Rikicin Tigray: Babban bala'in yunwa da mutane suka haddasa da hannayensu a Ethiopia

Wata karamar yarinya 'yar gudun hijira a Yammacin Tigray na jiran lokacin raba abinci a wajen wani aji a makarantar da aka tsugunar da su a birnin Mekele na yankin Tigray ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2021.

Asalin hoton, AFP

    • Marubuci, Daga Alex de Waal
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai sharhi kan Afirka
  • An wallafa

"Ana fama da fari a yanzu a Tigray." Babban jami'in tsare-tsare mai lura da agajin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Mark Lowcock ya bayyana wadannan kalamai kan halin da ake ciki a arewacin kasar Ethiopia ranar Alhamis.

Kalaman nasa - a wani zaman tattaunawa gabanin babban taron manyan kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki na G7 - sun haifar da daukar matakan amfani da sashen ma'aunin gwajin yanayin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya na IPC.

A wani rahoto, IPC din ya kididdige cewa mutum 353,000 ne a yankin Tigray ke kan mataki na biyar na aukuwar babban bala'in sannan karin wasu kusan miliyan 1.769 ne ke kan mataki na hudu na neman daukin gaggawa.

Hakan ya nuna cewa an fada cikin "matsananciyar yunwa".

Ma'aunin na IPC bai yi amfani da wannan kalma ba saboda yadda take da karfi a siyasance - kuma gwamnatin Ethiopia ka iya nuna adawa da hakan.

Mutuwa ta hanya mafi muni

A tattare da wadannan alkaluma, akwai mummunan al'amari na bakin ciki da ya shafi dan Adam.

Mazauna yankin Tigray sun bayar da labarin kauyuka masu nisa inda aka gano gawarwakin mutane da safe, bayan sun rasa rayukansu a cikin dare.

Matan da sojoji suka sace suka rike su a matsayin bayin da ake lalata da su, ana lura da su a asibitoci da gidaje masu kwanciyar hankali, na cikin halin dimauta daga raba su da 'yayansu da aka yi, da me yiwuwa suna cikin halin matsananciyar yunwa saboda babu kulawar iyayensu mata.

Wata motar sojojin da ta aka kona a gefen hanya a arewacin birnin Mekele, na yankin Tigray ranar 26 ga watan Fabrairun shekarar 2021.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yaki a Tigray ya barke a cikin watan Nuwamba

Rashin abinci hanya ce mafi muni ta mutuwa, bayan jikin dan Adam da ke cike da yunwa ya cinye kayan cikinsa don samun isasshen kuzarin ci gaba da rayuwa.

Wadanda suke fara gazawa su ne kananan yara - akasari biyu bisa ukun wadanda ke mutuwa a lokacin ja'ibar yunwar.

A bisa la'akari da alkaluma daga yankin Tigray, a bayyane take cewa ana fargabar mutuwar kananan yara 300,000 - daidai da rabin adadin yawan kananan yaran da ba su kai shekarun fara makaranta ba a birnin Landan.

Za a iya cewa wadannan alkaluma sun ma wuce yadda ake tsammani. Tawagar masu bincike ba ta iya kai wa ga duka yankunan ba, don haka ta dogara ne kawai ga kwatantawa da irin bayanai kadan da ta tattara daga takaitattun yankuna.

Kamar yadda masu bincike suka wallafa a taswirar agajin jin-kai a Jami'ar Ghent ta kasar Belgium, cikin mutane miliyan shida na yankin Tigray:

  • Daya -bisa-uku ne ke zaune a yankunan da gwamnatin Ethiopia ke rike da iko
  • Wani kashi ukun na zaune ne a yankunan da sojojin kasar Eritrea ne suka mamaye, wanda aminan sojojin Ethiopia ne, da ba sa bai wa kungiyoyin bayar da agaji hadin kai
  • Wasu karin mutane miliyan daya da rabi na zaune a yankunan karkara da 'yan tawayen Tigraya ke rike da iko, inda ma'aikatan agaji ba za su iya shiga ba kana inda aka yanke hanyoyin sadarwa na wayar salula.

