Abubuwan da suka kamata ku sani game da cutar hawan jini

SPL

Asalin hoton, Science Photo Library

An wallafa

Hawan jini cuta ce da ake kamuwa da ita ta dalilin toshewar wasu jijiyoyin jini da suke kai wa ƙwaƙwalwa saƙo, kuma da zarar sun gaza ayyukansu to matsala ta faru.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, cikin wani rahotonta, ta ce akwai kimanin mutum biliyan 1.13 da ke fama da wannan cuta a duniya, kuma kashi biyu cikin uku masu matsakaicin samu ne.

Wani bincike da WHO ta yi a 2015 ya nuna cewa namiji 1 cikin 4 na fama da wannan cuta, yayin da 1 cikin 5 a mata ke fama da hawan jini.

Hawan jini cuta ce mai wahalar sha'ani wadda ba a warkewa daga gare ta da zarar an kamu da ita.

Magungunanta na da tsada - ba irin na su ciwon kai ba ne ko kuma Maleriya.

Idan za a tattara kuɗin maganin da kuka saya a shekara uku saboda wannan cuta za ka ga ba ƙananan kuɗi ba ne.

Cuta ce da kullum ake samun ƙaruwar masu kamuwa da ita wadda kuma take haifar da ciwon zuciya, tana kuma haifar da matsalar ƙwaƙwalwa, ciwon ƙoda da dai sauran cutuka, kamar yadda WHO ta bayyana.

Getty

Asalin hoton, Getty Images

Ƙasa da kashi 1 ne cikin 5 na masu fama da wannan cuta ke iya shan magani yadda ya kamata, shi ya sa da yawa ke mutuwa da wuri kafin lokacinsu ya yi, a cewar hukumomin lafiya.

A Najeriya, wani bincike da aka yi ya ce sama da mutum miliyan 100 ne ke fama da wannan cuta, kuma maimakon raguwa kullum ƙaruwa adadin yake saboda tsarin yadda mutane ke rayuwa, da kuma irin abin da mutane ke ci ko sha, in ji shugaban asibitin koyarwa na Legas Farfesa Adewale Oke.

Saboda rashin zuwa asibiti da yawan mutane na fama da wannan rashin lafiya amma ba ma su san suna da ita ba.

Getty

Asalin hoton, Getty Images

Abubuwan da ke janyo cutar

  • Ƙiba ko kuma nauyin jiki
  • Damuwa a kwakwalwa
  • Shaye-shaye
  • Yawan cin gishiri
  • Cutar ciwon siga
  • Cin abinci mai kitse
  • Gado
  • Rashin motsa jiki

Yadda ake lallaɓa cutar hawan jini

Kamar yadda muka bayyana a sama cewa cutar hawan jini na zuwa da wasu cuta masu matuƙar haɗari, amma duk da haka ana iya lallaɓa cutar ta daɗe ba ta tashi ba.

  • Rage yawan cin gishiri (ƙasa da kilo giram 5 a rana)
  • Yawan cin ganyaye kayan itace
  • Motsa jiki akai-akai
  • ƙauracewa yawan shan taba