Afirka Ta Kudu: Ƙauyen da mazaunansa suka ruɗu da neman daiman

A boy holds what he believes to be a diamond after the discovery of unidentified stones at KwaHlathi village near Ladysmith, South Africa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An bayar da rahoton cewa wani makiyayi ne ya fara gano duwatsun a wani sarari
An wallafa

"Ban taba gani ko taɓa lu'u-lu'u ba a rayuwata. Wannan shi ne karon farko da na da na taɓa shi a nan.

Skhumbuzo Mbhele daya daga cikin ɗaruruwan mutane ne da suka yi tururuwa a wani ɗan ƙaramin ƙauye a ƙasar Afirka Ta Kudu, cike da ƙarfin gwiwar fatan samun wani abin alkhairi da mai sauya rayuwa.

Wannan 'tururuwar samun lu'u-lu'u' da ta mamaye yankin KwaHlathi mai nisan kilomita 250 daga arewacin birnin Durban ta ƙaru ne bayan wannan gamo-da-katar na ba-zata fiye da mako guda da ya gabata.

Yayin da gwamnatin lardin ta yi gargadi game da haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, da dama na ganin samun wadannan duwatsu masu daraja wata dama ce da ke zuwa sau daya a iya tsawon rayuwa wajen kauce wa talaucin tsawon rayuwa.

Yaya aka yi aka fara wannan ruguguwa?

An bayar da rahoton cewa wani makiyayi ne ya fara gano duwatsun a wani sarari.

Tun bayan wannan lokacin ne, hotuna da bidiyo suka fara bayyana a shafukan sada zumunta na wasu mutane, suna ikirarin cewa sun gano wasu duwatsu masu kama da lu'u-lu'u.

Wannan ya kara iza daruruwan mutane masu cike da fata daga ƙauyuka da garuruwa makwabta yi wa wannan wuri da ake tunani na kunshe da abubuwa masu daraja tsinke.

Su wanene masu neman wannan babbar sa'a?

A group of women carrying pickaxes

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ɗaruruwan mutane masu cike da fata daga ƙauyuka da garuruwa maƙwabta sun yi wa wannan wuri da ake tunani na ƙunshe da abubuwa masu daraja tsinke

Akasarin masu farautar wadannan duwatsu mata ne da ba su da wata sana'a ko aikin yi, in ji wakiliyar BBC a kasar Afirka Ta Kudu Nomsa Maseko.

"Tun da sanyin safiya lokacin da na isa can, akwai daruruwan mutane a fadin kwarin, akasarin su dauke da gatari da shebur, suna da hakar abinda suke tunanin lu'u-lu'u ne,'' ta ce.

"Akasarin matan da ke nan na kan shafe tsawon dare suna haka, wwasu sanye da rigunan barci saboda sun ce akwai sanyi a cikin dare.''

Velile Vilakazi, daya daga matan a filin hakar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: "Wannan zai taimaka wa matuka al'ummomin.

"Muna fata hakan zai kawo karshen aikata muggan laifuka saboda matasa suna aikata hakan ne saboda rashin aikin yi."

"Ina fata hakan zai kawo sauyi a gida saboda muna fama da wahalhalu, don haka al'amura su daidaita su yi kyau,'' in ji daya mai hakar, Skhumbuzo Mbhele.

Rashin aikin yi a Afirka Ta Kudu yanzu haka ya kai kashi 33 (33%), inda ya karu zuwa kashi 46 bisa dari (46%) a tsakanin mutane masu shekaru daga 15 zuwa 34, kamar yadda kididdigar hukuma ta Afirka Ta Kudu ta bayyana.

Dr Melinda du Toit, wata mai bincike game da halayyar dan adam daga cibiyar kula da cigaban al'umma ta Afirka Ta Kudu a Jami'ar Johannesburg, ta ce wasu masu hakar - akasarin su da ''ba su da komai'' - sun yi amanna cewa wannan ganowar wata kyauta ce daga mahalicci.

"Abin da wasu daga cikin mutanen ke cewa game da lu'u-lu'un - Allah ne ya aiko da shi, ƙasa ce ta samar mana da shi, kuma mun san za mu samu alkhairi.''

Fata ko kuma buri ya cika kenan?

An aerial shot showing a large number of pockmarks in the earth made by the miners

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Samun lu'u-lu'u a cikin wuri mai datti abu ne mai kamar da wuya

Gwamnatin lardin KwaZulu-Natal, ta umarci masu hakar da su bar wurin.

"Mun damu cewa muddin ba a shawo kan wannan ba hakan zai haifar da rikici, me yiwuwa kuma har da turmutsutsu,'' Firimiya Sihle Zikalala ya ce.

Kwararru daga sashen ma'adinai da wutar lantarki na shirin gudanar da bincike kan duwatsun don gano matsayinsu, in ji gwamnati.

Da alamu masu hakar ma'adinan na ba-zata sun haifar da wani fata - Tun da dama Afirka ta Kudu it ace ta hudu mafi girma wajen samar da lu'u-lu'u, kamar yadda wani shafin yanar gizo na geology.com ya wallafa.

It ace kuma inda aka taba samun lu'u-lu'u mafi girma da daraja a duniya - da ake kira ''Cullinan diamond'' - a shekarar 1905.

Amma kuma Dakta Michele Francis, wata mai bincike kan kimiyyar kasa ta Afirka ta Kudu a Jami'ar Stellenbosch ta yi amanna cewa ganowar wannan abu - wanda ke da kama da lu'u-lu'u.

"Samun lu'u-lu'u ba abu ne na ba kasafai ba,'' ta shaida wa BBC.

"Manyan kamfanonin hakar ma'adinai sun kashe kudade da dana wajen neman sabbin ma'adinan. Samun lu'u-lu'u a cikin wuri mai datti abu ne mai kamar da wuya."