Gwamnati ta bayyana cewa yanzu dakarun 'yan tawaye na Tigray "kalilan" ne suka rage, kuma ta yi alwashin ba da jimawa ba za ta karbe daukacin ikon yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa halin da ake cik mzai kara muni - abin tambayar kuma shi ne ya ake ciki da kuma yaushe ne.

Mutanen Tigray sun gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati kan yanayin rarraba tallafin abinci da kuma halin da ake ciki a yankin Tigray cewa wadanda suka rasa matsugunasu na zaune a makarantar sakandare ta Hawelti a birnin Mekele na Tigray ranar 8 ga watan Maris shekarar 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rikicin a Tigray ya tilsata wa dubban daruruwan mutane barin gidajensu

Rahoton na IPC ya hada da batun cewa "wannan rahoton bi samu amincewar gwamnatin Ethiopia ba". Wannan wani gargadi ne.

Me yiwuwa mahukuntan kaar ta Ethiopia su yi wasti da gargadi game da "yunwa", a kan bayanai a hukumance cewa yanayin ''babban bala'i" ya bazu a yankunan daban-bana na Tigray kana babu ko da wuri daya da adadin mutanen da ke kan mataki na biyar suka kai kashi 20 bisa dari na inda aka iyalan cewa kan ayyana "yunwa".

Huda a cikin duhu

Ma'aikatan agaji sun nuna damuwar cewa yayin da aka fara samun saukar ruwan sama na lokacin bazara a fadin yankin Tigray, ya kamata a ce manoma sun fara gyaran gonaki - amma ba su yi ba.

1px transparent line

Wata tawaga daga Jami'ar Ghent, da ke lura da wasu ayyukan noma a yankin, sun bayyana yadda aka bar manyan filayen noma ara zube a cikin wannan shekarar saboda kananan manoma ba su da iri, da shanun da za su yi huda ko kuma taki.

Mafi muni, sojoji na yi musu barazana: '' Ba za ka iya huda ba, ba za ka yi girbi ba, kuma muddin ka gwada yi za mu hukunta ka.''

A kauyuka masu nisan gaske, manoma kan daurawa shanunsu galma su rika yin huda cikin duhun dare kafin fitowar alfijir, tare da masu sa ido da kan gargade su game da sojoji masu sintiri.

Muddin babu amfanin gona a cikin karshen wannan shekarar, dole ne mazauna yankin na Tigrayan su dogara da tallafi - ko kuma su gamu da matsalar yunwa.

Wannan yunwa ce da dan adam ya haddasa. Babu matsalar fari, kuma a bara dandazon farin dango sun bar yankin.

Yankin yana cikin yankunan ka iyaka da aka bayyana ke da "wadatar abinci", kafin barkewar rikicin tsakanin sojojin 'yan tawaye na Tigray People's Liberation Front (TPLF) - da jami gwamnatin kasar karkashin jagorancin Firaiministaa Abiy Ahmed.

An sace kayan abinci na tallafi

Yakin ya tsayar da harkoki, da rufe bankuna tare da dakatar da manya ayyukan daukin gaggawa na gwamnati.

Yankuna masu albarkar kasar noma na yankin Tigray a mamaye suke da dakaru daga yankin Amhara mai makwabtaia, tare da haramta wa mazauna Tigray din ayyukan noma tare da hana samun damar gudanar da ayyukan kwadago da aka saba yi a duk shekara.

2px presentational grey line

Karin labarai game da rikicin yankin Tigray:

2px presentational grey line

An zargi dakarun Eritrea da suka shiga cikin fadan da yin samame da aikata fashi, kana tare da dakarun Ethiopia suna kone amfanin gona da asibitoci tare da hana manoma gyara filayen noman su.

