Duniyar da ake ruwan duwatsu, inda iskarta ke cike da rugugi tekunta kuma cike da wuta

Asalin hoton, NASA
- Marubuci, Daga Eva Ontiveros
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
A duniyar K2-141b, ruwan duwatsu ake yi, akwai kuma tekunsu mai cike da yumɓun duwatsun wuta da zurfinsa ya kai kilo mita 100, iskar wajen na da matuƙar sauri sama da ƙarar da muke ji sau huɗu.
"Wata duniya mai abin birgewa, da take da wani yanayi na musamman, akwai ma'adanai da ruwan sama da dusar ƙanƙara ga iskarta ta musamman," masu ilimin taurari da kuma jagoransu Tue Giang ya shaida wa BBC.
"Amma ba wuri ba ne da za a so a rayu a ciki ba, sai dai wuri ne da za a iya nazari kan abubuwa na daban da muke gani a duniyar Earth!" In ji Farfesa Nicolas Cowan.
Tare da wata tawagar masana taurari daga Indiya da Canada, sun wallafa sabon bincike kan duniyar K2-141b da wasu sabbin bincike, duniyar duwatsu kamar dai Earth.
Barkanmu da zuwa 'duniyar aman wuta'

Asalin hoton, Getty Images
Duniyar K2-141 wadda aka fi sani da EPIC 246393474.01, wadda take da nisan kilo mita tirliyan daga duniyarmu, a inda taurari suke taruwa.
Wata duniyar wuta ce wadda ba za a iya zama ciki ba, inda lokaci ke matukar gudu: a K2-141b inda taurari ke kusa da juna shekara ɗaya a nan kasa da awa bakwai ce.
Tauraron cikinta shi masana taurari suke kira "orange dwarf" - duniyar ba ta kai rana zafi ba - kuma ta yi duhu sosai ta yadda ba za a iya ganinta daga duniyar Earth ba.
"Duniyar da ke cike da yumɓun dutsen wuta" in ji masana kimiyya da ke sharhi da kuma ƙarin haske kan bayanan a cibiyar kimiyya ta Indiya da ke Kolkata, da kuma na Jami'ar York da Toronto da ke Canada da kuma McGill da ke Montreal duk dai a Canada.
Haka kuma wata duniya ce mai kama da tamu, saboda tsayin yinin bai wuce na wannan duniyar tamu ba, sai dai girmanta ya ninka na wadda muke sama da sau biyar (wanda hakan ke nufin maganaɗinsun da ke janyo abubuwa ƙasa a duniyar K2-141b ya ninka ta wannan duniyar tamu).
An gano K2-141b a 2018, kuma na'urar hangen nesa ta (Kepler Space Telescope's "K2 mission,") yanzu kuma masu bincike na ta roƙon a ci gaba da bankaɗo abubuwan al'ajabinta.
Yaya yanayin wajen yake?

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma K2-141b na zagaye tauraronta a cikin awannin, ba ta iya zagayen a kan layin da ya kamat ta bi kamar yadda duniyar Earth ke yi.
"Wanda hakan ke nufin kashi biyu cikin uku na duniyar ko da yaushe tana cikin haske a tsarin yini take ko da yaushe, kuma yanayin zafin wajen zai kai dubu uku a ma'aunin salshiyos," in ji Farfesa Cowan.
Idan kuma muka kwatanta da daya bangaren nata, ko da yaushe cikin duhu yake, yanayin sanyin wajen kuma zai kai -200 a ma'aunin salshiyos.
Wannan sauyin yanayin ne ya sanya ake samun sanyi sosai ... wanda masana taurari ke kiranta "ruwan duwatsu".
'Abin da ba a saba gani ba kuma abin burgewa'

Asalin hoton, Inpho
"Mene ne zai zo ranka, a wannan duniyar komai dutse ne," in ji shi.
Zafin da ake yi da rana ya ɓaci, duwatsun kuma suna narkewa kuma ma'adanan cikinta suna tashi zuwa sararin samaniya. Abu ne da ba a saba gani ba kuma gwanin sha'awa.
"Waɗannan abubuwan na ƙarewa ne a matsayin ruwan sama, a wasu lokutan kuma su riƙa sauka a matsayin dusar dutse, suna saukowa cikin tekun," ya kasar da cewa.
"Wannan ne bincike na farko da aka fara yi game da yadda yanayin duniyar za ta iya kasancewa."
Me yasa za mu mayar da hankali a kai?

Asalin hoton, Getty Images
Duka abubuwa ne masu ban sha'awa amma saboda me muke tattauna su?
"Bincike kan wannan duniyar zai taimaka mana wajen fahimtar duniyar Earth, wadda ita ma a baya a zagaye take da wannan shimfiɗa irinta k2-141b, in ji mawallafin binciken Mista Mguyen.
Da wannan bincike za mu iya ƙara fahimtar yadda aka samu duniyar Earth. Amma akwai ƙarin abubuwan da za mu iya lura da su...
"Wannan yumɓun wutar da ake samu daga duwatsun da ke narkewa ba ƙaramar baiwa ba ce, zai ba mu damar kara karantar wasu abubuwa na musamman!" in ji Farfesa Cowan.










