WAEC/BEPC: Ɗage jarabawar kammala sakandare a Nijar ya janyo ce-ce-ku-ce

Iyayen daliban makarantun sakandare a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da bayyana damuwarsu bisa dage ranar yin jarabawar kammala sakandare a faɗin ƙasar.
Ma'aikatar ilimi ta ƙasar ce ta ɗage ranar gudanar da jarabawar BEPC ko kuma WAEC zuwa ranar 6 ga watan gobe a duk faɗin ƙasar.
Gwamnatin ta sanar da hakan a cikin wata takarda da ke dauke da kalmar wasikar gaggawa da ministan ma'aikatar ilimi ta ƙasa ya sakawa hannu.
Tun tsakiyar shekarar karatun bana ne aka saka ranar 22 ga wannan wata na Yuni a matsayin ranar da za a gudanar da jarabawar.
Ɗaya daga cikin iyayen yaran ya bayyana wa BBC cewa matakin ma'aikatar ilimin ya janyo jita-jita matuƙa kuma suna tababa kan lamarin.
"Abun ya sa mun yi ayar tambaya dangane da dage wannan rana kai tsaye, muna daga cikin masu cewa aniyar gwamnati ta daƙile cin hanci da rashawa da ke faruwa a jarrabawar shi yasa gwamnati ta dauki matakin". in ji ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban.
Shi kuwa wani uba cewa ya yi har yanzu hukuma ba ta fito ta yi musu bayani kan dalilanta na sauya ranar jarrabawar ba.
A cewarsa, yana ganin gwamnatin ba za ta dauki irin wannan mataki ba ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba.
Sai dai ya ce watakila an kwarmata tambayoyin jarabawar wanda kuma dole zai sa mahukunta su sake yin duba domin fitar da wasu sabbin amsoshin.