Majalisar Dinkin Duniya ta kididdige cewa wadanda aka yi wa fyade su kimanin 22,000 na bukata taimako. Tsoron fyade da cin zarafi na nufin mata da 'yanmata sun boye kan su, sun kasa fita neman taimakon abinci.

Kungiyoyin agaji na tafiyar hawainiya wajen daukar matakai, wanda matsalar tsaro da nuna karfin iko daga bangaren gwamnati suka haifar.

Ma'aikatan agajin na bukatar kayan aiki na sadarwa domin gudanar da ayyukan nasu.

A hukumance, Majalisar Dinkin Duniya ta yi ikirarin cewa raba kayan agajin ya kai ga mutane miliyan biyu a dubu dari takwas.

Da dama daga cikin wadannan mutane da suka samu kayan tallafin kamar kilo 30 na garin fulawa - wanda zai ishi iyalai har na tsawon kwanaki 10. Wadanda suka fi takar sa'a sun samu tallafi har sau biyu.

Amma akwai yawan samun rahotannin cewa sojoji na sace tallafin da ake saukewa daga manyan motoci. Wasu mazauna kauyukan su bayar da rahoton cewa dakarun Eritrea kan bullo da zarar an gama rarraba kayan tallafin su kwashe kayan abincin.

Wata kididdiga mai zaman kan ta ta bayyana cewa kashi 13 bisa dari na mutane miliyan biyar da dubu dari biyu kacal ne ke bukatar tallafin.

Wata 'yar gudun hijira da wani karamin yaro daga Yammacin Tigray a wajen wani aji a makarantar da aka tsugunar da su a Makele babban birnin Tigray ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2021.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Akwai fargabar cewa kananan yara za su kare rayuwarsu a matsayin 'yan gudun hijira

An hallaka ma'aikatan agaji - na baya bayan nan a ranar 28 ga watan Mayu. Dakarun kasar Ethiopia na yawan toshe hanyoyin da masu kai kayan agaji ke bi don kai wa ga kauyuka masu nisa, tare da zarginsu da tallafa wa 'ya tawaye.

Jami'an gwamnati a yankin sun yi zargin cewa duka bangarorin biyu masu fada da juna na da hannu wajen sace kayan abinci na tallafin.

Amma kuma, Majalisar Dinkin Dunia ta bayar da rahoton abubuwa 129 da suka faru na "hada damar wucewa da kayan tallafin" daga bangaren dakarun gwamnatin Ethiopia da na Eritrea, kana 'yan tawayen sun hana shiga da kayan tallafin a watan da ya gabata - matsala daya daga bangaren dakarun yankin Tigray.

Rokon kan a tsagaita wuta

Akwai kuma yarjejeniya kan abubuwan da suka kamata a yi wajen rage kaifin mummunan al'amarin - yanzu ta kai makurar da ba za a iya hanawa ba.

Abu na farko a jerin matakan shi ne wanda Jan Egeland, shugaban hukumar lura da 'yan gudun hijira ta kasar Norway ya yi wa lakabi da "tsgaita wutar kiyaye abkuwar ja'ibar yunwa".

Dakarun Ethiopia na sintiri a birnin Mekelle na yankin Tigray a arewacin Ethiopia ranar 7 ga watan Maris shekarar 2021 bayan kwace birnin taga hannin dakarun (TPLF)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dakarun kasar Ethiopian lokacin da suka kawace ikon yankin Makele babban birnin yankin Tigray a farkon rikicin cikin watan Nuwamba

Wannan sun hada da kawo karshen rashin jituwar, da kare rayukan fararen hula dake cikin barazanar cin zarfi da suka hada da fyade da kuma damar samun agajin jinkai da babu shamaki.

A makon jiya ne, mai magana da yawun gwamnatin kasar Ethiopia ya jaddada ayyukan sojin da ke kan hanya zai kai ga samun galaba - tare da ajiye batun tsagaita wuta a gefe.

