Shugaban ƙasar Peru Merino ya yi murabus bayan wata mummunar zanga-zanga

Asalin hoton, Reuters
Shugaban riƙon ƙwaryar Peru ya yi murabus, kwana guda bayan an kashe wasu masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.
Manuel Merino, wanda tsohon kakakin majalisar dokokin ƙasar ne, ya karbi mukamin ne ƙasa da mako guda.
Ya maye gurbin Shugaba Martin Vizcarra, wanda aka tsige daga muƙaminsa a ranar Litinin ɗin da ta gabata saboda zarge-zarge cin hanci da rashawa, abin da ya sha musantawa.
'Yan siyasa sun yi ta kiran Mista Merino ya yi murabus, bayan rikici ya yi ƙamari yayin zanga-zangar adawa da shi.
Ministoci 12 ne da ya naɗa a matsayin muƙarrabansa suka sauka daga muƙamansu a safiyar ranar Lahadi, sakamakon zanga-zangar nuna adawa da cin zarafin da 'yan sanda ke yi da kuma yadda yake tafiyar da lamarin.
Majalisar dokokin ƙasar ta ki amincewa da maye gurbin Mista Merino lokacin da ta yi wani zama a ranar Lahadi, ta kuma ƙi amincewa da tawagar da Rocío Silva Santisteban ke jagoranta, wanda marubuci ne kuma tsohon mai fafutukar kare haƙƙin dan adam.
An gabatar da sabon jerin sunayen wasu manyan 'yan siyasa tare da na shugaban da zai jagoranci ƙasar na rikon ƙwarya, daga faɗin ƙasar.
Me ya sa ake zanga-zangar?
Dubban masu zanga-zanga waɗanda mafi yawansu matasa ne, su ne suka jagoranci gangamin neman tsige Shugaba Vizcarra a 'yan kwanakin nan.
Suna zargin majalisar dokokin ƙasar da ƙokarin juyin mulki. Mista Vizcarra, mai shekara 57, ya yi ta samun goyon baya daga mutane da dama daga cikin masu zaɓe lokacin da yake yunƙurin kawo sauyi.
Zanga-zangar da aka yi a ranar Asabar a Lima ta kwanciyar hankali ce, amma da yamma sai rikici ya ɓarke tsakanin su da 'yan sanda.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun bayyana cewa an ta harba hayaƙi mai sa hawaye da bindiga domin tarwatsa masu zanga-zanga, wadanda suka riƙa jifa da duwatsu.
An kashe ɗalibai biyu, Jack Pintado mai shekara 22 da kuma Inti Sotelo, mai shekara 24.
"Ina so na bayyana wa ɗaukacin ƙasarmu cewa na yi murabus," in ji Mista Merino.
Akwai fargabar barkewar rikicin siyasa a Peru, sakamakon matsalar tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta wanda cutar korona ta janyo.
Peru na ɗaya daga cikin kasashen Kudancin Amurka da suka fara sanya dokar kullen annobar korona mai tsauri saboda daƙile yaɗuwarta - amma har yanzu ana samun ci gaban masu cutar.
Ya zuwa yanzu akwai kusan mutum 935,000 da suka kamu da cutar kuma sama da mutum 35,000 suka jikkata, kamar yadda Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka ta bayyana.
An yi tsammanin Mista Merino zai shiƙe shugabancin ƙasar har zuwa watan Yulin 2021 - yayin da aka kawo ƙarshen gwamnatin Mista Vizcarra.
Tun lokacin da Mista Vizcarra zama shugaban ƙasar a watan Maris ɗin 2018 ya shiga rikici da majalisar ƙasar, wadda kuma wakilan 'yan adawa ne suka fi yawa a cikinta.
Ya musanta zarge-zargen cewa ya karɓi cin hancin da ya kai dalar Amurka 640,000, lokacin yana gwamnan yankin Kudancin Moquegua.










