An ƙirƙiri tsarin sa ido don tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon - Iran
Mai magana da yawun tawagar Iran da ke cikin tattaunawar Amurka da ƙasar, Esmail Baqaei, ya bayyana cewa an tsara wani tsari na musamman domin sa ido kan tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon.
Ya ce wannan tsari yana daga cikin muhimman abubuwan da aka cimma a tattaunawar da ake yi a Switzerland.
Baqaei ya ce an samar da tsarin ne tare da haɗin gwiwar ƙasashen Qatar da Pakistan da ke shiga tsakani, domin tabbatar da cewa an kawo ƙarshen yaƙin a Lebanon.
Ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da an ci gaba da kiyaye zaman lafiya a yankin.
Ya ƙara da cewa bisa tanadin sashe na farko na yarjejeniyar, wajibi ne a dakatar da yaƙi da duk wani aikin soja a dukkan wurare, ciki har da Lebanon.
A cewarsa, kafa wannan tsarin na nuni da cewa ana son tabbatar da tsagaita wutar ya ɗore ba tare da tangarɗa ba.
Haka kuma, Baqaei ya ce an samu ci gaba mai kyau dangane da alƙawarin Amurka na sakin wasu kadarorin Iran da aka ƙwace a baya, wanda yake daga cikin manyan batutuwan tattaunawar.





