Gomman mutane sun halaka a hare-haren Tigray

An wallafa

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin Habasha ta gudanar da bincike kan hare-hare ta sama da aka kai wata kasuwa da ke yankin Tigray na kasar.

Gomman mutane ne suka mutu a harin da aka kai garin Togoga, an kuma hana motocin daukar marasa lafiya shiga garin domin daukar wadanda suka jikkata.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta samu kai wasu marasa lafiya asibiti, tare da kiran a mutunta ayyukan jin kai na taimakon marasa lafiya a yankin.

Gwamnatin kasar Habasha ta musanta kai harin kan farar hula, tare da ikirarin an kai su ne kan masu tada kayar baya.

Watanni takwas ke nan da gwamnati ke yaki da masu tada kayar baya a yankin, inda rahotanni ke cewa cikin kwanakin da suka gabata masu tada kayar bayan sun yi nasara kan dakarun Habasha.

A bangare guda majalisar Dinkin Duniya ta kara kiran a gaggauta bude bincike mai zaman kan sa domin hukunta masu hannu a aharin na kasuwar Togoga.