Gomman mutane sun halaka a hare-haren Tigray

Relatives of Togoga residents wait for information about their loved ones outside Aider hospital in Mekelle, Ethiopia. Photo: 23 June 2021

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan uwan wadanda su ka jikkata sun shiga damuwa, inda su ke jiran labarin halin da s ke ciki
An wallafa

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin Habasha ta gudanar da bincike kan hare-hare ta sama da aka kai wata kasuwa da ke yankin Tigray na kasar.

Gomman mutane ne suka mutu a harin da aka kai garin Togoga, an kuma hana motocin daukar marasa lafiya shiga garin domin daukar wadanda suka jikkata.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta samu kai wasu marasa lafiya asibiti, tare da kiran a mutunta ayyukan jin kai na taimakon marasa lafiya a yankin.

Gwamnatin kasar Habasha ta musanta kai harin kan farar hula, tare da ikirarin an kai su ne kan masu tada kayar baya.

A man who was injured in Ethiopia's reported air strike is treated at Aider hospital in Mekelle, Ethiopia. Photo: 23 June 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fiye da mutum 40 ne su ka jikkata a hare-haren

Watanni takwas ke nan da gwamnati ke yaki da masu tada kayar baya a yankin, inda rahotanni ke cewa cikin kwanakin da suka gabata masu tada kayar bayan sun yi nasara kan dakarun Habasha.

A bangare guda majalisar Dinkin Duniya ta kara kiran a gaggauta bude bincike mai zaman kan sa domin hukunta masu hannu a aharin na kasuwar Togoga.