Pakistan, aƙalla mutum 21 ne suka rasa rayukansu bayan da dusar ƙankara mai yawa ta rutsa da su a cikin motocinsu yayin da suke ƙoƙarin kai wa gidajensu.

Kimanin motoci 1,000 ne suka maƙale yayin da mutanen - wadanda masu yawon bude idanu ne - suke rububin isa wani wurin da ruwa ke kwarara daga saman dutse a garin Murree.

Wani jami'ain dan sanda da matarsa da ƴaƴansu shida, tare da wasu mutanen gida guda su biyar na cikin wadanda suka halaka, kamar yadda masu ceto na yankin wato 1122 suka sanar.

Sojojin kasar sun ce sun ceto fiye da mutum 300 wadanda dusar kankarar ta rutsa da su.

Ministan harkokin cikin gida na Pakistan Sheikh Rashid ya ce tashin hankalin ya biyo bayan cunkoson motocin matafiya da aka samu ne a yankin da ke arewa da birnin Islamabad. Fiye da motoci 100,000 ne suka isa tsohon garin cikin kwanakin da suka gabata, har ta kai ga ana raba hotunan yadda jama'a ke shakatawa a wurin cikin dusar kankara.

Sai dai zuwa ranar Juma'a kafofin yada labaraia yankin sun fara fitar da rahotanni cewa masu yawon bude idanun sun fara makalewa. Lamarin ya kai tilas hukumomin yankin sun ayyana dokar ta baci zuwa ranar Asabar.

Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda motoci suka matse da juna gaba da baya, ga dusar kankara ta rufe su.

Rescue workers help people escape from their cars

Asalin hoton, Getty Images

Usman Abbasi, wani mai yawon bude idanu wanda dusar kankarar ta rutsa da shi a wani garin da ke yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta wayar tarho cewa, "Mutane na cikin hali na bala'i".

Mazauna yankin sun rika kai taimakon barguna da abinci ga wadanda dusar kankarar ta rutsa da su. Garin na saman wani dutse ne mai nisan mita 2,300 daga lebur din teku.

Gwamnatin yankin ta fara kai mutane cikin makarantu da gine-ginen gwamnati.

Firaministan Pakistan Imran Khan ya bayyana tashin hankalin da ya shiga bisa rasa rayukan da aka yi na masu yawon bude idanun.

Ya "bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike da kuma samar da matakan da za su hana irin wannan bala'in sake aukuwa."

Birtaniya ce dai ta gina garin Murree shekaru kusan 200 da suka gabata a matsayin sansanin sojojinta na mulkin mallaka.