'Yadda kwararrowar hamada ke tagayyara rayuwarmu'

Kwararar hamada
An wallafa

Yau ake bikin ranar yaƙi da kwararowar hamada da fari don wayar da kan jama'a wajen farfado da rayuwar halittu da kuma rage tasirin sauyin yanayi.

Ba wannan kaɗai ba, ranar ta kunshi jaddada mahimmancin tsirai duk da tasirin da annobar korona ta yi.

Matsalar ta kwararar hamada da kuma fari ta shafi ƙasashe irinsu Nijar sai dai gwamnatin ƙasar ta ce tana ƙoƙarin ƙirƙiro da ayyukan yi a yankunan da fari da hamada ke barazana ta hanyar samar musu da ayyukan gina-ka-ci da ke ba da damar ceto dubban kadada daga zaizayewa.

Wani manomi a ƙasar, Malam Sidi Shu'aibu Sanda ya shaida wa BBC cewa farin ya haifar da koma baya a harka noma.

"Abin da muke shukawa ba ma samun shi - bara na kashe jaka dari shida da wani abu amma abin da na samu bai kai jaka dari uku ba". in ji manomin.

Ya ce a shekarar da ta gabata, ya tafka mummunar asara a harkarsa ta noma saboda karanci da kuma yawaitar ruwa na haifar da matsala ga sana'arsu.

Ita kuwa Rabi Yusufu ta bayyana irin wahalar da suke sha wajen samun itacen yin girki wanda a yanzu ta ce ya yi tsada.

Ta ce a baya, idan suka sayi itace suna morarsa sosai - yin girkin safe da rana har ma da dare amma yanzu ba haka abin yake ba.

Fari

Matsalar kwararar hamada da kuma fari ba iya nan ta tsaya ba, ta kan jefa wasu jama'a ɗin zuwa ci-rani wasu garuruwan Nijar.

Muhammadu Sayyadi mazaunin Jibalan a jihar Tahoua ya bayyana cewa "Muna zuwa Yamai ci-rani kuma idan lokacin ruwa ya yi sai mu koma".

"Kamar lokacin da da yanzu ba daya bane, yanzu ana fuskantar fari, ba a samun ruwa sosai - an fi samu a baya sabanin yanzu". in ji shi.