Yayin da yake mayar da martani game da kiran da Amurka ke yi na janyewar kasar Eritrea, ministan harkokin wajen Eritrea ya zargi gwamnatin Biden da "kara iza wutar rikicin da haddasa rudani".

A ranar Talata ne dakarun 'yan tawayen Tigray TPLF suka ce suna maraba da tallafin kuma a shirye suke su raba su - amma ba su ambaci batun tsagaita wuta ba.

'Kada ku jira sai kun fara kirga kaburbura'

Kungiyoyin bayar da agaji sun samo wata hanya ta yin aiki a yankuna da ke fama da rikici - amma suna bukatar hadin kan duka bangarorin biyu masu fada da juna.

Babu alamar hakan daga bangaren gwamnatin Ethiopia da suke cigaba da jaddada cewa 'yan tawayen '''yan ta'adda ne'' don haka babu zancen hadin kai a tsakaninsu ko da kuwa a lokacin ceton rayuka ne.

Ayyukan agajin jinkai na karuwa sosai a yankin Tigray, amma har yanzu akwai tafiyar hawainiya wajen kawo sauyi.

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya na da manyan wurare biyu ne kacal na rarraba kayan tallafin a daukacin yankin, kana an lalata akasarin gine-gine.

Wani danuwan Arsema Berha, mai shekaru 9, na mayar da ita kan gado a asibitin Ayder Makele babban birnin Tigray ranar 25 ga watan Fabrairu shekaarar 2021, bayan samun raunuka a lokacin rikici tsakanin sojoji 'yan tawayen Tigray da na gwamnatin Ethiopia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane da dama na fafutikar samun agajin kiwon lafiya a Tigray

Ana bukatar karin wasu hanyoyin. Amurka ta sanar da karin tallafin dala miliyan dari da tamanin da daya ($181m) kwatankwacin fan miliyan dari da ashirin da daya (£128m) , tare da nuni da cewa tana fatan sauran masu bayar da tallafi za su fito taimaka.

Yanzu haka, matsalar samar da abinci na kara ta'azzara a yankunan Amhara da Afar masu makwabtaka, yayin da fadan da ake gwabzawa ke kara bazuwa a kasar tare da haifar da koma bayan tattalin arziki da samun ababen tafiyar da rayuwa na jama'a da karuwar talauci.

Akwai kuma gargadin karuwar bukatar abinci a kasar Sudan.

Abinda aka gaza samu shi ne daukar matakai daga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. A shekaru uku da suka gabata ne aka amince da dokar 2417 da ta safi yaki da kuma yunwa tare da yin la'akari da rikici mai kama da irin wannan.

Watanni bakwai bayan barkewar yakin -babu wani taro ko guda daya da Kwamitin Sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar kan abinda yanzu ya zama rikici da ya shafi al'umma mafi muni a duniya.

Dokar ta 2417 ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya damar kafa takunkumi kan duk wani mutum ko kasar da ta hana ayyukan agajin jinkai, tare da gargadin cewa amfani da yunwa a matsayin makamin yaki, aikata babban laifi ne na yaki.

A ciki karshen makon nan akwai yiwuwar shugabannin kasashen G7 za su yi matsin lamba kan kasashen Ethiopia da Eritrea da su bi karbi bukatar da aka gabatar musu na daukar matakan gaggawa kan agajin jinkan.

Wakilin musamman na Amurka Jeff Feldman ya yi gargadin cewa "kada mu jira sai mun fara kirga kaburbura" kafin mu ayyana cewa rikicin da ake yi a yakin Tigray a matsayin yunwar da mutum ya haddasa.

Short presentational grey line

Alex de Waal babban daraktan gidauniyar '' World Peace Foundation'' ne a makarantar nazarin harkokin shari'a da difilomasiyya a Jami'ar Tufts ta Amurka.