Ƙasashen da aka fitar da su daga Gasar Kofin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Zuwa yanzu an fara fitar da tawagar wasanni ƙasashe daga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da ke gudana a Amurka da Mexico da Kanada.
Ƙasashe 48 ne ke fafatawa a gasar, inda kowa ke neman tikitin zuwa zagayen gaba na kifa ɗaya ƙwala ta hanyar samun maki a wasannin rukuni.
Ga jerin ƙasashen da aka cire zuwa yanzu.
Tunisia

Asalin hoton, Getty Images
An cire Tunisia daga gasar ne bayan da Japan ta doke ta da ci 4-0 a wasan da suka buga a Monterrey ranar Lahadi.
Tun da farko Tunisia ta sha kashi da ci 5-1 a hannun Sweden a wasan farko na rukuni na F.
Tun a wasansu na farko ne dai aka kori kocin su Sabri Lamouchi, inda aka naɗa Hervé Renard da tunanin za su ga sauyi.
Sai dai da alama daga nan za su yi bankwana da gasar Kofin Duniya na 2026.
Sakamakon rashin samun ko maki ɗaya a wasanninta biyu na farko ya tabbatar da cewa ba za ta iya kaiwa zagayen ƴan 32 ba, duk da cewa akwai wasa guda ya rage mata a matakin rukuni.
Haiti

Asalin hoton, Getty Images
A rukuni na C kuwa, zakarun duniya sau biyar Brazil sun lallasa Haiti da ci 3-0 a birnin Philadelphia.
Wannan sakamako ya tabbatar da ficewar Haiti daga gasar bayan da ta kasa samun ko maki ɗaya a wasanni biyu.
A wasansu na farko dai Scotland ce ta ci su 1-0.
Ƙasar ce take ƙarshen teburin rukuni da bambancin ƙwallaye, lamarin da ya sa wasanta na ƙarshe da Morocco a ranar 24 ga Yuni zai zama wasan cike gurbi ne kawai.
Turkiya

Asalin hoton, Getty Images
A rukuni na D kuma, Türkiye ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Paraguay a wasan da aka buga a filin wasa na San Francisco Bay Area Stadium.
Shan kashi sau biyu a jere ba tare da samun maki ba, lamarin da ya tabbatar da ficewar ƙasar daga gasar tun kafin ta buga wasanta na ƙarshe a rukuni.
Turkiya ta sha kashi a hannun Australia da ci 2-0 a wasansu na farko.
Wasan da ya rage mata na ƙarshe shi ne wanda za ta fafata da Amurka.









